Gwamnoni 35 Sun Yi Matsaya kan Dakatar da Fubara da Tinubu Ya Yi
- Kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana dalilin da ya sa ba ta ce komai kan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara
- NGF ta ce ba ta son daukar matsayi a kan batutuwan siyasa domin gujewa rarrabuwa tsakanin mambobinta da ke jihohi
- Biyo bayan shirun da ta yi, kungiyar ta ce a shirye take ta mayar da hankali kan cigaban tattalin arziki da jin dadin al’umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta yi karin bayani kan dalilin da ya sa ba ta goyi bayan wani bangare ba kan batutuwan siyasar da suka faru kwanan nan.
Kungiyar ta ce manufarta ita ce zama wata kungiya mai ba da shawarwari da tsare-tsaren ci gaba, ba shiga siyasar bangaranci ba.

Asali: Facebook
A cewar wata sanarwa da jaridar Vanguard ta wallafa, NGF ta bayyana cewa matsayinta bai shafi siyasar bangaranci ba, saboda haka ba za ta dauki matsayi a rikicin jihar Ribas ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na zuwa ne bayan shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas, lamarin da ya jawo dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa.
Haka zalika matakin ya jawo dakatar da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
Kungiyar Gwamnonin ta fadi dalilin shirunta
A cikin wata sanarwa da ta fitar mai taken karin haske kan shiru da NGF ta yi kan lamuran siyasa, kungiyar ta fadi dalilin yin shiru kan rikicin Ribas.
NGF ta ce ta yanke shawarar gujewa daukar matsayi kan rikicin Ribas ne domin gujewa rarrabuwa tsakanin mambobinta.
A cewar Darakta Janar na NGF, Dr Abdulateef Shittu, kungiyar na aiki ne a matsayin wata mai ba da shawarwari kan tsare-tsaren ci gaba, ba wai siyasar bangaranci ba.
“Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kungiya ce da ke kare muradun gwamnatocin jihohi, domin ganin an samu ci gaba mai dorewa,”
- Dr Abdulateef Shittu

Asali: Facebook
Matsayar NGF kan ci gaban kasa
Ko da yake NGF ba ta ambaci rikicin Ribas kai tsaye ba, sanarwar ta jaddada cewa kungiyar za ta mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi ci gaban tattalin arziki da jin dadin al’umma.
Dr Shittu ya bayyana cewa a baya, akwai rikicin siyasa da ya taba shafar NGF, wanda hakan ya janyo rarrabuwa tsakanin mambobinta.
Business Day ta wallafa cewa Dr Shittu ya ce saboda haka ne kungiyar ba za ta shiga lamarin da ka iya haifar da sabon rabuwar kai ba.
Gwamnoni sun bukaci a fahimci matsayinsu
Darakta Janar na NGF ya ce duk da cewa kungiyar ba ta shiga rikicin siyasa, tana da karfin fada a ji kan batutuwan da suka shafi albashi, haraji, ilimi da kiwon lafiya.
Ya bukaci ‘yan jarida da al’ummar kasa da su fahimci matsayin NGF, yana mai cewa kungiyar tana da yakinin cewa hukumomin siyasa da na sasanta rikice-rikice za su warware matsalar.
Shugaban Ribas ya gargadi sarakuna
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban riko na jihar Ribas da aka nada ya gana da sarakunan gargajiya kan harkokin siyasa.
Sabon shugaban ya ce sarakunan suna da rawar da za su taka wajen magance matsalar tsaro yayin da ya gargade su kan shiga siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng