2027: Ministan Tinubu Ya Nuna Sha'awar Tsayawa Takarar Gwamna

2027: Ministan Tinubu Ya Nuna Sha'awar Tsayawa Takarar Gwamna

  • Yayin da ake tunkarar zaben 2027, 'yan siyasa a Bauchi sun fara neman hadin kan al'umma domin samun nasara a babban zaben mai zuwa
  • A APC, ana hasashen Yusuf Tuggar da Ali Pate na iya tsayawa takarar gwamna, yayin da a PDP ake tunanin Kyari Wunti zai nemi kujerar
  • Ministan lafiya, Ali Pate, ya bayyana sha'awarsa ta tsayawa takarar gwamna a 2027, yana mai cewa ya shirya yi wa Bauchi hidima
  • A zantawarmu da wasu matasan Bauchi, sun bayyana ra'ayoyinsu kan ministan ilimi, Farfesa Ali Pate, game da burinsa na tsayawa takara a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Yayin da ake tunkarar zaben 2027, 'yan siyasa a jihar Bauchi sun fara daura damarar kyautata alaka da mutane don samun nasara a babban zaben mai zuwa.

Kara karanta wannan

Bauchi: Sanata ya gagara boye kwadayin takarar gwamna, ya roki shugabannin PDP

Siyasar Bauchi na da rikitarwa kuma ba ta da tabbas, musamman idan ana batun zaɓen manyan mukamai, ciki har da na gwamnan jihar.

Ministan lafiya, Ali Pate ya yi magana kan sha'awarsa ta yin takarar gwamnan Bauchi
Ali Pate, ya nuna sha'awar tsayawa takarar gwamnan Bauchi a zaben 2027. Hoto: @muhammadpate
Asali: Twitter

Su wa za su iya tsayawa takarar gwamnan?

A halin yanzu, ministocin tarayya: Yusuf Tuggar da Ali Pate suna cikin wadanda ake ganin za su iya tsayawa takarar gwamna a jam’iyyar APC a 2027, inji rahoton Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan, akwai yiwuwar tsohon hafsan sojin sama, Abubakar El-Sadique, da Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu, Shehu Buba, su shiga takarar.

A jam’iyyar PDP mai mulki a jihar kuwa, ana rade-radin cewa babban darakta a kamfanin NNPCL, Kyari Wunti, yana sha’awar takarar gwamna.

Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Bala Mohammed na iya mara wa Wunti baya a matsayin magajinsa a 2027.

Duk da cewa Wunti bai bayyana aniyarsa a hukumance ba, amma majiyoyi sun ce ya riga ya yanki katin shaidar zama dan jam’iyyar PDP a sirrance.

Kara karanta wannan

Tirƙashi: PDP ta kori tsohon shugaban majalisar dattawa, an fadi zunubinsa

Bauchi: Ali Pate ya bayyana sha'awar yin takara

Ministan lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya bayyana sha'awarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Bauchi a zaben 2027.

A wata hira da ya yi da TVC News, Pate ya ce zai iya fitowa takara idan masu ruwa da tsaki a siyasar Bauchi suka goyi bayansa.

Shigarsa takarar na iya haifar da sababbin sauye-sauye a APC, jam’iyyar da ke kokarin karbe mulki daga PDP a Bauchi.

Duk da wannan kuduri, Ali Pate ya ce a halin yanzu ya mayar da hankali kan aikin da Shugaba Bola Tinubu ya ba shi a ma’aikatar lafiya.

Amma, ya bayyana cewa idan har APC na son cin zabe a Bauchi, dole ne jam’iyyar ta kasance tsintsiya madaurinki daya kafin 2027.

"A shirye nake na yiwa Bauchi hidima" – Minista

Ali Pate ya nuna sha'awar tsayawa takarar gwamna a Bauchi
Ministan lafiya, Ali Pate ya yi magana kan tsayawa takarar gwamnan Bauchi. Hoto: @muhammadpate
Asali: Facebook

Ali Pate ya ce yana da kusanci mai karfi da al’ummar Bauchi, kuma yana fahimtar matsalolin da ke addabar jihar da yadda za a magance su.

Kara karanta wannan

NNPP: Jam'iyyar Kwankwaso ta dakatar da dan takarar gwamna da mataimakinsa

“Idan ba a hada kai a jam’iyyar APC ba, ba za a iya kwace mulki daga PDP a 2027 ba," inji Farfesa Ali Pate.

Ya kara da cewa babban burinsa shi ne hada kan APC, goyon bayan Tinubu, da kuma tabbatar da ci gaban jihar Bauchi gaba daya.

Lokacin da aka tambaye shi idan zai tsaya takara a 2027, Ali Pate ya ce:

"Eh, ina da buri, kuma ina da kwarewa, cikin watanni masu zuwa, za mu ga yadda abubuwa za su kasance.
A shirye nake in yi wa Bauchi hidima, ina da burin bunkasa jihar da kuma ci gaban ƙasarmu."

Matasan Bauchi sun bayyana ra'ayinsu kan Pate

A zantawarmu da wasu matasan Bauchi, sun bayyana ra'ayoyinsu kan ministan ilimi, Farfesa Ali Pate, game da burinsa na tsayawa takara a 2027.

Mufeedat Abdulsamad, mazauniyar Wuntin Dada da ke Bauchi, ta ce yanzu jihar tana bukatar wanda zai kawo mata ci gaban da ake gani a jihohi kamarsu Kano da Kaduna.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya

Ta ce Gwamna Bala Mohammed, mai ci a yanzu, ya yi kokarin wajen shimfida tituna da kawo shirye-shirye na ci gaban jama'a don haka dole wanda zai gaje shi ya nunka a kan hakan.

"Mu yanzu mun daina wata siyasa ta jam'iyya ko ra'ayi. Yanzu muna yin siyasa ce ta ci gaban mutanenmu, domin sai al'umma ta ginu ne ake samun ci gaban rayuwa.
"Rashin ayyukan yi ne ke jefa matasanmu a shaye-shaye, sata da sauran laifuffuka, amma idan akwai aikin yi, ba za su yi ba. Allah ya jikan Isa Yuguda ba don ya mutu ba, a lokacinsa, an ba matasa aiki, kuma jihar ta zauna lafiya."

Shi kuwa Hassan Turum ce wa ya yi Ali Pate yana da duk wata cancanta ta zama gwamna, don haka ya fito takara a zaben mai zuwa.

"In sha Allahu za mu ba shi goyon baya, saboda shi na mutane ne. Kawai dai kwana biyu ya yi sanyi, ya koma Abuja, amma na san kafin lokacin ya zo ya sake shiga jama'a."

Kara karanta wannan

Littafin IBB ya tono tsuliyar dodo, an fadi kabilar da ake so ta yi mulki a 2027

Kalli hirar da aka yi da Ali Pate a nan kasa:

Badakalar $300m: Majalisa ta gayyaci Ali Pate

A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar wakilai ta nemi ministan lafiya, Farfesa Mohammed Ali Pate, ya gurfana gabanta don bayani kan wasu kudi da aka kashe.

Majalisar na zargin ma’aikatar lafiya da fitar da dala miliyan 300 a 2021 domin yaki da zazzabin cizon sauro, amma ta gano wasu matsaloli a yadda aka sarrafa kudin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.