Jigon PDP Ya Gano Hanyar Kayar da Shugaba Tinubu a Zaben 2027

Jigon PDP Ya Gano Hanyar Kayar da Shugaba Tinubu a Zaben 2027

  • Babban ƙusa a jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, Bode George, ya taɓo batun zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027
  • Bode George ya bayyana cewa jam'iyyar PDP za ta iya kayar da Shugaban kasa Bola Tinubu da APC a zaɓe mai zuwa
  • Jigon na PDP ya nuna cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ba zai iya kayar da Tinubu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Bode George, ya yi magana kan zaɓen 2027.

Bode George ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ba zai iya kayar da Bola Tinubu ba a 2027, sai da goyon bayan PDP.

Bode Goerge ya ce za a iya kayar da Tinubu a 2027
Bode George ya ce PDP za ta iya kayar da Tinubu a 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Chief Olabode George
Source: Facebook

Jaridar Tribune ta rahoto cewa jigon na PDP ya bayyana cewa Peter Obi ba zai kai labari ba idan ya yi takara da Tinubu a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

"Ɗan takara 1 tal gare mu," Sanatan APC ya hango wanda zai ci gaba da mulkin Najeriya a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon PDP ya ba Peter Obi shawara

A cewarsa, jam'iyyar LP ba ta da cikakken tsarin siyasa da zai iya gogayya da wanda APC mai mulki ta ke da shi.

Bode George ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ce kaɗai ke da ƙarfi da goyon bayan da za ta iya kayar da APC a zaɓen 2027.

Sai dai ya jaddada cewa hakan ba zai yiwu ba sai idan shugabannin PDP sun tabbatar da adalci, gaskiya, da daidaito a cikin jam’iyyar.

Wace hanya za a bi don kayar da Tinubu?

“Ba ni da wata matsala da Obi. Shi ɗan Kudu ne, amma gaskiyar magana ita ce, jam'iyyar LP ba ta da tsarin siyasa da zai iya gogayya da Bola Tinubu da APC a zaɓen 2027."
“PDP ce kaɗai jam’iyyar da ke da ƙarfi, da goyon baya da za su iya kayar da APC. Ban kuma yarda cewa za a sake zaɓen Bola Tinubu cikin sauƙi kamar yadda wasu ke zato ba."

Kara karanta wannan

PDP ta ji jiki a Zamfara, jiga-jiganta da tsohon ɗan takarar gwamna sun shiga APC

"Ana iya kayar da shi a zaɓen 2027, amma sai idan shugabannin PDP sun yi abin da ya dace ta hanyar tabbatar da adalci, gaskiya, da daidaito."

- Bode George

Bode George ya ba Wike shawara

George ya kuma yi kira ga ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, da ya sake duba matsayarsa kan PDP

Ya yi kira a gare shi da ya ƙara yin ƙoƙari wajen ba da gudunmawarsa domin sake gina Najeriya.

Bugu da kari, Bode George ya soki shishigin da gwamnatin tarayya ke yi a harkokin siyasar jihohi.

Ya yi gargaɗin cewa hakan na iya haifar da matsalar tsaro idan ba a magance ta ba.

Bode George ya ba PDP shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban jigo a jam'iyyar PDP, Bode George, ya ba masu ruwa da tsaki na jam'iyyar shawara kan zaɓen shugaban ƙasa.

Tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasan ya buƙaci masu ruwa da tsakin jam'iyyar da ka da su ba Atiku Abubakar tikitin takara a zaɓen 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng