Kaduna: Ɗan PDP Ya Aikawa Sanatansa Sako Ya Hana Dakatar da Fubara a Majalisa
- Wani matashi dan jam'iyyar PDP a Kaduna, Aliyu Kwarbai ya tura sako ga Sanata Ibrahim Khalid Soba kan dokar ta-ɓaci a Rivers
- Kwarbai ya roki sanatan ka da ya goyi bayan cire Gwamna Simi Fubara daga kujera, yana cewa hakan zai bar baya da kura a jihar
- 'Dan siyasar ya bayyana cewa ya taimaka wurin yakin zaben sanatan a 2023, amma bai taba neman wani abu a wajensa ba
- Ya roƙi Soba da ya tsaya tsayin daka wajen kare dimukradiyya da adalci, yana cewa hakan ne abin da ya dace da shugaba na gari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Wani daga cikin matasan 'yan siyasa a jam'iyyar PDP a jihar Kaduna ya tura sako ga sanatansa kan dokar ta-ɓaci a Rivers.
Matashin mai suna Aliyu A. Kwarbai ya tura sakon ne da yake rokon Sanata Ibrahim Khalid Soba ya ki amincewa da tabbatar da dokar.

Asali: Twitter
Rivers: 'Dan PDP ya roki Sanatansa daga Kaduna
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Aliyu Kwarbai ya wallafa a shafin X a yau Alhamis 20 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, matashin ya ce ya tura sakon ne ga Sanata Ibrahim Khalid Soba da ke wakiltar Kaduna ta Arewa a Majalisar Dattawa.
Kwarbai wanda ya so tsayawa takarar shugaban karamar hukumar Zariya, ya roki Sanatan ka da ya amince da bukatar shugaban kasa.
An bukaci majalisa ta yi na'am a dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara daga kujerarsa a jihar.
Matashin ya ce hakan zai kare dimukradiyya da kuma wasu abubuwa da ka iya biyo bayan amincewa da cire gwamnan.
A cikin rubutunsa ya ce:
"Ina kwana, jajirtaccen sanatan yankina, sunana Aliyu Kwarbai, mun yi magana na karshe ne tun ana saura mako daya a yi zaben ka.

Kara karanta wannan
Rivers: Atiku ya sauya salo, ya roƙi ƴan Najeriya bayan Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci
"A matsayina na ɗan a mutun PDP, na ba da gudunmawa wurin yakin neman zabenka kuma ban taba neman wani taimako a wurinka ba saboda na san halin da ake ciki.
"Amma a yau zan nema, duk yadda za a yi ka da ka goyi bayan cire Gwamna Fubara a Rivers, ka kare dimukradiyya, Nagode sanatana."

Asali: Twitter
Martanin wasu masu amfani da kafar X
Wasu masu ta'ammali da shafin X sun bayyana ra'ayinsu kan sakon matashin ga Sanatan da ke wakiltarsa a mazabar Kaduna ta Arewa.
@Tazaya_:
"Har yanzu shi yake wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa?"
@hithertOO:
"Wannan ai dan zaman benci ne, abin da su ke so kawai zai yi."
@kabir_baba:
"Mai girma Sanata ba."
@salisuahmed51:
"Kuma ba zai taba mayar da martani ba."
@GodwinC15:
"Dalilin haka, ka sa na fara bibiyar shafinka."
Atiku ya caccaki Tinubu kan sanya dokar ta-ɓaci
Mun ba ku labarin cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar, ya bukaci 'yan Najeriya su tashi tsaye su kare dimokuradiyya daga dokar ta-baci a Rivers.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa tilas ne a hana wannan yunkuri na kifar da gwamnatin da aka zaba ta hanyar doka marar dalili.
Atiku ya fadi hakan ne a Abuja yayin wani taron manema labarai na wasu shugabannin siyasa da ke nuna damuwa kan halin da ake ciki a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng