Nasarori 3 da Nyesom Wike Ya Samu a cikin Kwanaki 3 a Siyasar Jam'iyyar PDP

Nasarori 3 da Nyesom Wike Ya Samu a cikin Kwanaki 3 a Siyasar Jam'iyyar PDP

Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya samu manyan nasarori a makon da ya gabata, wanda su ka kawo sauyi a siyasar kasar nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Duk da kasancewarsa jigo a PDP, nasarorin da ya samu a cikin kwanaki uku kacal na kara durkusar da jam’iyyar a gaban gwamnatin Bola Tinubu da APC.

Nyesom
Wike ya samu nasarorin dunkufar da jam'iyyarsa Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru, wanda Nyesom Wike ke maraba da su, wadanda ake kuma kallon sun jefa PDP a cikin mawuyacin hali.

1. Dakatar da gwamnan Ribas

A ranar 18 ga watan Maris, 2025, Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas, wanda ya kai ga dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara daga mukaminsa.

Kara karanta wannan

Yadda Akpabio ya "murkushe" yan majalisa da suka ki amincewa da dokar ta-baci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Arise News ta ruwaito cewa an kuma dakatar da mataimakinsa da dukkannin ‘yan majalisar jihar na tsawon watanni shida saboda yawaitar rikicin siyasa da barna da ake yi wa bututun mai a jihar.

A jawabin shugaban kasa, bai nuna akwai hannun Nyesom Wike a rikicin Ribas ba. Wannan kusan ya nuna irin fadar ministan a gwamnatin APC.

Nyesom
Ana zargin Wike da hannu a dakatar da gwamnan Ribas Hoto: Sir Siminalayi Fubara/Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Twitter

Bayan hakan, Shugaban Kasa ya nada tsohon Hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) a matsayin sabon shugaban rikon kwarya na jihar Ribas.

Ko da yake gwamnatin APC ta wanke Nyesom Wike daga zargin, amma ana ganin tasirinsa a siyasar jihar da matsayinsa a gwamnatin tarayya sun taka rawa wajen dakatar da gwamnan.

2. Wike ya amince an karbe sakatariyar PDP

Daily Trust ta ruwaito cewa a matsayin hukumar gudanarwar Abuja a karkashin Nyesom Wike ta kwace iko da filin da PDP ke amfani da shi a matsayin hedikwata, da ke Wadata Plaza.

Kara karanta wannan

Awanni da nada sababbin hadimai, Abba ya ba su umarnin bayyana yawan kadarorinsu

Hukumar Abujan ta bayyana cewa an dauki matakin ne sakamakon gaza biyan harajin fili na tsawon sama da shekaru 20 da PDP ta yi.

Sai dai PDP ta koka, tana mai cewa wannan yunkuri ne na murkushe ‘yan adawa, lamarin da hukumar ta musanta, tare da bayyana cewa wannan wani bangare ne ta tilasta bin doka.

3. Yaron Wike, Anyanwu ya yi nasara a kotu

A hukuncin da Kotun Koli ta yanke a ranar Juma'a, an soke hukuncin da ya kori Sanata Samuel Anyanwu a matsayin Sakataren PDP na kasa.

Wannan mataki na da matukar muhimmanci, domin ana kallonsa a matsayin nasara ga bangaren Wike da suka zama karfen kafa a jam'iyyar PDP.

Kwamitin gudanarwar PDP na kasa, Kwamitin amintattu, gwamnonin PDP, sun sha tabbatar da Udeh-Okoye a matsayin Sakataren jam’iyyar na Kasa a lokuta daban-daban a baya.

Sai dai wannan hukunci ya jawo rudani, bangarorin Udeh-Okoye da Wike su na cewa su ne suka samu nasara a shari'ar kotun koli.

Kara karanta wannan

Ribas: An fallasa yadda Wike da gwamnatin Tinubu suka kitsa dakatar da Fubara

An zargi Wike da kitsa matsalar Ribas

A baya, mun wallafa cewa wani babba a yankin Neja Delta, Cif Anabs Sara-Igbe, ya yi tir da dakatar da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, lamarin da ya ke ganin haramun ne a dokar kasa.

Ya bayyana cewa Nyesom Wike da gwamnatin tarayya sun dade suna kitsa yadda za a sanya dokar ta baci a jihar domin a dunkufar da gwamnatin Fubara saboda bukatar kashin kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.