Tsagin NNPP Ya Kwanto Wa Kwankwaso da Mabiyansa Ruwa, Jam'iyya Ta Tura Wasiƙa ga INEC

Tsagin NNPP Ya Kwanto Wa Kwankwaso da Mabiyansa Ruwa, Jam'iyya Ta Tura Wasiƙa ga INEC

  • Tsagin NNPP karƙashin jagorancin Agbo Major ta rubuta wasika zuwa ga INEC tana sanar da cewa ta raba gari da Kwankwasiyya da kungiyar TNM
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa ta katse yarjejeniyar aiki tare da suka ƙulla da ƙungiyoyin ƙarƙashin jagorancin Rabiu Kwankwaso da Buba Galadima
  • A cewar NNPP, ta lura Kwankwaso da mabiyansa na ci gaba da ayyana kansu a matsayin ƴaƴanta duk da ƙarewar yarjejeniyar da suka yi kafin zaben 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jam’iyyar NNPP ta tsagin Agbo Major ta jaddada raba gari da Kwankwasiyya karkashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso da ƙungiyar TNM.

Jam'iyyar ta nesanta kanta da ƙungiyoyin tare da gargaɗinsu da su daina ayyana kansu a matsayin ƴaƴan NNPP daga yanzu.

NNPP da Kwankwaso.
Jam’iyyar NNPP ta nesanta kanta da Kwankwasiyya da kungiyar TNM Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Jam'iyyar NNPP ta rubuta wasika ga INEC

Vanguard ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata wasika da tsagin NNPP ya aika wa hukumar zaɓe (INEC) mai ɗauke da kwanan watan 20 ga watan Maris, 2025.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun faɗi damuwarsu kan dokar ta ɓaci a Ribas, sun ambaci Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasikar na ɗauke da sa hannun Shugaban Majalisar Amintattu (BoT) na NNPP, Dakta Boniface Aniebonam, da Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Dakta Agbo Major.

Tsagin NNPP ya kuma aika kwafin wasikar ga sufetan ƴan sandan Najeriya domin sanar da shi cewa ba ruwan jam'iyyar da su Kwankwaso.

NNPP ta tunatar da kungiyoyin cewa ya kamata su kiyaye yarjejeniyar fahimtar juna watau MoU da suka kulla da su, wacce ta ƙare tun shekarar 2023.

A cewar jam’iyyar, shugabannin kungiyoyin, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Buba Galadima, dole ne su mutunta ƙarshen wannan yarjejeniya da aka yi kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Yadda NNPP ta yi yarjejeniya da Kwankwaso

A baya, NNPP ta kulla yarjejeniya da Kwankwasiyya ƙarƙashin Rabiu Kwankwaso da kuma TNM a ƙarƙashin Galadima, domin yin aiki tare da babban zaɓen 2023.

Sai dai, bayan kammala zaɓen, jam’iyyar ta sanar da rushe yarjejeniyar a cikin wata wasika da ta aika a watan Yuli na 2023.

Kara karanta wannan

Wike ya sake samun nasara, Kotun Koli ta yi hukunci kan rikicin sakataren PDP na ƙasa

Wannan mataki ya jawo sabani, inda kungiyoyin suka ƙi amincewa da ƙarewar yarjejeniyar, suka kuma ci gaba da riƙe kansu a matsayin ’yan NNPP.

Bisa haka, NNPP ta sallami wasu daga cikin mambobin da ke cikin kungiyoyin, bisa zargin su da aikata abubuwan da suka saɓa wa jam’iyya.

Wasiƙar da jam'iyyar NNPP ta turawa INEC

A cikin wasikar, NNPP ta ce:

"Muna tunatar da ku cewa tun ranar 28 ga Yuli, 2023, mun sanar da ku janye kanmu daga yarjejeniyar da muka kulla da ku, wato Kwankwasiyya da NNPP."
"Amma mun lura cewa har yanzu kuna ci gaba da bayyana kanku a matsayin shugabanni ko mambobin jam’iyyar NNPP. Ya zama wajibi ku dakatar da wannan yunkuri mara da’a nan take.
"Muna gargadinku da ku daina yaudarar jama’a da ƙarya game da matsayin ku a jam’iyyar NNPP.”

Buba Galadima ya soki masu shiga SDP

A wani labarin, kun ji cewa jigon NNPP, Buba Galadima ya caccaki ƴan siyasar da ke bin tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai zuwa SDP.

Galadima ya ce babu wani abin mamaki dangane da rashin ganin jiga-jigan NNPP suna komawa SDP , domin a cewarsa, jam’iyyar wani reshe ne na APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng