Jam'iyyar APC Ta Yi wa Gwamnatin Jihar Kano Barazana da Dokar Ta Ɓaci

Jam'iyyar APC Ta Yi wa Gwamnatin Jihar Kano Barazana da Dokar Ta Ɓaci

  • APC ta yi barazana ga gwamnatin Kano saboda kalaman Mataimakin gwamna, Kwamred Aminu Abdulsalam, kan Hafsat Ganduje
  • Mataimakin gwamnan ya zargi matar tsohon gwamnan Kano kuma shugaban APC na yanzu, Abdullahi Ganduje da ɓincine kuɗin fansho
  • Ya ƙara da kiranta 'gwaggwon matsiyata', lamarin da ya fusata ƴan APC har ta fara batun a ƙaƙaba wa Kano dokar ta ɓaci kamar a Ribas

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jam'iyyar adawa ta APC a Kano ta fara barazana ga gwamnatin NNPP ƙarƙashin Mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf.

Barazanar ta biyo bayan kalaman Mataimakin gwamna, Kwamred Aminu Abdulsalam, kan matar Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje.

Ganduje
APC ta gargadi gwamnatin Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf/Bayo Onanuga/Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

A wani bidiyo da Nuhu Sani Dambazau ya wallafa a shafinsa na Facebook, ana iya ganin Kwamred Abdulsalam yana zargin matar tsohon gwamnan da yin kutse a cikin kuɗin fansho.

Kara karanta wannan

Wike ya sake samun nasara, Kotun Koli ta yi hukunci kan rikicin sakataren PDP na ƙasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin gwamnan ya ce gwamnatin yanzu tana biyan tsofaffin ma'aikata fansho kai tsaye, amma a lokacin Ganduje, sai Farfesa Hafsat ta cire kasonta kafin a biya bayin Allah haƙƙinsu. .

APC ta yi martani ga gwamnatin Kano

A wata hira da ya yi da Express Radio, Sakataren yaɗa labaran APC a Kano, Ahmad S. Aruwa, ya bayyana takaicin kalaman Mataimakin gwamnan kan Hafsat Ganduje.

Aruwa ya ƙara da cewa kalaman Kwamred Aminu Abdulsalam sun ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya, yana mai bayyana su a matsayin cin zarafi.

Ganduje
An zargi mataimakin gwamnan Kano da muzanta Hafsa Ganduje Hoto: Hajiya Hafsat Ganduje
Asali: Facebook

Sakataren ya yi barazanar cewa irin waɗannan kalamai na iya jawo ayyana dokar ta-ɓaci a Kano, kamar yadda gwamnatin Bola Tinubu ta yi a jihar Ribas.

A kalamansa, ya ce:

"Maganganun da Mataimakin gwamnan Kano, Kwamred Aminu Abdulsalam, yake yi na cin zarafin mai dakin Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa sun saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa.

Kara karanta wannan

Rivers: An shiga fargabar halin da Fubara ya shiga kwanaki 2 bayan dakatar da shi

Wannan ya na iya haifar da matsala mai tsanani da ka iya kai wa ga ayyana dokar ta-baci a Kano, kamar yadda aka yi a jihar Ribas.”

An yi martani ga barazanar jam'iyyar APC

Masu amfani da shafin Facebook sun bayyana rashin jin daɗin kalaman Sakataren yaɗa labaran APC, wanda wasu ke kallon yunƙuri ne na jawo masifa ga Kano.

Idrees Alay ya wallafa cewa:

"Su dai dole sai musiba ta sauka a Kano, kuma in ta zo, tafi ƙarfin su. Sai ka ji suna kiran sunan Allah cewa shi ne ya kawo, suna roƙon a yi musu addu’a.
Sai ka rasa wace al’umma ce muke rayuwa a cikinta."

Aminu Yaro Na-Abba ya ce:

"Ku dokar ta-baci ku ke tsoro? Mu fushin Allah muke jin tsoro lokacin da Abdullahi Abbas ya ce kada Allah ya kiyaye ranar zaɓe.
Da ba don Allah ya riga ya gama tsara komai ba, da a lokutan baya har yanzu an kifar da duniya."

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya naɗa sababbin mukamai, tsohon mai adawa da gwamnati ya rabauta

NNPP ta soki gwamnatin APC

Shugaban APC na Kano, Hashimu Dungurawa ya shaidawa Legit cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta samu babbar lamba a mulkin kama karya da danniya. Ya ce jihohi kamar su Katsina, Zamfara da Borno sun fuskanci matsaloli masu kamanceceniya da ta Ribas, amma ko dokar ta ɓaci ba a bayyana ba ballantana dakatar da gwamnati. Ya kara da cewa suna kara shirin da zai fatattaki gwamnatin APC daga mulkin Najeriya a 2027 domin ceto talakawan Najeriya daga halin da suke ciki.

Ana tsoron gwamnatin APC saboda dokar ta baci

A wani labarin, kun ji cewa fitacciyar ƴar gwagwarmaya a Arewacin Najeriya, Naja’atu Muhammad, ta bayyana fargabar gwamnatin Bola Tinubu na murkushe adawa.

Ta bayyana cewa gwamnatin za ta iya riƙa yin barazana da dokar ta-ɓaci don kame muhimman jihohi domin ba Bola Tinubu damar tazarce a zaben da ya ke tunkaro wa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng