Aiki zai Dawo Sabo: Gwamnoni 12 za Su Maka Tinubu a Kotu kan Fubara

Aiki zai Dawo Sabo: Gwamnoni 12 za Su Maka Tinubu a Kotu kan Fubara

  • Gwamna Seyi Makinde ya ce gwamnonin PDP za su maka gwamnatin tarayya a kotu kan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara
  • Seyi Makinde ya ce dole ne a kare dimokuradiyya, domin dakatar da gwamna mai ci da ‘yan majalisar dokoki ba bisa doka ba ne
  • Hakan na zuwa ne bayan Bola Ahmed Tinubu ya sanya dokar ta baci a jihar Rivers da dakatar da gwamna da mataimakiyarsa
  • Lamarin ya jawo suka daga 'yan jam'iyyun adawa ciki har da Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso, Nasir El-Rufa'i da Peter Obi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa gwamnonin PDP za su kalubalanci matakin Bola Tinubu na dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Dokar ta baci a Ribas: Ana zargin Shugaba Tinubu da 'juyin mulki'

Makinde ya bayyana hakan ne a cikin wasiƙar sa ta wata-wata a ranar 19 ga Maris, ya ce ba za su zuba ido ba a take dimokuradiyya da suka shafe kusan shekaru 30 suna ginawa.

Fubara
Gwamnonin PDP za su maka Tinubu a kotu. Hoto: @officialABAT, @seyimakinde, @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Legit ta tattaro bayanan da gwamna Seyi Makinde ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya kara da cewa dole ne a tsaya tsayin daka domin kare dimokuradiyya, komai bambancin ra’ayi ko biyayya ta siyasa.

PDP ta ce dole a janye dokar ta-baci a Rivers

Seyi Makinde ya ce gwamnonin PDP sun gudanar da taron gaggawa, kuma a karshen taron sun cimma matsaya guda daya, wato kalubalantar matakin Tinubu a gaban babbar kotu.

A cewar Seyi Makinde:

“Mun amince gaba daya cewa za mu shigar da kara a kotu domin kalubalantar matakin shugaba Bola Ahmed Tinubu.”

Kara karanta wannan

An nemi kama sakataren APC kan yunkurin dakatar da gwamnan PDP a Osun

Tun da fari, gwamnonin PDP sun fito fili sun yi watsi da dakatar da Fubara, suna masu cewa wannan babban kuskure ne da ke barazana ga dimokuradiyya.

Fubara
Gwamnan Rivers da aka dakatar. Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Instagram

Gwamnonin PDP sun bukaci a janye matakin

Bayan taron da gwamnonin PDP suka gudanar karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed na Bauchi, sun bukaci shugaba Tinubu da ya janye dakatarwar da ya yi wa Fubara.

Sun bayyana cewa daukar wannan mataki ba daidai ba ne, domin kuwa ya na barazana ga tsarin mulki na dimokuradiyya a Najeriya.

PDP na da gwamnoni 12 a jihohin Najeriya, kuma su ne:

  • Adamawa – Ahmadu Fintiri
  • Akwa Ibom – Umo Eno
  • Bauchi – Bala Mohammed
  • Bayelsa – Douye Diri
  • Delta – Sheriff Oborevwori
  • Enugu – Peter Mbah
  • Osun – Ademola Adeleke
  • Oyo – Seyi Makinde
  • Plateau – Caleb Mutfwang
  • Rivers – Siminalayi Fubara (wanda aka dakatar)
  • Taraba – Agbu Kefas
  • Zamfara – Dauda Lawal

Kara karanta wannan

Fubara: Kwankwaso ya hade da Atiku, El Rufa'i, Obi kan rikicin Ribas

Legit ta wallafa cewa gwamnonin sun yi alkawarin ci gaba da kare dokokin kasa da kuma tabbatar da adalci ga kowa.

Kwankwaso ya kalubalaci dakatar da Fubara

A wani rahoton, kun ji cewa Rabiu Kwankwaso ya yi Allah wadai da dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da Bola Tinubu ya yi.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa matakin ya saba tsarin dimokuradiyya da kundin mulkin Najeriya da ake aiki da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng