Ganduje Ya Yi Martani kan Haduwar Atiku, El Rufa'i da Obi don Kifar da Tinubu a 2027

Ganduje Ya Yi Martani kan Haduwar Atiku, El Rufa'i da Obi don Kifar da Tinubu a 2027

  • Shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce babu wata hadaka da za ta hana Bola Tinubu sake cin zabe a 2027
  • Hakan na zuwa ne bayan Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan ‘yan adawa sun sanar da sabuwar hadaka don hambarar da Tinubu
  • Abdullahi Umar Ganduje ya ce hadakar da ‘yan hamayya suka yi ba za ta yi tasiri ba, domin ba su da hadin kai a tsakaninsu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya caccaki sabuwar hadakar ‘yan adawa da suka kafa don kalubalantar Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

A cewarsa, Tinubu yana aiwatar da kyawawan manufofi tun bayan hawansa mulki, kuma ba wata dabara da za ta hana shi samun nasara a 2027.

Kara karanta wannan

"Ka da a ɗora mun laifi": Gwamna Fubara ya cire tsoro, ya ƙaryata kalaman Tinubu

Ganduje
Ganduje ya yi martani ga 'yan adawa kan zaben 2027. Hoto: Mr. Peter Obi|Atiku Abubakar|Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wani hadimin Abdullahi Ganduje ne ya yi martanin a madadinsa a karshen makon nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin na zuwa ne bayan da Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan ‘yan adawa suka hadu a Abuja, suka bayyana aniyarsu ta kifar da gwamnatin Tinubu a babban zabe mai zuwa.

Ganduje ya ce Tinubu zai sake lashe zabe

Ganduje ya jaddada cewa Tinubu zai sake lashe zabe saboda irin ci gaban da yake kokarin kawowa tun bayan hawansa mulki.

Abdulahi Ganduje ya ce duk wani shiri da ‘yan adawa ke yi ba zai hana ‘yan Najeriya sake zaben Tinubu ba, domin yana kokarin kawo sauyi a tattalin arzikin kasa.

The Guardian ta wallafa cewa hadimin Ganduje, Oliver Okpala ya jaddada wa 'yan siyasar Arewa masu son tsayawa takara a 2027 su dakata sai 2031.

Ganduje ya caccaki hadakar ‘yan adawa

Kara karanta wannan

Atiku, El-Rufai, Obi da jiga jigan APC sun hadu domin shirin kifar da Tinubu a 2027

Ganduje ya bayyana cewa hadakar ‘yan adawa ba za ta yi tasiri ba, domin ba su da cikakken hadin kai da tsari.

Shugaban APC ya ce:

"Hadakar da suka yi daga PDP zuwa LP da SDP ba ta da wani tushe mai karfi, domin kowannensu ya na da muradi na daban."

A yanzu haka 'yan Najeriya suna sauraron ganin ta hanyar da 'yan adawa za su tunkari Bola Tinubu yayin da lamarin ke cigaba da daukar hankali.

Shugaban APC din ya bayyana cewa yawancin ‘yan adawa da ke kokarin hambarar da Tinubu ba su da wata tushe mai karfi a siyasa.

Ya ce duk wata magana da Atiku da sauran ‘yan adawa ke yi ba komai ba ne face magana maras tushe.

Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Minista ya na ganin nasarar APC

A daya bangaren, ministan harkokin gidaje, Yusuf Abdullahi Ata ya ce hadakar 'yan adawa ba za ta yi tasiri ba.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Ata ya ce bayan samun jagora na gari, wato Bola Tinubu, 'yan Najeriya ba su bukatar sauyi a zaben 2027.

Fubara: Kwankwaso ya ragargaji Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi Allah wadai da matakin shugaba Bola Ahmed Tinubu na dakatar da gwamna Simi Fubara.

Kwankwaso ya yi kira ga 'yan majalisa da su rika aikin sa-ido da aka zabe su domin aiwatarwa ba su dawo 'yan amshin shatar gwamnati ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng