An Fadi Halin da Fubara Ke ciki bayan Shugaban Rikon Kwarya Ya Shiga Ofis a Rivers
- Kakakin Simi Fubara da aka dakatar, Nelson Chukwudi, ya tabbatar da gwamnan ya na lafiya kuma babu matsala da lafiyarsa
- Chukwudi ya bayyana hakan ne a wata hira da yan jaridu yana mai karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta
- Ya ce mutane su yi watsi da labaran da suke gani a shafukan intanet domin babu barazanae da ke fuskantar Gwamna Fubara
- Duk da rikicin siyasa, Fubara yana cikin kwanciyar hankali kuma yana ci gaba da gudanar da rayuwarsa cikin koshin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Mai magana da yawun dakataccen gwamnan Rivers ya yi magana halin da mai gidansa ke ciki.
Mista Nelson Chukwudi ya ce Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers da aka dakatar yana nan ba matsala kuma yana cikin koshin lafiya.

Asali: Instagram
Ibok-Ete ya kama aiki bayan dakatar da gwamna
Chukwudi ya fadi haka ne yayin da yake magana da jaridar Leadership a daren yau Juma’a 21 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na zuwa ne bayan sabon shugaban rikon kwarya a Rivers ya shiga ofishinsa bayan kama rantsuwa a jiya Alhamis.
Sabon shugaban rikon kwarya Ibok-Ete Ibas, ya bayyana kansa a matsayin dan yankin, yana mai sha'awar dawo da zaman lafiya.
Shugaban ya gargadi mazauna jihar da su guji ta da fitina da lalata man fetur, inda ya jaddada illar hakan ga tattalin arziki da muhalli.
A karshe, ya yaba da matakin shugaba Bola Tinubu na ayyana dokar ta-baci da cewa hakan zai dawo da doka da ci gaban tattalin arziki.
Ibas ya ce zai yi aiki da dukkanin bangarori don tabbatar da zaman lafiya da dorewar dimokuradiyya a jihar Rivers.

Asali: Facebook
Kakakin Fubara ya kore jita-jita a kafofin sadarwa
Chukwudi ya ce mutane ya kamata su bar yada karairayi a kafafen sadarwa kan abubuwan da ba su da masaniya a kansu.
Hadimin ya ƙaryata labarin da ake ta yadawa kan halin da Fubara ke ciki tun bayan kwace iko da aka yi sanadin sanya dokar ta-ɓaci.
A cikin hirar, Chukwudi ya ce:
“Ku manta da abin da kuke gani a kafafen sada zumunta, Gwamnan yana nan garau kuma yana cikin koshin lafiya.”
Har ila yau, Chukwudi ya ce babu wani abu marar kyau ko na rashin jin dadi da gwamnan ke ciki a halin yanzu.
Rivers: Jigon PDP ya goyi bayan dokar ta-ɓaci
A baya, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar PDP a Rivers, Alex Wele, ya bukaci al’umma su mara wa shugaban rikon kwarya a jihar baya don samun zaman lafiya.
'Dan PDP ya fadi haka ne a yau Juma'a yayin da jam'iyyarsa da sauran al'umma ke sukar matakin da Bola Tinubu ya ɗauka na sanya dokar ta-ɓaci a jihar.
Wele ya ce ko da yake dokar ta-baci ba ta kamata a farko ba, amma matakin gwamnatin tarayya abin yabawa ne don dakile rikicin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng