Shugaba Bola Tinubu ke Daukar Nauyin SDP? Jam'iyyar Ta Yi Magana

Shugaba Bola Tinubu ke Daukar Nauyin SDP? Jam'iyyar Ta Yi Magana

  • Jam'iyyar SDP ta kasa kauda kai kan jita-jitar da ake yaɗawa cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne yake ɗaukar nauyinta
  • Sakataren jam'iyyar SDP na ƙasa ya fitar da wata sanarwa a ranar Laraba, inda ya yi martani kan jita-jitar da ake ta yawo da ita
  • Araba Rufus Ayenigba ya ce duk da akwai alaƙa a tsakanin Tinubu da SDP a baya, ko kaɗan ba shi ne yake samar mata da kuɗi ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam'iyyar SDP ta yi martani kan batun cewa Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne yake ɗaukar nauyinta.

Jam'iyyar SDP ta ƙaryata jita-jitar da yawo mai cewa Tinubu ne yake da ita, inda ta bayyana hakan a matsayin zuƙi ta malle.

SDP ta ce Tinubu bai daukar nauyinta
SDP ta musanta cewa Tinubu ke daukar nauyinta Hoto: Alhaji Shehu Gabam, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar SDP na ƙasa, Araba Rufus Ayenigba, ya fitar ga manema labarai a Abuja, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Atiku ya tabbatar da shirin kawar da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce jam'iyyar ba ta yi niyyar yin martani kan jita-jitar ba, amma ta yi martanin ne duba da irin girman ƙaryar da ake yaɗawa a kanta.

Ya bayyana cewa shugabannin jam'iyyar sun sha samun kiran waya inda ake tambayarsu cewa Shugaba Bola Tinubu ne ke ɗaukar nauyin SDP.

Wane martani jam'iyyar SDP ta yi?

"Da farko, mun yanke shawarar cewa ba za mu bayar da wata amsa ga wadannan maganganu marasa tushe ba, don kar su samu wata daraja."
“Amma bayan tunani mai zurfi da kuma la’akari da yawan kiran da muke samu daga ƴan Najeriya masu kishin ƙasa, mun yanke shawarar mayar da martani."
"SDP jam’iyya ce ta ƙasa wacce ke tafiya bisa tsarin kundinta na mulki, kuma tana aiki da aƙida wacce ta sanya mutane a gaba."
"Babu wani mutum guda da ke da jam’iyyar SDP, kuma babu wani uban gida da take da shi, ƴan Najeriya ne ke da jam’iyyar."

Kara karanta wannan

Kiranye daga majalisa: Sanata Natasha ta fadi aɓin da take tsoro

"Duk da cewa SDP ce ta zama tushen siyasar Shugaba Tinubu, inda ta ba shi damar takara da lashe kujerar Sanata mai wakiltar Legas ta Yamma tare da Sanata Kofoworola Akerele-Buknor da Sanata Anthony Adefuye a zaben da aka soke na Jamhuriya ta uku."
"Babu wata alaƙa ko hulɗa ta siyasa tsakanin jam’iyyar da shugaban ƙasa ko wakilansa."
"Jam’iyyar ta dogara da kanta wajen samun kuɗinta daga gudunmawar mambobinta a duk faɗin ƙasar nan."
"SDP ba ta shiga wata haɗaka da kowace jam’iyya ba, kuma ba za ta shiga kowace haɗaka ba."

- Araba Rufus Ayenigba

Shugaban SDP ya faɗi kuskuren Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa, Alhaji Shehu Gabam, ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tafka kan manufofin da ya ɓullo da su a ƙasar nan.

Shugaban na SDP ya bayyana cewa manufofin shugaba Bola Tinubu kan tattalim arziƙi za su ba shi cikas a zaɓen shekarar 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel