Gwamna a Arewa Ya Samu Goyon Baya, Ana So Ya Nemi Takarar Shugaban Ƙasa a 2027

Gwamna a Arewa Ya Samu Goyon Baya, Ana So Ya Nemi Takarar Shugaban Ƙasa a 2027

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed na ci gaba da samun goyon baya daga al'umma tare da kiraye-kirayen ya nemi takara
  • Gamayyar dattawa da matasan kiristoci ƴan siyasa na jihar Bauchi sun ayyana cikakken goyon baya ga Gwamna Bala a 2027
  • Sun jaddada cewa za su yi wa mai girma gwamnan biyayya kan duk ɗan takarar da ya tsayar don ya gaje shi a jihar Bauchi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da.kullum

Bauchi - Ƙungiyar gamayyar matasa da dattawan kiristoci ƴan siyasa ta ayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamna Bala Muhammed a shirinsa na takara a 2027.

Kungiyar ta sha alwashin marawa duk wani dan takarar da gwamnan zai tsayar a zaben 2027 baya, ciki har da wanda zai gaje shi a kujerar gwamnan jihar Bauchi.

Gwamna Bala Muhammed.
Kungiyar kiristoci ta ayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamna Bala Mohammed a 2027 Hoto: Sen. Bala Mohammed
Asali: Facebook

Shugabannin kungiyar, Joel Joshua da Ɗanladi Audu ne suka bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Laraba a Bauchi, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

APC ta fadi abin da zai mayar da Tinubu kujerarsa bayan zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun jinjinawa Bala Mohammed bisa shugabancinsa na bai daya, mai adalci da rashin nuna banbanci.

A cewarsu, Gwamna Bala ya tabbatar da hadin kan kabilu da addinai ba tare da nuna bambanci ba a faɗin jihar Bsuchi.

Kira ga Gwamna Bala ya fito takara a 2027

Kungiyar ta kuma bukaci Gwamna Bala Mohammed da ya saurari kiraye-kirayen da ake masa daga sassa daban-daban na kasar nan na ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027.

“Muna kara jaddada bukatar jama’a da kiran Gwamna Bala ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027.
"Yana daya daga cikin shugabannin da suka cancanta, waɗanda za su iya ceto Najeriya daga matsalolin tattalin arziki da tsaro. Muna masa addu’a tare da cikakken goyon baya,” in ji kungiyar.

Nasarorin da gwamnan ya cimma a Bauchi

Kungiyar ta yaba da kokarin gwamnan wajen samar da tsaro da ingantaccen shugabanci a shekarun da ya shafe yana mulkin Bauchi.

Kara karanta wannan

Shirin babban taron APC ya gama kankama, jagororin jam'iyya sun hallara Abuja

Ta ƙara da cewa Bauchi na daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Arewa maso Gabas a karkashin jagorancinsa.

Haka kuma, kungiyar ta jaddada irin kyakkyawar alaka da gwamnan ke da ita da Kiristoci, tana mai tunatar da cewa a 2023, ya dauki nauyin kiristoci 176 zuwa aikin hajji a Isra’ila tare da ba su tallafin kuɗi domin jin dadinsu.

Gwamna Bala Mohammed.
Kiristoci sun marawa gwamnan Bauchi baya, sun nemi ya fito takara a 2027 Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Facebook

Kungiyar ta bukaci gwamnan ya tabbatar da cewa Bauchi za ta cigaba da samun shugabanci mai nagarta bayan wa’adinsa.

“Mun aminta da cewa idan lokacin zabe ya zo, mai girma gwamna zai zabi mutumin da ya cancanta, wanda zai ci gaba da kyawawan ayyukan da yake yi,” in ji kungiyar.

Gwamna Bala ya damu da ƙarancin abinci

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Bala ya bayyana cewa abin kunya ne ƙasa kamar Najeriya ta gaza samar da wadataccen abinci da jama'arta.

Ƙauran Bauchi ya nuna damuwa kan ƙarancin abinci da ake fama da shi, ya ce jiharsa a shirye take ta ba masu zuba hannu jari a ɓangare noma dukkan dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262