Magana Ta Kare: Atiku Ya Tabbatar da Shirin Kawar da Tinubu a 2027
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya tabbatar da shirin jam'iyyun adawa na yin haɗaka a don tunkarar zaɓe
- Atiku Abubakar ya ba da tabbacin cewa haɗakar za ta zama babbar hamayya ga jam'iyyar APC da shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027
- Hakan dai na zuwa ne bayan ƴan adawa sun sha kiran haɗewa a waje ɗaya domin karɓo mulki a hannun jam'iyyar APC da Bola Tinubu
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya kuma soki matakin da Tinubu ya ɗauka na ƙaƙaba dokar ta ɓaci a jihar Rivers wacce ke da arziƙin mai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi magana kan haɗaka don kawar da Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Atiku Abubakar ya tabbatar da kafa wata haɗaka da nufin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki da Bola Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan
Atiku, El-Rufai, Obi da jiga jigan APC sun hadu domin shirin kifar da Tinubu a 2027

Asali: Facebook
Atiku ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis, 20 ga watan Maris, 2025, a cibiyar Shehu Musa Yar’adua da ke Abuja, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron ya tara shugabanni da manyan ƴan siyasa masu ruwa da tsaki a Najeriya, inda aka mayar da hankali kan matakin da shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na ayyana dokar ta ɓaci a jihar Rivers kwanaki biyu da suka gabata.
Atiku ya tabbatar da shirin haɗakar ƴan adawa
Lokacin da aka tambaye shi ko wannan sabuwar haɗakar za ta zama babbar hamayya ga APC a zaɓen da ke tafe na 2027, Atiku ya tabbatar da hakan da hanyar cewa “Eh.”
Tabbacin da ya bayar ya nuna sabon tsarin sake fasalin siyasar Najeriya, jam’iyyun adawa na ƙoƙarin haɗa kai domin ƙalubalantar jam'iyyar APC a zaɓen 2027.
Ko da yake cikakkun bayanai kan wannan haɗaka ba su fito fili ba tukuna, matakin ya nuna an fara yunkurin samar da hadin kai a tsakanin ƴan adawa don tunkarar jam’iyyar mai mulki.
Hakazalika, a lokacin taron, Atiku da sauran ƴan siyasa sun yi tir da dokar ta ɓacin da aka kakabawa jihar Rivers.
Sun bayyana hakan a matsayin matakin da ya saɓwa kundin tsarin mulkin Najeriya kuma da nufin kassara dimokuraɗiyya a ƙasar nan.
Matsayar jam'iyyar NNPP kan yin haɗaka
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban ƙusa a jam'iyyar SDP, Buba Galadima, ya yi tsokaci kan shirin haɗaka da wasu jam'iyyun suke yi.
Buba Galadima ya bayyana cewa jam'iyyar NNPP ba za ta shiga wata haɗaka ba da aka gina da nufin ƙwace mulki ko ta halin ƙaƙa.
Babban jigon ya bayyana cewa za su tsaya su gina jam'iyyar NNPP ta yadda za ta iya babban zaɓe a ƙasar nan a nan gaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng