Rigimar Ciyamomi Ta Hana Gwamnan PDP Sukuni, Ya Je Neman Mafita wajen Jigon APC

Rigimar Ciyamomi Ta Hana Gwamnan PDP Sukuni, Ya Je Neman Mafita wajen Jigon APC

  • Gwamnan Osun ya kai ziyara ga tsohon shugaban APC, Cif Bisi Akande, inda suka shafe sa’o’i biyu suna tattaunawa kan batutuwan siyasa
  • Gwamnatin jihar ta ce ganawar ta mayar da hankali kan rikicin shugabancin kananan hukumomi da kuma burin Adeleke na neman tazarce
  • Bisi Akande ya yaba wa Adeleke bisa wannan ziyarar ta neman shawara musamman ganin cewa suna da bambancin ra'ayi a jam'iyya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya kai ziyara ga tsohon shugaban jam’iyyar APC, Chief Bisi Akande, inda suka yi ganawar sirri na tsawon sa’o’i biyu.

Adeleke ya ziyarci Akande a gidansa da ke Ibadan, tare da shugaban majalisar Osun, Adewale Egbedun, da sakataren gwamnati, Teslim Igbalaye.

Gwamnatin Osun ta yi magana da Gwamna Adeleke ya ziyarci jigon jam'iyyar APC
Gwamnan Osun ya ziyarci tsohon shugaban APC kan rigimar kananan hukumomi. Hoto: @Osun_State_Gov
Source: Twitter

Gwamna Adeleke ya ziyarci jigon APC

Kara karanta wannan

Natasha: 'Yan siyasar Arewa sun huro wuta, suna so shugaban majalisa ya yi murabus

Tawagar gwamnan ta hada da shugaban ma’aikatan gwamnati, Kazeem Akinleye, Antoni Janar, Wole Jimi-Bada, da kwamishinan labarai, Kolapo Alimi, inji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa ganawar na da nasaba da rikicin shugabancin kananan hukumomi da ke gudana tsakanin ciyamomin APC aka mayar ofis da sababbin shugabannin PDP a jihar.

Haka nan, ana kyautata zaton cewa ganawar Adeleke da Akande na da alaka da burinsa na neman wa’adin mulki na biyu a 2026.

Adeleke na tuntubar kusoshin jihar Osun

Kakakin gwamnan, Olawale Rasheed, ya tabbatar da cewa ganawar ta mayar da hankali kan rikicin shugabancin kananan hukumomi a jihar Osun.

Rasheed ya ce Adeleke ya kaddamar da shirin tuntubar manyan jiga-jigan siyasa don tattauna batun rikicin da ya dabaibaye shugabancin kananan hukumomi.

Kakakin gwamnan ya ce:

"Gwamnan zai gana da majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Osun a wani zama na musamman don sanar da su ci gaban da aka samu kan rikicin.
"Adeleke ya tattauna da Akande kan batutuwan da suka shafi Osun da kasa baki daya, yana mai jaddada bin doka wajen warware matsalolin siyasa."

Kara karanta wannan

An tsallake Tinubu, Atiku an ba Kwankwaso lambar karramawa a Najeriya

Jigon APC ya ba gwamnan PDP shawara

Jigon APC ya yi magana da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Osun
Tsohon shugaban APC ya gana da gwamnan Osun, sun tattauna na tsawon awa biyu. Hoto: @Osun_State_Gov
Source: Twitter

Rasheed ya ce gwamnan ya kuma jaddada goyon bayan Osun ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa suna da kyakkyawar alaka da gwamnatin tarayya.

"A kan siyasar kasa, Gwamna Adeleke ya yaba da rawar da Chief Akande ke takawa wajen daidaita shugabanci a jihar da kuma kasa, yana mai cewa Osun na alfahari da shi."

- Olawale Rasheed.

Bisi Akande ya yaba wa Adeleke kan wannan ziyara, yana mai cewa hakan alama ce ta shugabanci nagari duk da bambancin jam’iyyunsu.

Akande ya bayyana cewa ya saurari jawabin da tawagar gwamnan ta gabatar, inda ya bukaci a ci gaba da bin doka da oda domin amfanin jihar.

Adeleke zai koma jam'iyyar APC?

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya karyata jita-jitar cewa yana shirin barin PDP don komawa APC, yana mai cewa labarin ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware kudin ciyarwa a Ramadan, ta fadi abin da za ta kashe

A wata sanarwa da kakakinsa, Mallam Olawale Rasheed, ya fitar, ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya kuma ƙage maras tushe ko madogara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com