Rivers: Atiku Ya Sauya Salo, Ya Roƙi Ƴan Najeriya bayan Tinubu Ya Sanya Dokar Ta Ɓaci
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci 'yan Najeriya su tashi tsaye su kare dimokuradiyya daga dokar ta-baci a Rivers
- Atiku ya bayyana cewa tilas ne a hana wannan yunkuri na kifar da gwamnatin da aka zaba ta hanyar doka marar dalili da inganci
- Ya fadi hakan ne a Abuja yayin wani taron manema labarai na wasu shugabannin siyasa da ke nuna damuwa kan halin da ake ciki a jihar
- Atiku ya ce kare dimokuradiyya ba aikin jam'iyyun adawa kawai ba ne, amma aikin kowa da kowa da ke kaunar gaskiya da doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya sake yin magana kan dokar ta-ɓaci da aka sanya a jihar Rivers.
Atiku Abubakar ya ce dole ne 'yan Najeriya su tashi tsaye su kare dimokuradiyya daga kokarin yi mata illa da ake yi.

Asali: Twitter
Tsohon mataimakin shugaban ya yi wannan magana ne a Abuja a yau Alhamis 20 ga watan Maris, 2025, cewar rahoton TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a Rivers
Wannan martani na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya ɗauki mataki kan rikicin siyasar da ya addabi jihar Rivers mai arziƙin mai a Kudancin Najeriya.
Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a jihar bayan abubuwa sun dagule tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da majalisar dokoki.
Mabanbantan ra'ayi kan dokar ta-ɓaci a Rivers
Shugaban ya kuma dakatar da gwamnan tare da mataimakiyarsa har na tsawon watanni shida, ya nada sabon shugaban rikon kwarya a jihar.
Wannan mataki na Tinubu ya jawo ka-ce-na-ce a cikin kasa yayin da aka samu mabambantan ra'ayoyi duba da ikirarin cewa ya saba kundin tsarin mulki.
Masana harkokin shari'a da siyasa sun yi ta fadin ra'ayinsu game da dokar wanda har yanzu majalisar tarayya ba ta gama zama domin goyon baya ko sabanin haka kan lamarin ba.

Asali: Facebook
Rivers: Abin da Atiku ya ce kan dokar ta-ɓaci
Tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP ya fadi hakan yayin wani taro na musamman da shugabannin siyasa suka shirya.
Ya ce kare dimokuradiyya ba aikin jam’iyyun adawa kawai ba ne, amma nauyi ne da ya rataya kan duk wani mai kishin kasa, Vanguard ta ruwaito.
Ya kara da cewa wajibi ne a ki yarda da wannan “mummunan hari” da ake kaiwa kan gwamnatin da aka zaba ta hanyar kuri’a a Rivers.
Halin kunci: Atiku ya yabawa 'yar bautar ƙasa
A baya, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya tsoma baki kan dambarwar da ake yi tsakanin Hukumar NYSC da matashiya mai bautar ƙasa.
Atiku na daga cikin wadanda suka ba ta kwarin gwiwar tabbatar da an samu sauyi mai dorewa a Najeriya, musamman a yanayin da ake ciki.
Jigon jam'iyyar PDP ya bayyana cewa, matasa irin Raye ne ke tashi domin tabbatar da an samu sauyi a fannin siyasa da ci gaban kasa mai girma irin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng