Wata Sabuwa: Ana Neman Cin Tarar Tinubu Dala Miliyan 10 kan Dakatar da Fubara

Wata Sabuwa: Ana Neman Cin Tarar Tinubu Dala Miliyan 10 kan Dakatar da Fubara

  • Kungiyar matasan Ijaw ta maka Gwamnatin Tarayya da Bola Tinubu a kotun ECOWAS kan ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas
  • Matasan sun bukaci kotu ta soke dakatar da zababbun jami’an gwamnati da kuma dakatar shugaban rikon kwarya da aka nada a jihar
  • Kungiyar ta bukaci a biya su diyyar Dala miliyan 10 saboda keta hakkinsu na dimokuradiyya da kuma dakatar da gwamnatin Ribas

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Wasu mambobin kungiyar matasan Ijaw sun maka Gwamnatin Tarayya a kotun ECOWAS kan ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas.

Matasan sun bukaci kotu ta rusa matakin da shugaba Bola Tinubu ya dauka na fyade wa dimokuradiyya a jihar, suna masu cewa hakan ya saba wa tsarin mulkin kasa.

Kara karanta wannan

Daga fara mulki, shugaban rikon Ribas ya yi zazzafan gargadi wa sarakuna

Fubara
An maka Tinubu a kotu kan dakatar da Fubara. Hoto: Bayo Onanuga|Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

A cewar jaridar The Cable, matasan sun bukaci kotun ta rusa duk wata doka da sabon shugaban riko na jihar, Ibok-Ete Ibas, ya kafa, tare da dawo da duka zababbun jami’an gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar matasan ta bayyana cewa dakatar da gwamnati da majalisar dokoki a jihar ya na da matukar illa ga dimokuradiyya, kuma hakan ya sabawa ‘yancin da ‘yan jihar Ribas suke da shi.

Matasan Ijaw sun kalubalanci dokar ta-baci

A karar da suka shigar a ranar 20 ga watan Maris, matasan sun bayyana cewa matakin shugaba Bola Tinubu ya saba wa tsarin dimokuradiyya.

Sun ce babu wata doka da ta ba shugaban kasa damar rusa gwamnati ta dimokuradiyya ba tare da bin ka’idoji na kundin tsarin mulki ba.

A cewar matasan, dokar ta-baci ba ta nufin cewa dole ne a dakatar da gwamnati gaba daya, musamman ma idan babu wani hatsari na kai tsaye da zai iya kawo barazana ga zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Nasarori 3 da Nyesom Wike ya samu a cikin kwanaki 3 a siyasar jam'iyyar PDP

An bukaci kotu ta rusa dokokin da aka kafa

Kungiyar matasan ta bukaci kotun ECOWAS ta rusa duk wasu dokoki da sabon shugaban rikon jihar Ribas ya kafa, wanda Shugaba Tinubu ya nada bayan ayyana dokar ta-baci.

A cewarsu, daukar matakin rushe dimokuradiyya a wata jiha ya na nufin cewa gwamnatin tarayya na kokarin karbe iko da karfi, wanda hakan ka iya zama barazana ga kasa.

Fubara
Gwamnan Ribas da aka dakatar. Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Instagram

Matasan Ijaw sun bukaci diyyar Dala miliyan 10

A cikin karar da suka shigar, matasan sun bukaci kotun ECOWAS ta umarci Gwamnatin Tarayya da ta biya su diyyar Dala miliyan 10.

Sun ce matakin da aka dauka ya tauye musu hakkin su na zabar shugabanni da kuma yin rayuwa a karkashin dimokuradiyya.

A cewarsu, yin karan tsaye wa dimokuradiyya a jihar Ribas ba wai kawai cutar da ‘yan jihar ne ba, har ma da barazana ga tsarin mulkin kasa.

Kara karanta wannan

Dokar ta baci a Ribas: Ana zargin Shugaba Tinubu da 'juyin mulki'

Channels TV ta wallafa cewa matasan sun kara da cewa idan aka yarda hakan ya faru a wata jiha, za a iya maimaita irin wannan a sauran jihohi.

Kwankwaso ya soki dakatar da Fubara

A wani rahoton, kun ji cewa Rabiu Kwankwaso ya soki gwamnatin tarayya kan dakatar da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara.

Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa lamarin ya saba dokar kasa kuma ya zama barazana ga dimokuradiyya da aka kafa a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng