"Dama Karfa Karfa Aka Mana a 2023," Sanata Tambuwal Ya Hango Faɗuwar Tinubu a 2027
- Aminu Waziri Tambuwal ya ce idan Allah ya yarda jam'iyyar PDP za ta karɓe mulkin Najeriya daga hannun APC a zaɓen 2027
- Tsohon gwamnan Sakkwato ya bayyana hakan ne a wurin taron fara rabon kayan abinci ga al'ummar mazaɓarsa albarkacin Ramadan
- Sanatan ya ce jam'iyyar PDP ta shirya dawo da abin da aka ƙwace mata a zaɓen 2023, yana mai rokon ƴaƴan jam'iyyar su haɗa kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Tsohon gwamnan Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Kudancin jihar, Aminu Tambuwal, ya sake jaddada cewa jam’iyyar PDP ta shirya kwace mulki a 2027.
Sanata Aminu Tambuwal ya bayyana cewa yana da ƙwarin guiwa da yaƙinin cewa PDP za ta samu galaba kan APC a babban zaɓen 2025.

Asali: Facebook
Tambuwal ya bayyana hakan ne yayin da yake ƙaddamar da raba kayan tallafin azumin Ramadan ga al’ummar jihar Sokoto, kamar yadda Leadership ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aminu Tambuwal ya raba tallafin Ramadan
Tsohon gwamnan ya ce ‘yan majalisar PDP daga matakin jiha da na tarayya sun shirya rarraba dubban buhunan shinkafa da sauran kayan abinci ga matasa da mata domin sauƙaƙa musu wahalhalu da azumi.
Aminu Tambuwal ya ce:
"Dole ne mu gode wa Allah da ya ba mu tsawon rai nuka shaida wannan wata mai alfarma na Ramadan, duk da yawan rayukan da suka salwanta.
"Muna roƙon Allah ya ƙara mana lafiya da tsawon rai don mu samu damar ganin watan Ramadan mai zuwa bayan wannan."
Sanatan ya kuma gode wa shugaban jam’iyyar PDP a jihar Sakkwato da sauran shugabanni bisa ƙoƙarin da suke yi wajen ƙarfafa jam’iyyar da haɗa kan ‘ya'yanta.
"PDP za ta dawo kan mulki" – Tambuwal
Sanata Tambuwal ya jaddada cewa PDP jam’iyya ce mai ƙarfi da haɗin kai, kuma tana riga da ta gama shirin karɓar mulki daga hannun APC a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan
Bayan El Rufai ya yi fatan ya dawo SDP, alamu sun nuna Peter Obi na shirin canza jam'iyya
"An mana ƙarfa-ƙarfa a zaben da ya gabata, amma yanzu mu na sake tsara yadda za mu dawo kan mulki. Insha Allah, za mu kwato abin da aka kwace mana a 2027," in ji Tambuwal.

Asali: Facebook
Shugaban PDP ya yabawa ƴan jam'iyya
A nasa jawabin, shugaban PDP na jihar Sokoto, Bello Goronyo, ya gode wa ‘ya’yan jam’iyyar bisa goyon bayan da suke bayarwa, yana mai cewa PDP ce kawai ke kula da jin daɗin talakawa.
Bello Goronyo ya soki halin ƙuncin rayuwa da ake ciki a yanzu, yana mai cewa hakan bai taɓa faruwa a lokacin mulkin PDP ba.
Ya kuma ƙira ga mutanen Sokoto da al’ummar Najeriya su guji APC a 2027 domin kwato ‘yancinsu daga mulkin ƴan kama karya.
A cewar wani ɗan PDP a jihar Katsina, Abdullahi Kabir, Tambuwal na ɗaya daga cikin waɗanda suka hargitsa jam'iyyar.
Da yake zantawa da wakilin Legit Hausa, matashin ɗan siyasar ya ce duk da haka har yanzu PDP na da isasshen lokacin da za ta gyara kura-kuranta.

Kara karanta wannan
"Ba mu yarda ba," El Rufai ya ƙara shiga matsala bayan komawa SDP, matasa sun masa rubdugu
"Warware rikicin PDP abu ne mai wahala amma da manyan za su jingine duk wani saɓani, za a samu maslaha, babbar matsalar ita ce kowa na son mulki, kuma yana gani shi ke da gaskiya," in ji shi.
Tambuwal ya soki masu shiga APC
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Aminu Tambuwal ya caccaki ƴan siyasar da ba su da alkibla, waɗanda ke yawan sauya sheka daga wannan jam'iyya zuwa wata.
Tsohon gwamnan ya soki masu komawa jam’iyyar APC mai mulki, yana mai cewa ba domin al'umma suke yin hakan ba, sai don cimma burinsu ne na ƙashin kai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng