Fubara: Bayan Majalisa, Gwamnoni Sun Kalubalanci Tinubu kan Rikicin Rivers

Fubara: Bayan Majalisa, Gwamnoni Sun Kalubalanci Tinubu kan Rikicin Rivers

  • Gwamnonin Kudu maso Kudu sun kalubalanci Bola Tinubu kan matakin sanya dokar ta-baci a jihar Rivers da dakatar da Siminalayi Fubara
  • Sun ce rikicin siyasar jihar bai ya jawo a dauki matakin gaggawa ba, kuma su bayyana hanyoyin da ya kamata a bi wajen warware matsalar
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnonin yankin sun gargadi gwamnatin tarayya da kada ta karya tsarin mulki da dimokuradiyya a jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Kungiyar gwamnonin yankin Kudu Maso Kudu ta bukaci Bola Ahmed Tinubu da ya janye dokar ta-baci da ya ayyana a jihar Rivers.

Gwamnonin yankin sun bukaci maido da zababbun jami’an gwamnati da aka dakatar, ciki har da gwamna Siminalayi Fubara.

Kudu maso Kudu
Gwamnonin Kudu maso Kudu sun bukaci dawo da Fubara. Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar the Cable ta wallafa cewa gwamnonin sun bukaci a bi hanyar laluma wajen magance rikicin siyasar jihar.

Kara karanta wannan

Ribas: An fallasa yadda Wike da gwamnatin Tinubu suka kitsa dakatar da Fubara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Douye Diri na Jihar Bayelsa, wanda shi ne shugaban kungiyar, ya ce gwamnonin sun bayyana cewa rikicin siyasa da ke gudana a jihar bai kai a dauki matakin dokar ta-baci ba.

Bukatar bin doka da tsarin mulki

Gwamnonin sun amince da rawar da Shugaban Kasa ke takawa wajen tabbatar da doka da oda, amma sun bukaci da a mutunta ikon gwamnonin a yankinsu.

Rahoton Channels TV ya nuna cewa sun ce Sashe na 305(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya fayyace sharuddan da za a iya ayyana dokar ta-baci, ciki har da:

  • Yaki ko mamaya daga kasashen waje
  • Rugujewar doka da oda
  • Barazana ga hadin kan kasa

A cewarsu, babu wani daga cikin wadannan dalilai da ya faru a Jihar Rivers da zai halatta matakin da shugaba Tinubu ya dauka.

Zargin take hakkin wadanda aka zaba

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

Kungiyar ta kuma jaddada cewa kundin tsarin mulki ya yi bayani filla-filla kan yadda ake cire Gwamna da Mataimakinsa, kamar yadda Sashe na 188 ya tanada.

Sun ce dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Rivers ba tare da bin matakan doka ba, ya sabawa tsarin mulki.

Bayan saba tsarin mulki, gwamnonin sun ce matakin ya kasance barazana ne ga tsarin dimokuradiyya.

Gwamnonin sun yi gargadi cewa kada gwamnati ta saba doka domin cimma muradunta na siyasa, inda suka bukaci a bi hanyoyin shari’a wajen warware rikicin siyasar Rivers.

Fubara
Gwamnan Rivers da aka dakatar. Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Bukatar maido da dimokuradiyya a Rivers

Gwamnonin sun bukaci gwamnati ta gaggauta kawo karshen dokar ta-bacin tare da mutunta tsarin mulki.

Sun kuma bukaci bangarorin da ke rikici a Jihar Rivers su yi amfani da hanyoyin siyasa da doka wajen warware matsalolinsu, maimakon amfani da karfi.

Kara karanta wannan

El-Rufa'i ya aika da sako ga Tinubu kan dakatar da zababben gwamnan Ribas

Sun kammala da cewa matakin da Shugaban Kasa ya dauka zai iya zama barazana ga sauran jihohin Najeriya, don haka dole ne a dakatar da shi domin kare dimokuradiyya.

Rivers: 'Yan adawa sun kalubalanci Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa manyan 'yan adawa a Najeriya sun kalubalanci shugaba Bola Tinubu kan sanya dokar ta-baci a jihar Rivers.

'Yan adawar da suka hada da Atiku, Nasir El-Rufa'i sun bukaci a maido da gwamna Siminalayi Fubara da sauran wadanda aka dakatar a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng