"Mu ba Mabarata ba ne," Tsohon Ɗan Takara a Kano Ya Caccaki Ɗan Shugaba Tinubu
- Tsohon ɗan takarar Majalisa a Kano, Adnan Mukhtar TudunWada ya soki ziyarar da Seyi Tinubu ya kawo Arewa, ya ce wannan cin mutunci ne
- Adnan ya bayyana cewa ɗan shugaban ƙasa bai isa ya yi wa sarakunan Kudu abin da ya yi wa na Arewa ba, yana mai cewa akwai raini a lamarin
- Matashin ya shaida Legit Hausa cewa Arewa na bukatar a inganta ilimi, wutar lantarki, cibiyoyin fasaha da sauransu ba wai raba abinci ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Tsohon ɗan takarar Majalisar dokokin jihar Kano, Hon. Adnan Mukhtar TudunWada ya caccaki ziyarar da ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu ya kawo Arewa.
Hon. Adnan ya bayyana cewa abin da ɗan Bola Tinubu ya yi ba komai ba ne face cin mutunci da raina manyan mutane a Arewacin Najeriya.

Source: Facebook
Adnan Mukhtar ya yi wannan zazzafan raddi ne a wata hira da ya yi da ɗaya daga cikin wakilan Legit Hausa ranar Laraba, 19 ga watan Maris, 2024.
Matashin ɗan siyasa ya ce ƴan Arewa ba mabarata ba ne da ɗan shugaban kasar zai zo yana raba abinci, yana mai cewa hakan ba ƙaramin abin kunya ba ne.
Adnan ya caccaki ziyarar Seyi Tinubu
Ya kara da cewa abubuwan da Seyi Tinubu ya yi ya ƙara kashewa mahaifinsa kasuwa domin tuni suka fara wayar da kan jama'a kan su gujewa zaben waɗannan mutanen.
"Na ɗaya shi ba musulmi ba ne, ya zo ya yi buɗa baki da matasanmu, wani ma ya kira ni wai abin kunya ne ba a gayyace ni ba, to dan ban je na ci abinci da ɗan shugaban ƙasa ba sai menene? Ina da abincin a gidana.
"Ya zo ya raba mana abinci a leda, kamar almajirai kuma ka duba yadda ya je ya na gaisawa da sarakunanmu, ya na zama a kujera kamar gwamna, bayan ba rike yake da muƙami ba.

Kara karanta wannan
Ana tsaka da batun Ribas, tsohon ɗan takara a Kano ya caccaki shugaban matasan PDP
"Amma aka ba shi kujerar gwamna a fadar sarkin Zazzau da sarkin Damaturu, ya zauna da takalmi yake shiga fada, wanda bai isa ya yi haka a Kudu ba."
- In ji Adnan.

Source: Facebook
Seyi Tinubu ba zai yi haka a Kudu ba
Tsohon ɗan takarar Majalisar Kano ya ƙara da cewa Seyi Tinubu bai isa ya yi wa sarakunan Kudu abin da ya yi wa sarakunan Arewa ba.
"Bai isa ya shiga fadar Ooni na Ife da takalmi ba, bai isa ya ba shi hannu ba. Bai isa ya je fadar Alaafin na Oyo ya ba shi hannu ko ya shiga da takalmi ba, bai isa ya yi haka a fadar Oba na Legas ba.
"Wannan rashin mutunci ne (abin da ya yi a Arewa) kuma wannan raini ne," in ji Hon. Adnan Mukhtar.
Abubuwan da mutanen Arewa ke bukata
Adnan ya ƙara da cewa abin da al'ummar Arewa ke bukata shi ne a inganta ilimi, samar da cibiyoyin fasahar zamani (ICT), wutar lantarki, ƙarin makarantu da sauran abubuwan ci gaba.
Ya ce wannan shi ne abin da ƴan Arewa ke buƙata ba abincin da ɗan shugaban ƙasa ya raba ba, wanda iyakarshi rana guda.

Kara karanta wannan
Ba jira: Ministan Tsaro, Matawalle ya fadi shirin sojoji kan dokar ta baci a Rivers
Adnan ya soki shugaban matasan PDP
A wani labarin, kun ji cewa Hon. Adnan ya soki shugaban matasan PDP na ƙasa, Muhammad Kadade, ya ce ya kamata a tashi tsaye.
Tsohon ɗan takarar ya bayyana cewa Kadade ya gaza jagorantar matasa yadda ya kamata, ya koma ɗaukar hotuna da manyan mutane.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
