Me Ke Faruwa da PDP? An Rufe Siyar da Fom na Takarar Gwamna, Babu Wanda Ya Siya

Me Ke Faruwa da PDP? An Rufe Siyar da Fom na Takarar Gwamna, Babu Wanda Ya Siya

  • Jam'iyyar PDP ta rufe siyar da fom ɗin takarar gwamna na jihar Anambra, amma babu wanda ya siya ko nuna sha'awa
  • Jam’iyyar ta tsawaita lokacin sayar da fom ɗin har zuwa 10 ga Maris inda wasu ke danganta hakan da rigimar cikin gida
  • Rikicin jagoranci ya haddasa rashin tabbaci, musamman kan mukamin sakataren jam'iyya na ƙasa da ake shari'a a kotu
  • Yanzu haka mulkin jihar Anambra ta hannun jam'iyyar APGA a karkashin Charles Soludo wanda ya gaji Willie Obiano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Awka, Anambra - Jam’iyyar PDP ta rufe siyar da fom ɗin takarar gwamna na jihar Anambra da za a yi a karshen 2025 amma babu wanda ya siya.

An ce wasu yan takara ba sa son saka kuɗi saboda matsalolin cikin gida da suka addabi jam'iyyar don gudun asara.

Kara karanta wannan

Mataimakiyar gwamna ta ji wuta, ta yi murabus daga muƙaminta? Bayanai sun fito

Matsala ta faru a PDP kan siyan fom ɗin takarar gwamna
Har an rufe siyar da fom ɗin takarar gwamna babu wanda ya siya a Anambra. Hoto: People's Democratic Party, PDP.
Asali: Facebook

Yadda rikicin PDP ya tsananta a dukkan matakai

Punch ta ce jam’iyyar ta fara siyar da fom ɗin daga 24 ga Fabrairu zuwa 5 ga Maris, 2025 inda aka sanya ranar 7 ga Maris don miƙa fom.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan shirya taron masu ruwa da tsaki da kwamitin NWC a ranar 10 ga Maris a hedikwatar PDP a Abuja.

Rikicin PDP ya tsananta sakamakon gardama kan mukamin matsayin sakatare na ƙasa, inda Sam Anyanwu da Ude-Okoye ke kokawa.

An shirya zaman kotun koli a ranar 10 ga Maris don yanke hukunci kan batun, wanda ke kawo rabuwar kai a jam’iyyar.

'Yan takara sun kauracewa siyan fom na PDP

A game da zaben Anambra, za a yi zaɓen fitar da gwani na PDP a ranar 5 ga Afrilu, yayin da za a saurari ƙorafe-ƙorafe ranar 8 ga Afrilu.

Wata majiya a jam'iyyar PDP ta ce ‘yan takara na tsoron kashe kuɗi saboda rikicin jagoranci.

Kara karanta wannan

Duk da korafin CAN a jihohi, an fara hutun azumin Ramadan a jami'ar tarayya

Majiyar ta ce:

“Jam’iyyar ta yi rauni, don haka ba su so su saka kuɗi domin gudun tafka asara."
PDP na ci gaba da neman mafita kan rikicin cikin gida da ya addabe ta
Wasu yan PDP sun nuna damuwa kan rigimar da ke faruwa jam'iyyar. Hoto: People's Democratic Party, PDP.
Asali: Facebook

Dalilin PDP na tsawaita siyar da fom din takara

Majiyar ta ƙara da cewa matsalar ta shafi jihohi, yankuna da ma ƙasa baki ɗaya, kuma hakan ya sa wasu ba su da tabbacin yin adalci.

Don shawo kan matsalar, PDP ta tsawaita lokacin sayar da fom ɗin har zuwa 10 ga Maris, domin ƙarfafa ‘yan takara su shiga takara.

“Za a fitar da sabon jadawalin zabe kafin ƙarshen mako, Mun tsawaita wa’adin sayar da fom zuwa 10 ga Maris."

- In ji wata majiya

Legit Hausa ta yi magana da dan PDP

Kwamred Aliyu Abdulkadir ya koka kan halin da PDP ke ciki a yanzu musamman rikicin cikin gida.

Aliyu ya ce wannan babban matsala ne ga jam'iyyar a ce fom na takarar gwamna guda babu wanda ya siya har aka rufe.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina ta kare matakin kulle makarantu a Ramadan, ta tura sako ga CAN

Aliyu ya ce:

"Abin takaici ne abin da ke faruwa a PDP, ya kamata shugabanni su nemo hanyar dakile matsalolin saboda gudun akasi a zaben 2027."

Bode George ya gargadi ba Atiku takara

Kun ji cewa kusa a jam'iyyar PDP, Bode George ya bukaci PDP da kada ta sake tsayar da Atiku Abubakar a matsayin dan takararta a zaɓen 2027.

George na ganin jam'iyyar PDP za ta iya samun matsala a zaben kamar yadda aka yi a baya idan ba a sauya dan takara zuwa wani daga Kudancin kasar ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng