'Me Shirunsa ke Nufi?' An Taso Kwankwaso a Gaba game da Dokar Ta Ɓaci a Rivers

'Me Shirunsa ke Nufi?' An Taso Kwankwaso a Gaba game da Dokar Ta Ɓaci a Rivers

  • Sanata Rabiu Kwankwaso yana fuskantar suka daga jama'a saboda kin fadin ra'ayinsa kan dokar ta-ɓacin da aka kafa a jihar Rivers
  • Wani ɗan PDP ya bayyana damuwarsa, ya na tambayar dalilin da ya sa Kwankwaso bai bayyana matsayinsa ba kamar sauran shugabannin adawa
  • Ya ce Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai da Kungiyar Gwamnoni duk sun yi magana, amma har yanzu Kwankwaso bai ce komai ba
  • Matashin ya tambaya ko Kwankwaso na da niyyar shugabantar adawa ganin yadda har yanzu bai kare muradin 'yan hamayya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - An taso Sanata Rabiu Kwankwaso a gaba kan rashin yin magana game da sanya dokar ta-ɓaci a jihar Rivers.

Manyan ƴan adawa a Najeriya sun yi martani kan lamarin inda suke sukar matakin da Bola Tinubu ya dauka a jihar.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ɗan PDP ya aikawa sanatansa sako ya hana dakatar da Fubara a Majalisa

Ana zargin Kwankwaso bayan yaki cewa komai game da dokar ta-ɓaci a Rivers
Jama'a sun taso Rabiu Musa Kwankwaso a gaba game da dokar ta-ɓaci a Rivers. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Twitter

An bukaci sanin matsayar Kwankwaso kan dokar ta-ɓaci

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da @AdnanMouckhtar ya wallafa a shafin X a yau Alhamis 20 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adnan matashin 'dan siyasa wanda sau biyu ya na neman damar tsayawa takarar 'dan majalisa a jihar Kano, amma bai yi nasara ba.

A cikin rubutun, malamin jami'ar ya tambaya shin menene matsayar Rabiu Kwankwaso duba da yadda bai ce komai ba game da lamarin da ya faru a jihar Rivers.

Matashin ya bayyana cewa:

“Atiku Abubakar ya yi magana, haka ma Peter Obi, Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta fadi albarkacin bakinta, El-Rufai ma bai yi shiru ba.
“Yawancin ‘yan adawa sun riga sun bayyana matsayinsu, amma Rabiu Kwankwaso bai ce uffan ba, saboda wani dalili da shi kadai ya sani.
“Wasu mutane kuwa sai ihu suke, suna kiransa jagoran adawa, amma har yanzu bai yi magana ba domin kare muradin kasa ko bayyana matsayinsa.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

“To yanzu, yaushe ne Kwankwaso zai fito fili ya yi magana? Shin da gaske ne yana shirin jagorantar adawa a kasar nan?”
Ana zargin Kwankwaso bayan kin magana game da dokar ta-ɓaci a Rivers
An taso Kwankwaso a gaba game da rashin cewa komai bayan sanya dokar ta-ɓaci a Rivers. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Facebook

Rivers: Martanin mutane game da shirun Kwankwaso

Mutane da dama sun yi martani kan lamarin inda wasu ke cewa Kwankwaso bai cancanci zama jagoran adawa a Najeriya ba.

@BashirAhmaad:

"Shirin haɗewa mana, Kwamred."

@Tahirtalba:

"Wani lokaci shiru fa alheri ne."

@JACOB_EML:

"Kwankwaso ba dan siyasar kasa ba ne kawai jagora ne a masarautar Kano."

@Anthonyapakboro:

"Ni kam waye ne ma Kwankwaso kam?"

@Educatedlawyer:

"Wannan lamari ne na kasa da ya fi ƙarfinsa, ya kamata ya mayar da hankali ne kan siyasar Kano kawai."

@otuo_ogbajie:

"Bayan wannan, wani da ake kira Buba Galadima zai fito yana yaudaran kansa cewa Kwankwaso kwararren dan siyasa ne."

Rivers: 'Dan PDP ya tura sako ga sanatansa

A baya, kun ji cewa wani matashi dan jam'iyyar PDP a Kaduna, Aliyu Kwarbai ya tura sako ga Sanata Ibrahim Khalid Soba kan dokar ta-ɓaci a Rivers.

Kara karanta wannan

Rivers: Atiku ya sauya salo, ya roƙi ƴan Najeriya bayan Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci

Matashin ya roki sanatan ka da ya goyi bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara daga kujera, yana cewa hakan zai bar baya da kura a jihar.

Kwarbai ya bayyana cewa ya taimaka wurin yakin neman zaben sanatan a 2023, amma bai taba neman wani abu a wajensa ba sai a yanzu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng