Bayan Ƙarewar Wa'adin Sa'o'i 48, Gwamna na Neman Tattago Rigima da Majalisar Dokoki
- Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ba zai mutunta gayyatar da Majalisar Dokoki ta yi masa domin ya sake gabatar da kasafin kuɗin 2025 ba
- Sakataren gwamnatin jihar, Dr. Tammy Danagogo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ɗauke da kwanan watan 5 ga watan Maris, 2025
- Ya ce har zuwa jiya Talata, babu wata takarda daga Majalisa a hukumance wanda ke nuna bukatar sake gabatar da kasafin, ya ce a soshiyal midiya suka ji
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Gwamnatin jihar Ribas karkashin jagorancin Gwamna Siminalayi Fubara ta ce ba za ta mutunta gayyatar Majalisar dokoki ba.
Gwamnatin ta ce mai girma gwamna ba zai bi umarnin Majalisar Dokokin jihar ba dangane da sake gabatar da kasafin kudin 2025.

Source: Facebook
A rahoton da The Nation ta tattaro, Gwamnatin Ribas ta ɗauki wannan matsaya ne saboda ba ta karɓi wata takarda daga majalisar da ke sanar da bukatar hakan ba.

Kara karanta wannan
Rikici ya ƙara Kamari, jam'iyyar APC ta buƙaci gwamna ya yi murabus cikin sa'o'i 48
Majalisa ta ba gwamna wa'adin sa'o'i 48
Idan ba ku manta ba Majalisar karkashin jagorancin kakakinta, Hon. Martins Amaewhule, ta bai wa Gwamna Siminalayi Fubara wa’adin sa’o’i 48 da ya sake gabatar da kasafin kudin 2025.
Majalisar ta ba gwamnan wannan wa'adi kwanaki ƙalilan bayan kotun kolin Najeriya ta kawo ƙarshen rikicin da ya raba Majalisar dokokin gida biyu.
A hukuncin kotun ƙolin, an tabbatar da Martin Amaewhule da ƴan majalisa da ke tsaginsa a matsayin halastattun mambobin Majalisar dokokin jihar Ribas.
A zaman farko da suka yi bayan hukuncin kotu, ƴan Majalisa sun ba Gwamna Simi Fubara ranakun aiki biyu ya sake gabatar da kasafin kudin 2025.
Gwamnatin Ribas ta maidawa majalisa martani
Sai dai a wata takardar da gwamnatin Ribas ta aike wa Majalisa mai ɗauke da kwanan watan 5 ga watan Maris, ta ce ba za ta mutunta gayyatar da aka yi wa Fubara ba.
Takardar mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin Ribas, Dr. Tammy Danagogo, ta ce ba ta karɓi wata sanarwa daga majalisar ba, illa dai ta samu labarin hakan ne daga kafafen sada zumunta.

Source: Twitter
A rahoton Leadership, Dr. Danagogo ya ce:
“Har zuwa ƙarshen lokacin aiki a ranar Talata, 4 ga Maris, 2025, ba mu samu takarda a hukumance daga Majalisar Dokoki ba.
"Babu wannan takarda a ofishin gwamna, mataimakin gwamna, ko kuma na Akanta-Janar na jihar."
Gwamna Fubara zai ɗauki matakin da ya dace
Gwamnatin Fubara ta tunatar da majalisar cewa a jawabin da gwamnan ya yi a ranar 2 ga Maris, ya ce, duk da ra’ayinsa kan hukuncin Kotun Koli, zai bi doka kuma zai aiwatar da matakan da suka dace domin moriyar al’umma.
Haka kuma, ta ce lauyoyin gwamnati na jiran takardar hukuncin Kotun Koli, kuma da zarar gwamnan ya samu cikakken bayani, zai aiwatar da matakin da ya dace.
Rikicin Ribas jarabawa ce daga Allah
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Simi Subara ya ce duk rikicin da ake fama da shi a jihar Ribas ba komai ba ne face jarabawa daga Allah.

Kara karanta wannan
Majalisar shari'ar Musulunci ta goyi bayan rufe makarantu, ta kirayi jihohi 3 su bi sahu
Gwamnan ya shaida wa babban limamin coci cewa Allah ya jaraba Ribas da wannan matsala ne domin shi da sauran al'umma su sami cikakken ƴanci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
