PDP Ta Ji Jiki a Zamfara, Jiga Jiganta da Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Sun Shiga APC

PDP Ta Ji Jiki a Zamfara, Jiga Jiganta da Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Sun Shiga APC

  • Dan majalisar wakilai, Hon. Aminu Jaji ya karɓi sababbin tuba zuwa jam'iyyar APC a jihar Zamfara
  • Hon. Jaji ya karbi dan takarar gwamna a AAC, Muhammad Kabir-Sani da magoya bayansa bayan sun sauya sheƙa daga jam'iyyar da PDP
  • Kabir-Sani ya ce sun shiga APC saboda gamsuwa da ayyukan wakilci na Jaji, yayin da Ibrahim Labbo-Anka ya ce APC ce mafi ƙarfi a Zamfara
  • Jaji ya ce sauya sheƙar waɗanda suka shiga APC zai ƙarfafa jam’iyyar, ya kuma tabbatar musu da adalci da haɗin gwiwa a harkokin siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Dan majalisar wakilai, Aminu Jaji ya karɓi jiga-jigan jam'iyyun adawa zuwa APC a jihar Zamfara.

Hon. Jaji ya karbi tsohon ɗan takarar gwamna na AAC a zaɓen 2023, Muhammad Kabir-Sani da magoya bayansa.

Kara karanta wannan

Bayan kusoshin APC sun kaurace wa taron jam'iyya, Tinubu ya dora wa Ganduje aiki

APC ta nakasa PDP da sauran jam'iyyun adawa a Zamfara
Hon. Aminu.Jaji ya karbi jiga-jigan PDP da sauran jam'iyyun adawa zuwa APC. Hoto: Hon. Aminu Sani Jaji, Dauda Lawal.
Asali: Facebook

Jiga-jigan jam'iyyun adawa sun dawo APC

Premium Times ta ruwaito cewa Kabir-Sani ya sauya sheƙa tare da wasu ’yan takarar majalisar dokokin jiha na PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗanda suka sauya sheƙar da dubban magoya bayansu sun shiga APC ta hannun tafiyar Jajiyya APC karkashin jagorancin Isiyaka Ajiya-Anka.

Sun bayyana shiga APC tare da dubban mambobin AAC da PDP bayan wata ganawa da suka yi da dan majalisa a gidansa da ke Gusau.

Tsohon ɗan takarar gwamnan AAC ya ce sun shiga APC ne karkashin tafiyar siyasar Jaji.

Ya ce:

“Mun gamsu da ayyukan wakilcin Aminu Jaji da irin ci gaban da ya kawo wa mazaɓarsa da Zamfara gaba ɗaya."

Ibrahim Labbo-Anka, wakilin ’yan takarar majalisar dokokin PDP, ya ce sun shiga APC saboda ita ce jam’iyya mafi ƙarfi a jihar.

A cewarsa:

“Muna da kyakkyawar fahimta da Hon. Aminu Jaji, don haka muka yanke shawarar zama cikin APC don cigaban jihar mu."

Kara karanta wannan

An yanke makomar Ganduje, APC ta bayyana yankin da ta maida shugabancin jam'iyya

APC ta yi nasarar karbar sababbin tuba a Zamfara
Jam'iyyar APC ta nakasa PDP da sauran jam'iyyun adawa a Zamfara. Hoto: All Progressives Congress.
Asali: Twitter

Alkawuran da Hon. Jaji ya yi musu

Yayin karɓar waɗanda suka sauya sheƙa, Jaji, wanda shi ne shugaban kwamitin kula da Asusun Muhalli a majalisa, ya yaba musu.

Dan majalisar ya ce wannan sauya sheƙa babban ci gaba ne ga APC a jihar da Najeriya gaba ɗaya.

Ya tabbatar da cewa za a yi wa sababbin mambobin adalci tare da haɗa kai don ƙarfafa jam’iyyar, cewar TheCable.

Jaji ya ce kwarewar siyasa da cancantar shugabannin da suka sauya sheƙa za su ƙara ƙarfin tafiyar Jajiyya da APC.

Hon. Jaji ya ce:

“Ina roƙonku da ku tsaya da APC kuma ku ba da gudunmawar da za ku iya don cigaban jam’iyyar."

Shugaban tafiyar APC-Jajiyya, Isiyaka Ajiya-Anka, ya ce wannan tafiya ce mafi ƙarfi a jihar, tana da tasiri a kananan hukumomi 14.

Sule Lamido ya soki salon mulkin APC

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce mulkin APC ya yi kamanceceniya da na Fir’auna da aka yi a tarihi.

Sule Lamido ya ce talauci ya zama makami, yunwa kuma tana yawo a titunan kasar wanda ke illa ga al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.