Tallafin Ramadan Ya Haɗa Rigima, Gwamna da Jam'iyya Sun Fara Nuna wa Juna Yatsa
- Rikici ya ɓarke tsakanin Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe da jam'iyyar PDP, sun fara musayar yawu kan tallafin Ramadan
- Jam'iyyar PDP ta yi ikirarin tallafin da gwamnatin Gombe ke rabawa mutane ba ita ta sayo ba, gwamnatin tarayya ce ta aiko da shi
- Sai dai hadimin Gwamna ya musanta ikirarin PDP amma duk da haka ya yaba mata bisa yadda ta amince da ƙoƙarin gwamnatin tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe - An fara musayar yawu tsakanin gwamnatin jihar Gombe karkashin jagorancin Gwamna Muhammaed Inuwa Yahaya da jam'iyyar adawa ta PDP.
Jam’iyyar PDP ta zargi gwamnatin Inuwa da karɓe tallafin rage raɗaɗin rayuwa na Ramadan da gwamnatin tarayya ta bayar, ta ce nata ne da ta sayo don rabawa talakawa.

Source: Twitter
Gwamna Inuwa ya fara rabon tallafin azumi
Daily Trust ta tattaro cewa a ƙarshen makon jiya, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya ƙaddamar da rabon kayan abinci ga al’ummar Musulmi masu azumi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya kaddamar da fara rabon tallafin azumin ne domin ragewa jama'a radaɗi da ƙuncin rayuwa a lokacin da suke ibada a watan Ramadan.
Ramadan: PDP ta caccaki Gwamna Inuwa
Sai dai a wata sanarwa da kakakin jam'iyyar PDP na Gombe, Abdulkadir Ahmad Dukku, ya fitar, ya yi zargin cewa kayan abincin da aka raba na gwamnatin tarayya ne.
“Wannan yunkuri na gwamnatin Gombe ba komai ba ne face yaudarar jama’a da ƙoƙarin karɓe yabo kan wani tallafi da ba nata ba.
"Mun damu matuka kan yadda gwamnatin jihar nan ta gaza fitowa ta godewa gwamnatin tarayya da kuma kokarin shugaba Bola Ahmed Tinubu na agaza wa mabukata."
"Muna kira ga gwamna da ya faɗa wa jama'a gaskiya cewa tallafin nan daga gwamnatin tarayya da Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC) ya fito, kuma a ba kowa da kowa maimakon sanya siyasa a ciki."
- Abdulkadir Ahmad Dukku.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ƙara shiga tsaka mai wuya, Majalisar Dokoki ta dawo da shirin tsige shi
Gwamnatin Gombe ta maida martani
Amma a martaninsa, Daraktan Hulɗa da Jama’a na gwamnatin jihar Gombe, Ismaila Uba-Misilli, ya yi watsi da zargin PDP, yana mai cewa ba komai ba ne face siyasa.
Ya bayyana cewa, babu wani sabon tallafin Ramadan da jihar Gombe ta samu daga gwamnatin tarayya, jaridar Punch ta ruwaito.

Source: UGC
Duk da haka, Isma'ila Misilli ya yaba wa PDP bisa amincewar da ta yi da kokarin gwamnatin tarayya, yana mai cewa hakan na ƙara tabbatar da nagartar manufofin APC.
“A gaskiya, Gwamna Inuwa Yahaya ya bada umarni a fitar da duk kayan abincin da ake da su a ajiya domin rabawa jama’a, wanda ya haɗa da na gwamnatin tarayya, na hukumar NEDC, da kuma waɗanda gwamnatin jihar ta saya,” in ji shi.
Sanatan Gombe ya raba kayan sana'o'i
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Muhammad Ɗanjuma Goje ya rabawa jama'ar mazaɓarsa tallafi domin bunƙasa sana'o'insu na hannu.

Kara karanta wannan
Zargin Shugaban Majalisa da neman lalata da matar aure ya riƙide, an samu wasiƙa daga Kogi
Sanata Goje ya raba kekunan dinki guda 700 ga masu kananan sana’o’i, domin ba su damar dogaro da kansu da kuma habaka sana’ar dinki a yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
