Mataimakiyar Gwamna Ta Ji Wuta, Ta Yi Murabus daga Muƙaminta? Bayanai Sun Fito

Mataimakiyar Gwamna Ta Ji Wuta, Ta Yi Murabus daga Muƙaminta? Bayanai Sun Fito

  • Farfesa Ngozi Odu ta musanta raɗe-raɗin da mutane ke yaɗawa cewa ta yi murabus daga kujerar mataimakiyar gwamnan Ribas
  • Mataimakiyar gwamnan ta yi fatali da jita-jitar gaba ɗaya, tana mai cewa ba ta tushe balle kuma makama
  • Wannan dai na zuwa ne yayin da rikicin siyasar Ribas ya ƙara zafi musamman tsakanin Majalisa da ɓangaren gwamnatin Fubara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Mataimakiyar gwamnan jihar Rivers, Farfesa Ngozi Odu, ta musanta rahotannin da ke yawo cewa ta yi murabus daga mukaminta.

Wannan na zuwa ne bayan wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna cewa ta yi murabus sakamakon matsin lamba da take fuskanta daga wasu bangarorin a jihar.

Farfesa Ngozi Odu.
Mataimakiyar Gwamnan jihar Rivers, Farfesa Ngozi Odu, ta musanta rade-raɗin cewa ta ajiye mukaminta Hoto: Dr. Mrs Ipalibo Harry Banigo
Asali: Facebook

Rahoton Daily Trust ya ce a wata sanarwa da sakataren watsa labaranta, Owupele Benebo, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa wannan labari ba shi da tushe kuma ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Majalisar shari'ar Musulunci ta goyi bayan rufe makarantu, ta kirayi jihohi 3 su bi sahu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakiyar gwamnan Ribas ta yi murabus?

Ya ce mataimakiyar gwamnan na nan daram a kujerarta, tana ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa doka da kuma amana da aka ba ta.

"Ofishin mataimakiyar gwamnan jihar Ribas ya yi watsi da wannan jita-jita mara tushe da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Mai Girma Farfesa Ngozi Nma Odu, DSSRS, ta yi murabus.
"Saɓanin wannan zargi mara tushe, tana nan tana gudanar da ayyukanta a matsayin mataimakiyar gwamna, mukamin da aka zabe ta tare da Mai Girma Gwamna Sir Siminalayi Fubara, GSSRS."

Sanarwar ta ci gaba da cewa Farfesa Odu tana da cikakken goyon baya daga Gwamna Fubara kuma tana aiki tare da shi don cika alƙawurraɓ da suka yi wa jama'a.

Farfesa Odu na da goyon bayan gwamna

Ta kara da cewa Farfesa Odu tana da gogewa mai zurfi a harkokin gudanar da gwamnati da ilimi, kuma tana da kwarewar da za ta ci gaba da ba da gudunmawa ga ci gaban jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Zargin lalata: Sanata Natasha na tsaka mai wuya, Hadimin Osinbajo ya tona shirin majalisa

"A matsayinta na gogaggiyar ma’aikaciyar gwamnati kuma malamar jami’a, Farfesa Odu tana tare da gwamna wajen tabbatar da cika alkawarin da aka yi wa jama’a.
"Jagorancinta da kwarewarta sun kasance abin alfahari ga wannan gwamnati, kuma tana nan daram tana gudanar da ayyukanta."

An buƙaci jama'a su yi fatali da jita-jitar

Sanarwar ta bukaci al’ummar jihar Ribas da su yi watsi da irin wadannan rahotanni marasa tushe, tana mai bayyana su a matsayin ƙoƙarin tayar da zaune tsaye.

A makonni da suka gabata, rikici ya ƙara ƙamari a siyasar jihar Ribas musamnan tsakanin ɓangaren gwamnati da ƴan Majalisar Dokoki.

Gwamna Fubara.
Mataimakiyar gwamnan Riba na nan daram a kujerarta Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Wannan rikici ya jawo fargaba da rade-radin da ke yaduwa kan halin da wasu manyan jami’an gwamnati ke ciki, rahoton Vanguard.

Duk da haka, sanarwar daga ofishin mataimakiyar gwamnan ta nuna cewa babu wani abu makamancin hakan, kuma Farfesa Odu na nan daram a kan kujerarta tana ci gaba da aiki.

Kara karanta wannan

Gwamna ya daina ɓoye ɓoye, ya jero mutanen da ke jefa matasa harkar ƴan bindiga

Gwamnatin Ribas ta yi watsi da buƙatar Majalisa

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Ribas ta ce har yanzu ba ta karɓi takarda a hukumance daga majalisar dokoki dangane da kasafin kudin 2025 ba.

A wata sanarwa da sakataren gwamnatin Ribas ya fitar, ya ce mai girma gwamna ba zai amsa gayyatar da Majaliss ta masa kan kasafin ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng