Fubara: Kwankwaso Ya Hade da Atiku, El Rufa'i, Obi kan Rikicin Ribas

Fubara: Kwankwaso Ya Hade da Atiku, El Rufa'i, Obi kan Rikicin Ribas

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki matakin Shugaba Bola Tinubu na dakatar da gwamnan Ribas da sauran zababbun shugabanni
  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa dokar ta-baci da aka ayyana a jihar ba ta da tushe a kundin tsarin mulki
  • Ya bukaci 'yan majalisa su daina zama 'yan-amshin shata ga bangaren zartarwa, ya ce matakin ka iya haddasa tarnaki ga dimokuradiyya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana rashin amincewarsa da matakin Shugaba Bola Tinubu na dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara.

A cewarsa, hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma hakan ka iya zama barazana ga tsarin dimokuradiyya da kasar ta gina tun 1999.

KWankwaso
Kwankwaso ya yi Allah wadai da dakatar da Fubara. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a Facebook, tsohon gwamnan Kano ya ce matakin da Tinubu ya dauka a Ribas ka iya zama wata hanyar hana 'yancin cin gashin kai na jihohi.

Kara karanta wannan

'Me shirunsa ke nufi?' An taso Kwankwaso a gaba game da dokar ta ɓaci a Rivers

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya sabawa tsarin mulki - Kwankwaso

Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa dakatar da Gwamna Fubara da sauran zababbun shugabannin jihar ya saba wa kundin tsarin mulki na 1999.

A karkashin haka, Kwankwaso ya yi Allah wadai da matakin Bola Tinubu, musamman yadda ya ke ikirarin kare domokuradiyya a Najeriya.

Menene ya sa Kwankwaso yin shiru da farko?

Sanata Kwankwaso ya yi magana ne bayan mutane sun fara surutu kan shiru da ya yi a kan lamarin yayin da 'yan adawa ke sukar matakin da Tinubu ya dauka a Ribas.

Kwankwaso ya ce shirun da ya yi, yana jira ne yaga matakin da jami'an gwamnati da abin ya shafa za su dauka, musamman majalisar tarayya.

Kwankwaso: Majalisa ta gaza yin aikinta na sa ido

Sanata Kwankwaso ya caccaki majalisar tarayya, ya na mai cewa ba ta cika aikinta na sa ido kan bangaren zartarwa ba, illa kawai bin umarnin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Fubara: Bayan majalisa, gwamnoni sun kalubalanci Tinubu kan rikicin Rivers

Ya ce yadda majalisa ta amince da bukatar Tinubu cikin gaggawa ya kara dagula lamarin, domin ba a bi ka'idojin kada kuri'a yadda ya kamata ba.

Ya kara da cewa, wajibi ne bangaren shari'a ya tsaya kan gaskiya wajen yanke hukunci, ba tare da wata tsangwama ko biyayya ga gwamnati ba.

Hana soja shiga harkokin mulki a Najeriya

Kwankwaso ya bayyana cewa shigar da sojoji cikin mulkin jihar Ribas wani babban kuskure ne da zai iya barazana ga dimokuradiyya.

Fubara
Gwamnan Rivers da aka dakatar. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Instagram

Ya tunatar da yadda tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya hana sojoji shiga harkokin siyasa a lokacin mulkinsa.

Tsohon gwamnan ya bukaci shugaba Tinubu da ya sauya matsayarsa kan lamarin Ribas domin bai wa dimokuradiyya damar ci gaba da gudana yadda ya kamata.

Gwamnatin Fubara ta bukaci dakatar da Wike

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Rivers da gwamna Siminalayi Fubara ya jagoranta ta yi Allah wadai da matakin da Bola Tinubu ya dauka na kin dakatar da Nyesom Wike.

Gwamnatin ta ce idan akwai wanda ya kamata a dakatar a kan abin da ke faruwa a jihar to shi ne ministan birnin tarayya, Nyesom Wike.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel