El Rufa'i: "Kwangilar Tinubu ce Uba Sani Ya Karbo domin Karya Ni a Siyasa"

El Rufa'i: "Kwangilar Tinubu ce Uba Sani Ya Karbo domin Karya Ni a Siyasa"

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya yi zargin cewa Gwamna Uba Sani ya karɓi kwangila daga Shugaban Ƙasa domin bata shi
  • Ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta san ta yi masa laifi, wanda hakan ya sa ta dauki Uba Sani ya kawo masa cikas kafin zaben 2027
  • Tsohon gwamnan ya bayyana irin ladan da gwamnatin tarayya ke mikawa jihar Kaduna, lamarin da ya ke ganin ba za a yi nasara ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya zargi gwamnan jihar, Uba Sani, da karɓar kwangila daga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu domin durƙusar da shi a siyasa kafin zaɓen 2027.

El-Rufa'i ya yi wannan bayani ne bayan kalaman da gwamna Uba Sani ya yi kan bashin da tsohuwar gwamnatin Kaduna ta karɓa, wanda ya ce ba za a iya biya ba.

Kara karanta wannan

'Yadda Ribadu ya hada kai da ICPC domin kai ni kurkuku kafin zaben 2027' - El-Rufai

Kaduna
El Rufa'i na zargin Uba Sani da karbo kwangilar durkusar da shi Hoto: Nasir El-Rufa'i/Bayo Onanuga/Uba Sani
Asali: Facebook

A wata hira da aka yi da shi a Freedom Radio Kaduna, wacce aka wallafa a shafin YouTube, tsohon gwamnan ya zargi gwamnatin Uba Sani da gazawa, saboda rashin ilimi da fasahar aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufa'i: "An ba Uba Sani kwangilar karya ni"

A cewar El-Rufa'i, Uba Sani ya karɓi wannan "kwangila" ne saboda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tana fargabar cewa zai yi adawa da ita a nan gaba.

Ya ce:

“Abin da ya sa Uba Sani ya fito yana wannan magana shi ne domin an ba shi kwangila.
An ba shi kwangila ne da cewa: ‘Ka zo ka bata, ka karya, ka durƙusar da Nasiru El-Rufai, domin muna ganin zai yaki Tinubu a nan gaba.’”
“Mun yi masa laifi, mu na ganin zai yaki Tinubu nan gaba, ka taimake mu, ka durƙusar da shi a siyasance. Saboda haka, ka fito da maganar bashin nan, mu kuma za mu riƙa tallafa maka.”

Kara karanta wannan

"40% ake ba shi," El Rufai ya zargi Uba Sani da yin kashe mu raba da ƴan kwangila

El-Rufa'i: "Ribar kwangilar da Uba Sani ya Karɓo"

Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya na ba wa Gwamna Uba Sani lada ta hanyar ba shi kuɗin gudanar da ayyuka a Kaduna.

Ya ce:

“Za mu riƙa ba ka kuɗi domin ka yi ayyukanka, ka yi sace-sacenka idan kana so ka yi, amma ka gama da wannan mutumin don shi haɗari ne. Wannan ita ce kwangilar da Uba Sani ya karɓa.”

"Gwamnatin Kaduna ta gaza," El-Rufa'i

El-Rufa'i ya zargi gwamnatin Jihar Kaduna da rashin sanin yadda za a biya basussukan da ake da su domin inganta rayuwar jama’a.

Kaduna
Tsohon gwamnan Kaduna ya ce gwamnatinsa ta yi aiki Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Ya ƙaryata zargin cewa gwamnatinsa ta karɓi bashi fiye da ƙima, yana mai cewa ko a watan da ya bar mulki, sai da gwamnatinsa ta tara kuɗin shiga da ya kai N6bn zuwa N7bn.

Tsohon gwamnan ya ce:

“Uba Sani yana cewa wai kowane wata ana cire N4bn saboda basussukan da muka ci, ko ba haka ya faɗa ba? Saboda haka ya kasa biyan albashi.”

Kara karanta wannan

'Za ku ga karshen su,' El Rufa'i ya yi Allah ya isa ga 'yan majalisar Kaduna

“To, watan da muka bar gwamnati, kuɗin shiga da muka tara, N6bn ne ko N7bn. Ka fahimta? Wanda ya kusa ninka abin da ya ce ake cire masa. Saboda haka, ya kamata su tsaya su duba.”

Ya ce dole ne gwamnatin ta nutsu domin ta mori gwadaben ci gaban tattalin arziki da gwamnatinsa ta dora jihar Kaduna a kai.

El-Rufa'i ya zargi Uba Sani da 'sata'

A wani labarin, kun ji yadda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, ya zargi magajinsa, Gwamna Uba Sani, da karkatar da kuɗin kananan hukumomi na jihar zuwa Turai.

El-Rufa'i ya yi ikirarin cewa Gwamna Uba yana amfani da waɗannan kuɗin talakawan jiharsa wajen sayen kadarori a ƙasashen Seychelles, Afrika ta Kudu, da Birtaniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel