Buba Galadima Ya Fadi Matsayar NNPP kan Hadaka da 'Yan Adawa
- Buba Galadima ya caccaki ƴan siyasan da ke komawa jam'iyyar APC bayan sun yi takara a wasu jam'iyyun
- Jigon na jam'iyyar NNPP ya kuma bayyana SDP a matsayin wani reshe na APC mai mulki a tarayyar Najeriya
- Injiniya Galadima ya nuna cewa NNPP ba za ta shiga wata haɗaka ba da nufin ƙwace mulki ko ta halin ƙaƙa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Babban jigo a jam’iyyar NNPP, Alhaji Buba Galadima, ya yi watsi da sauya sheƙar da wasu ƴan siyasa suke yi zuwa SDP.
Buba Galadima ya bayyana cewa SDP ba komai ba ce illa wani reshen jam’iyya mai mulki, wato APC.

Asali: Facebook
Jigon na NNPP ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana a wani shiri na tashar Arise Tv a ranar Talata, 18 ga Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Buba Galadima ya ce kan SDP?
Buba Galadima ya ce babu wani abin mamaki dangane da rashin ganin jiga-jigan NNPP suna komawa SDP, domin a cewarsa, jam’iyyar wani reshe ne na APC.
"SDP da kuka ambata a gabatarwarku wani reshen APC ce. Mutanen APC ne suka koma abin da kuke kira SDP. Babu wani abu daban."
“Waɗanne mutane daga wasu jam’iyyu suka koma SDP? Wannan shi ne tambayar da mutane ya kamata su yi. Saboda haka, babu abin mamaki. Kun san irin salon siyasar Legas, yin duk mai yiwuwa don murƙushe ƴan adawa."
- Buba Galadima
Jawabin Galadima ya biyo bayan kiran da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi na cewa ya kamata shugabannin ƴan adawa su haɗu a SDP domin su ƙwace mulki daga APC a 2027.
Buba ya soki ƴan adawar da ke komawa APC
Buba Galadima ya kuma caccaki ƴan siyasar adawa da ke komawa APC bayan sun tsaya takara a wasu jam’iyyu.

Kara karanta wannan
A karon farko, jam'iyyar APC ta kasa ta yi maganar sauya shekar El Rufai zuwa SDP
Ya kawo misalin tsohon ɗan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a jihar Legas, Abdul-Azeez Adediran (Jandor), wanda ya koma APC a ranar Litinin.
"Kalli abin da Jandor ya yi. Ka kalli irin goyon bayan da mutanen Legas suka ba shi. A gaskiya, zan ce shi ne ya lashe zaɓen, kawai an ƙwace masa ne.”
“Amma ka dube shi, ya koma baya ya sake komawa APC. Yaya za mu yi adawa idan mutane na komawa baya? Ya kamata muyi adawa bisa tsari da ƙa’ida. Ko da kai kaɗai ne, ya kamata ka tsaya kan abin da ka yarda da shi."
- Buba Galadima
NNPP ba za ta yi haɗaka don neman mulki ba
Sai dai, Buba Galadima ya jaddada cewa NNPP ba za ta yi haɗaka da wata jam’iyya don samun mulki ba.
“Mu jam’iyya ce mai aƙida. Mu jam’iyya ce mai tsari. Ba ma shiga haɗaka da wasu kawai don mu samu mulki ko ta halin ƙaƙa."
“Mun gamsu da jam'iyyar da muke da ita. Wata rana, za mu ƙarfafa jam’iyyar nan mu lashe zaɓen ƙasa."
- Buba Galadima
Buba Galadima ya magantu kan saukar farashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Buba Galadima, ya bayyana cewa saukar da farashin abinci ke yi a ƙasar nan ba abin farin ciki ba ne.
Buba Galadima ya bayyana cewa saukar da farashin ya yi saboda shigo da abinci daga ƙetare, zai haifar da matsaloli a nan gaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng