"An Yi Rashin Nasara Sau 3," Shugaba a PDP Ya Ja Kunne kan Tsaida Atiku Takara a 2027

"An Yi Rashin Nasara Sau 3," Shugaba a PDP Ya Ja Kunne kan Tsaida Atiku Takara a 2027

  • Jagora a PDP, Cif Bode George ya bukaci PDP da kada ta sake tsayar da Atiku Abubakar a matsayin dan takararta a 2027
  • Yana ganin cewa PDP za ta yi rashin nasara a zaben matukar ba a sauya dan takara zuwa wani daga Kudancin kasar nan ba
  • Daga cikin dalilan da ya bayar da kar a ba Atiku takara, akwai zargin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya raina Kudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban PDP na kasa, Bode George, ya bukaci masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da kada su yi tunanin barin Atiku Abubakar ya zama dan takarar jam’iyyar a zaben 2027.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya rike tutar jam’iyyar na neman kujerar shugaban kasa a zaben 2019 da 2023.

Kara karanta wannan

Tirƙashi: PDP ta kori tsohon shugaban majalisar dattawa, an fadi zunubinsa

Atiku
An shawarci PDP kan tsayar da Atiku takara Hoto: Atiku Abubakar/Bode George Campaign organization
Asali: Facebook

A hira da ta kebanta ga The Guardian, George ya ce idan aka sake tsayar da Atiku a matsayin dan takarar PDP, za su fuskanci matsala a babban zaben shugaban kasa na gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya saba samun tuta ba tare da ya yi nasara ba. Ya nemi takara tun daga 2007, kuma PDP ta tsaida shi a 2019 da 2023.

'Dan PDP ya zargi Atiku da raina ‘yan Kudu

Bode George ya zargi Atiku da rashin mutunta yankin Kudu, yana mai cewa ya nuna hakan a yadda ya tafiyar da shirin PDP na zaben fitar da gwani na 2023.

Ya ce wannan raini da aka gani shi ne abin da ya fusata gwamnoni shida a karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike har suka jawo mata asara.

Ya ce:

"Atiku ba shi da ra’ayin cigaban Kudu a zuciyarsa, kuma ba zai iya zama shugaban kowa ba, idan har a karkashin jagorancinsa aka hana yankin Kudu maso Yamma komai."

Kara karanta wannan

Ana binciken Natasha maimakon Akpabio duk da zargin shugaban majalisa da lalata

Bode George: “Dan Kudu PDP take bukata”

Tsohon Gwamnan Soja na Jihar Ondo ya na ganin zai zama cin fuska ne da zalunci ga yankin Kudu idan har wani dan Arewa ya sake lashe tikitin takarar shugaban kasa na PDP a 2027.

Atiku
Ana zargin Atiku ba ya kishin Kudancin Najeriya Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ya ce:

"Ina tabbatar muku cewa babu wani dan Kudu mai hankali da zai yi wa dan Arewa kamfen domin ya zama Shugaban Kasa a 2027.
Ni kuma ba zan taba yin hakan ba har sai bayan 2031, lokacin da yankin Kudu ya kammala wa’adin shekara takwas.”

Ana son Peter Obi ya koma PDP

Dangane da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, Bode George ya ce ba zai iya nasarar fafata wa da APC a zaben 2027 ba.

Ya ce:

"Ba ni da wata matsala da Obi; dan Kudu ne, amma gaskiya ita ce, tsohon gwamnan Anambra ba zai iya cimma burinsa na zama Shugaban Kasa ba sai a kan dandalin PDP, ba jam’iyyar LP ba da ke da matsala ta rashin karfi a jihohi 36."

Kara karanta wannan

Me yake shiryawa?: Na hannun damar Peter Obi da ya fice daga LP ya gana da Atiku

"Babu yadda jam’iyyar LP a halin yanzu za ta iya tunkarar karfin Bola Tinubu da jam’iyyar APC a 2027.”

An shawarci PDP ta tsayar da Atiku takara

A baya, kun samu labarin cewa shugaban gidauniyar ECK, Dr. Emeka Kalu, ya ce tsohon dan takarar PDP, Atiku Abubakar ne ya kamata ya zama shugaban kasa don ya cancanta.

A cewarsa, Atiku ne kadai ke da ƙwarewa da hangen nesa na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan idan har aka ba shi dama a 2027, saboda gogewarsa wajen sanin matsalolin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng