An Jero Abubuwa 2 da El Rufai Zai Yi Amfani da Su wajen Karya Tinubu da APC a 2027
- An faɗawa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai abubuwa biyu da zai yi amfani da su wajen samun nasara kan Shugaba Bola Tinubu a 2027
- Shugaban ƙungiyar Citizens Coalition, Kelly Agaba, ya ce damar El-Rufai na yin nasara a kan APC ta dogara ne kan wasu muhimman abubuwa
- Legit.ng ta ta tattaro cewa El-Rufai na ta ƙoƙarin tattara ‘yan siyasar adawa don su haɗu a jam’iyyar SDP domin fatattakar shugaba Tinubu a zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban ƙungiyar Citizens Coalition, Kelly Agaba, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, na da damar da zai kayar da APC.
Mista Agaba ya ce El-Rufai zai iya kalubalantar gwamnatin APC karkashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu duba da tarihinsa a siyasa da muƙaman da ya riƙe.

Kara karanta wannan
A karon farko, jam'iyyar APC ta kasa ta yi maganar sauya shekar El Rufai zuwa SDP

Asali: Facebook
A rahoton Punch, El-Rufai na ci gaba da jan hankalin manyan ƴan siyasa, akwai yiwuwar tsofaffin ministoci, tsofaffin gwamnoni da jiga-jigai su bi shi zuwa SDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gogewa da basirar Nasir El-Rufai a siyasa
Da yake hira da Legit.ng, Agaba ya ce El-Rufai mutum ne da ake mutuntawa da girmamawa bisa la'akari da hangen nesansa da kuma ƙarfinsa a siyasar Najeriya.
Agaba ya ce El-Rufai yana da ƙwarewar da ake buƙata don kawo sauyi mai kyau, duba da cewa ya taɓa riƙe muƙamin minista da gwamna a gwamnatocin da suka gabata.
Masanin al'amuran siyasar ya ce tsohon gwamnan ya yi ƙaurin suna a matsayin mai tunani mai zurfi da kuma ƙwarewa wajen tattara jama'a.
Agaba ya bayyana cewa damar El-Rufai na samun nasara a kan shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC a 2027 za ta dogara ne kan iyawarsa na samun goyon baya da gina ƙawance mai ƙarfi.

Kara karanta wannan
'Ka nemi afuwa': Gidauniyar Dahiru Bauchi ga El-Rufai, ta ba shi wa'adi kafin ƙarshen Ramadan
Abubuwan da za su taimaki El-Rufai a 2027
"A matsayinsa na mutum mai basira, Nasir El-Rufai ya yi suna da kaifin tunani da kuma ƙwarewa wajen tattara jama'a. Kwarewarsa a matsayin minista da gwamna ta ba shi gogewar da ake buƙata don kawo sauyi mai kyau.
“Dangane da karɓuwarsa a wurin jama'a, ra’ayoyi na iya bambanta saboda halayensa da kuma kafiyarsa kan al’amura. Duk da haka, jajircewarsa ga ci gaban Najeriya ba za a musanta ta ba.
“Idan aka duba 2027, damar El-Rufai na kalubalantar gwamnatin jam’iyyar APC mai ci za ta dogara ne kan abubuwa da dama, ciki har da iya samun goyon baya da gina ƙawance mai ƙarfi.”
- In ji Agada.
Daga ƙarshe, ya bayyana cewa wuƙa da nama na hannun ƴan Najeriya, domin su ne za su yanke wanda suke so ya shugabance su.
"A ƙarshe, hukunci na hannun ƴan Najeriya, waɗanda za su zaɓi shugaban da suke ganin zai kawo wadata da ci gaban ƙasa," in ji shi.
El-Rufai ya tona shirin Tinubu a kansa
A wani rahoton, kun ji cewa El-Rufai ya yi zargin cewa Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya karɓo kwangila daga wurin Bola Tinubu domin ya karya shi a siyasa.
El-Rufa'i ya ce Uba Sani ya karɓi wan nan kwangila ne saboda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tana fargabar cewa zai yi adawa da ita a nan gaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng