2027: Jigon APC Ya Yi Hangen Nesa, Ya Fadi Abin da Zai Hana Tinubu Yin Tazarce

2027: Jigon APC Ya Yi Hangen Nesa, Ya Fadi Abin da Zai Hana Tinubu Yin Tazarce

  • Wani babban ƙusa a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Olatunbosun Oyintiloye, ya yi watsi da barazanar da ƴan adawa za su iya yi wa Bola Tinubu a 2027
  • Jigon na APC ya bayyana cewa babu wata haɗakar ƴan adawa da za ta iya kawo cikas ga shirin tazarcen Shugaba Tinubu a zaɓen 2027
  • Oyintiloye ya nuna cewa shugaban ƙasan ya san dabaru iri-iri saboda gogewar da yake da ita a fagen siyasa
  • Ya shawarci ƴan adawa da su je su yi karatun ta natsu, su fahimci wane irin mutum ne mai girma Shugaba.Bola Tinubu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Osun - Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Olatunbosun Oyintiloye, ya yi magana kan takarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Jigon na APC ya ce babu ficewar mambobin jam’iyyar ko ƙawancen ƴan adawa da zai iya kayar da Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

Bayan sutale El Rufai, APC ta fadi abin koyi daga Muhammadu Buhari

Jigon APC ya kare Bola Tinubu
Jigon APC ya ce Tinubu zai yi tazarce a 2027 Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Olatunbosun Oyintiloye ya yi wannan bayanin ne yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Lahadi a Osogbo, babbar birnin jihar Osun, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon na APC ya yi wannan martani ne dangane da ficewar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, daga APC zuwa jam’iyyar SDP.

Jigon APC ya hango nasarar Tinubu a 2027

Oyintiloye ya ce duk wata haɗakar siyasa ba za ta iya hana Tinubu zarcewa kan wa'adi na biyu ba a 2027, rahoton Tribune ya tabbatar.

Jigon na APC ya ce ƴan siyasar da suke adawa da shugaban ƙasa za su gane kuskuren da suke yi na rashin mara masa baya.

“Waɗanda ke taruwa domin su ƙalubalance shi kafin 2027, ya kamata su yi kokarin fahimtar wane irin mutum ne Shugaba Bola Tinubu."
"Ya na da dabarar nasara, kuma yana horar da maza da mata masu kyakkyawan fata a faɗin Najeriya."
“Shugaban ƙasa zai yi nasara, kuma masu adawa da shi za su gane kuskuren da suke yi na rashin mara masa baya."

Kara karanta wannan

SDP ta tono 'makarkashiyar' da gwmanatin APC ke shiryawa El Rufai

"Waɗanda ke wasu ƙananan maganganu a kansa ya kamata su duba tarihin ayyukansa, nasarorinsa, da shahararsa a faɗin Najeriya."
"Ƙarfin siyasar Tinubu, tasirinsa, da jajircewarsa waɗanda suka ba shi damar shawo kan dukkan ƙalubale ya yi nasara a 2023, za su sake ba shi damar samun nasara a 2027.”

- Olatunbosun Oyintiloye

Talaka ne zai raba gardama

Kabir Lawal ya bayyanawa Legit Hausa cewa a zaɓen 2027, talakan Najeriya ne zai tantance wanda zai mulke shi ba.

"Ƴan Najeriya ai sun yi hankali, yanzu sun bambance tsakanin aya da tsakuwa. Na san cewa dole a 2027 su tsaya su zaɓi wanda zai ceto su daga halin da suka samu kansu a ciki."
"Ƴan siyasar nan kusan duk abu ɗaya ne, amma munaa addu'ar Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi."

- Kabir Lawal

Tinubu ya magantu kan shirin haɗaka a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban ƙasan Najeriya ta yi taɓo batun haɗaƙa da ƴan adawa suke yi domin tunkarar zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Yunkurin tsige gwamna ya jefa Shugaba Tinubu a matsala, an yi masa barazana

Hadimin Shugaba Bola Tinubu kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya bayyana cewa shugaban ƙasan ba batun zaɓen 2027 ya sanya a gaba ba.

Sunday Dare ya bayyana cewa shugaban ƙasan ya damu ne wajen ganin ya inganta rayuwar ƴan Najeriya ta yadda za su yi alfahari da shi.

Ya nuna cewa Tinubu yana son ya ga ya ɗora ƙasar nan a kan turba ta yadda za ta tsata da ƙafafunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel