Fubara: Jigon PDP Ya Fita Daban da Sauran ƴan Jam'iyya kan Sanya Dokar Ta Ɓaci

Fubara: Jigon PDP Ya Fita Daban da Sauran ƴan Jam'iyya kan Sanya Dokar Ta Ɓaci

  • Wani jigo a PDP a Rivers, Alex Wele, ya bukaci al’umma su mara wa shugaban rikon kwarya a jihar baya don samun zaman lafiya
  • Wele ya ce ko da yake dokar ta-baci ba ta kamata a farko ba, amma matakin gwamnatin tarayya abin yabawa ne don dakile rikicin
  • Ya shawarci gwamna da ’yan majalisar dokokin da aka dakatar su yi amfani da lokacin don sasanci da kawo fahimta a tsakaninsu
  • Wannan 'dan PDP ya jaddada bukatar hadin kai da mai rikon Jihar da kuma gwamnatin tarayya domin dawo da doka da oda

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt - Wani jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Rivers, Alex Wele, ya barranta da sauran yan jamiyyarsa kan dokar ta-ɓaci a Rivers.

Wele ya bukaci al’ummar jihar su goyi bayan shugaban rikon kwarya a Rivers, Ibok-Ette Ibas domin tabbatar da zaman lafiya ya sake dawowa a yankin.

Kara karanta wannan

Aiki zai dawo sabo: Gwamnoni 12 za su maka Tinubu a kotu kan Fubara

Jigon PDP a Rivers ya goyi bayan shugaban riko a jihar
Jigon PDP ya barranta da sauran ƴan jam'iyyarsa kan dokar ta-ɓaci a Rivers. Hoto: @aonanuga1956.
Asali: Twitter

Rivers: Jigon PDP ya goyi bayan dokar ta-ɓaci

Wele ya bayyana hakan ne a wata hira da yan jaridu a ranar Juma’a 21 ga watan Maris, 2025 a birnin Port Harcourt, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ko da yake ba a yi tsammanin dokar ta-baci ba, amma matakin gwamnati abin yabawa ne domin kawo karshen rikicin siyasa a jihar.

Wele ya bukaci Gwamna Siminalayi Fubara da ’yan majalisar da aka dakatar da su yi amfani da wannan lokaci wajen sasanci da warware sabanin da ke tsakaninsu.

A cewarsa, sasanci na gaskiya zai iya kawo hadin kai da kuma mayar da su bakin aikinsu idan abubuwa suka daidaita.

Wele ya ce:

“Shawarar da nake baiwa mutanen Rivers ita ce su zauna lafiya da kwanciyar hankali tare da hadin kai da gwamnati da mai rikon jihar.
“An ba shi umarni na musamman don dawo da doka da oda, mu hadu da shi mu ga ko gwamna da ’yan majalisar za su dawo su sulhunta.”

Kara karanta wannan

Dokar ta baci a Ribas: Ana zargin Shugaba Tinubu da 'juyin mulki'

An fara samun rarrabuwar kawuna kan dokar ta-ɓaci a Rivers
Wani ɗan PDP ya goyi bayan dokar ta-ɓaci a jihar Rivers. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Twitter

Jigon PDP ya shawarci al'ummar Rivers

Yayin da yake bayyana rikicin a matsayin mara amfani kuma wanda bai zama dole ba, dattijon ya bukaci bangarorin rikicin su rungumi zaman lafiya.

Haka kuma, ya shawarci gwamnan da ’yan majalisar da su mayar da hankali wajen samar da ci gaban dimokuradiyya idan aka dawo da su.

Ya ce hakan ne kawai zai tabbatar da kawo zaman lafiya cikin sauki bayan barkewar rikicin siyasa a jihar, cewar rahoton The Nation.

Shugaban rikon kwarya a Rivers ya gargadi al'umma

Mun ba ku labarin cewa sabon shugaban rikon kwarya a Rivers, Ibok-Ete Ibas, ya bayyana kansa a matsayin dan yankin, ya na mai sha'awar dawo da zaman lafiya.

Ibok-Ete Ibas ya gargadi mazauna jihar da su guji ta da fitina da lalata kayan mai, ya jaddada illar hakan ga tattalin arziki da muhallin yankin da ke da tasiri a Najeriya.

Tsohon shugaban sojojin ruwa yaba da matakin shugaba Bola Tinubu na ayyana dokar ta-baci da cewa hakan zai dawo da doka da ci gaban tattalin arziki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel