Zargin Lalata: Sanata Natasha Ta Fitar da Saƙo Mai Zafi bayan Dakatar da Ita a Majalisa
- Sanata Cyril Fasuyi, mai wakiltar Ekiti ta Arewa ya yi ikirarin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta taɓa zargin Kayode Fayemi da cin zarafinta
- Akpoti-Uduaghan ta mayar da martani, tana zargin Fasuyi da yi mata karya a zauren majalisa yayin da yake ambato ayoyin Littafi Mai Tsarki
- Ta ce babu lokacin da ta taba zargin Fayemi da sayar da Kamfanin Karafa na Ajaokuta, ta yi Allah wadai da kokarin bata mata suna a bainar jama’a
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kogi - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta maidawa abokin aikinta, Sanata Cyrill Fasuryi martani.
Sanata Natasha ta zargi Sanata Cyril Fasuyi daga jihar Ekiti da jingina mata ƙarya a lokacin zaman majalisar dattawa na ranar Laraba, 5 ga Maris, 2025.

Source: Facebook
Natasha wacce ke fuskantar hukunci kan zargin karya doka ta bayyana haka ne a wani gajeren saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Natasha ta taɓa zargin Fayemi
Legit Hausa ta ruwaito cewa Sanata Fasuyi ya yi ikirarin cewa Natasha Akpoti-Uduaghan ta taba yin wasu kalamai marasa, tana zargin tsohon gwamnan Ekiti. Kayode Fayemi da cin zarafinta.
A cewarsa, Natasha ta zargi Fayemi ne a lokacin da yake rike da mukamin ministan ma’adanai da ci gaban karafa a gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Tsohon ministan ya musanta zargin
Sai dai, a wata sanarwa da mai magana Fayemi, Ahmad Sajoh, ya fitar, tsohon gwamnan ya musanta zargin cewa Sanata Natasha ta ci zarafinsa.
Tsohon ministan ya ƙara da cewa duk wata hulda da ta shiga tsakaninsa da Natasha Akpoti-Uduaghan ta kasance ne a kan aiki kawai, ba tare da wata matsala ta kashin kai ba.

Source: Twitter
Sanata Natasha ta yabawa Fayemi
Da take mayar da martani kan bayanin Fayemi, Sanata Natasha ta wallafa wata gajeriyar sanarwa a shafinta na Facebook, inda ta yaba wa tsohon ministan bisa fitowa fili ya fadi gaskiya.

Kara karanta wannan
Zargin lalata: Sanata Natasha ta sake yamutsa Hazo, ta yi magana kan dakatar da ita
Ta ce:
"Nagode, Mai Girma @kfayemi, saboda ka fito ka fadi gaskiya. Duk wani abu da na yi a wannan lokacin a matsayin minista ya kasance ne domin kokarin farfado da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta.
"Abin kunya ne ga Sanata Cyril Fasuyi ya fito yana faɗin karya a kaina kuma a zauren majalisa a daidai lokacin da yake ambato Littafi Mai Tsarki. Lallai, Allah mai hakuri ne."
Wannan sabuwar rigima na kara nuna yadda siyasar majalisar dattawa ke kara daukar sabon salo, musamman kan batutuwa da suka shafi shugabanci da rawar da sanatoci ke takawa a wakilcin al’ummarsu.
Majalisa ta dakatar da Sanata Natasha
A wani rahoton, kun ji cewa bayan kai ruwa da rana, majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya.
Majalisar ta kuma dakatar da albashi da alawus na Sanata Natasha, rufe ofishinta, janye jami’an tsaro, da hana ta zuwa ko kusa da majalisar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
