Jerin Majalisun Dokoki na Jihohi 6 da Aka Sha Fama da Rikicin Shugabanci a Najeriya

Jerin Majalisun Dokoki na Jihohi 6 da Aka Sha Fama da Rikicin Shugabanci a Najeriya

A makon jiya ne rikicin da ya ɓarke a Majalisar dokokin jihar Legas ya buɗe sabon shafi, inda jami'an tsaro suka mamaye zauren Majalisar ranar Litinin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rikicin dai ya ƙara ƙamari a lokacin da dakarun suka rufe ofisoshin kakakin majalisar dokokin, Hon. Mojisola Meranda, mataimakinta da magatakarda.

Majalisar dokokin jihar Legas.
Jerin jihohin da aka sha fama da rikicin shugabanci a Majalisar dokoki Hoto: Mojisola Meranda
Asali: Twitter

Duk wannan rigima da ke faruwa ta samo asali ne daga tsige tsohon kakakin majalisar, Hon. Mudashiru Obasa, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Tsige Obasa ya raba kawunan shugabannin APC a jihar Legas, wasu na ganin ƴan majalisar sun yi gaban kansu wajen canza shugabanci ba tare da tuntuba ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tattaro maku rigingimun shugabanci da suka faru a wasu Majalisun dokoki na jihohin ƙasar nan, ga su kamar haka:

Kara karanta wannan

"Akwai sauran rigima": Kotu ta yi hukunci kan batun tsige ɗan Majalisar Zamfara

1. Majalisar dokokin jihar Legas

Rigima ta ƙara ɗaukar zafi a Majalisar dokokin jihar Lagos lokacin da jami’an DSS suka mamaye zauren bisa umarnin magatakarda, rahoton This Day.

A wannan rana, 'yan majalisa sun kutsa kai cikin zauren majalisar da karfi, inda suka bayyana goyon bayansu ga sabuwar kakaki, Hon. Mojisola Meranda.

Majalisar GAC, wanda shi ne lamba ɗaya wajen yanke shawara a APC ta Legas, ya shirya ganawa da shugaba Bola Tinubu domin tattaunawa kan rikicin da ke faruwa a majalisar.

Mudashiru Obasa, Meranda.
Tsige Obasa daga shugabancin Majalisar dokokin Legas ta haifar da rikici Hoto: Mudashiru Obasa, Mojisola Meranda
Asali: Twitter

An ruwaito cewa rikicin ya kara kamari sakamakon yunkurin tsohon kakakin majalisa, Hon. Mudashiru Obasa, na komawa kan mukaminsa.

Obasa, wanda aka tsige daga mukaminsa a ranar 13 ga Janairu, 2025, ya kai majalisar da sabuwar kakakin gaban babbar botun jihar Legas da ke Ikeja.

Ya kalubalanci matakin cire shi daga muƙaminsa, yana mai cewa an tsige shi ne ba bisa ka’ida ba, duba da cewa majalisar tana cikin hutun aiki a lokacin da hakan ta faru.

Kara karanta wannan

Mai alfarma sarkin musulmi ya aika saƙo ga malamai ana shirin fara azumin Ramadan

2. Majalisar dokokin jihar Ribas

A watan Disamba 2023, aka fara zargin cewa mambobi 27 na Majalisar dokokin Ribas sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC, a lokacin da rikicin siyasa ya tsananta a jihar.

Wadannan ‘yan majalisa, karkashin jagorancin Rt. Hon. Martins Amaewhule, suna da goyon bayan tsohon gwamnan jihar, kuma ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike.

Oko Jumbo
Majalisar dokokin jihar Ribas na fama da rikici tun bayan sauya shekar ƴan Majalisa 27 Hoto: Victor Oko Jumbo
Asali: Facebook

A gefe guda, wani bangare na majalisar da ke karkashin jagorancin Victor Oko Jumbo wanda ke da mambobi biyar, yana goyon bayan Gwamna Simi Fubara.

Wannan rikici na ci gaba da jefa siyasar jihar Ribas cikin rudani, lamarin da ya kai shigar ƙararraki gaban kotu, kamar yadda Ripples Nigeria ta kawo.

3. Majalisar dokokin jihar Ogun

A watan Janairu 2024, ƴan majalisar dokokin Jihar Ogun 18 suka tsige Olakunle Oluomo daga mukamin kakakin majalisar.

Daily Trust ta tattaro cewa bayan tsige shi, majalisar ta zabi Hon. Oludaisi Elemide, wanda ke wakiltar mazabar Odeda, a matsayin sabon kakaki.

Kara karanta wannan

Dakatar da ƴan Majalisa 4 a Kano ya tayar da ƙura, sun yi wa Kwankwaso rubdugu

Olakunle Oluomo
Majalisar dokokin jihar Ogun ta sauke Olakunle Oluomo daga matsayin kakaki Hoto: Olakunle Oluomo
Asali: Facebook

Rahotanni sun nuna cewa lokacin da aka tsige shi, Oluomo ya tafi cibiyar al’adu ta June 12 a Kuto, Abeokuta, domin halartar bikin rantsar da alkalai.

Gwamnan jihar, Dapo Abiodun ya danganta tsige Oluomo da rikicin cikin gida da ya daɗe yana faruwa a majalisar, wanda ya kara kamari duk da yunkurin sasanta bangarorin da suka samu sabani.

4. Majalisar dokokin jihar Ondo

A ranar 2 ga Yuni, 2023, jami’an tsaro suka rufe Majalisar dokokin jihar Ondo sakamakon wani yunkuri na tsige kakakin majalisar, Bamidele Oloyelogun.

Wannan mataki ya biyo bayan wata wasikar murabus da ake zargin an rubuta a madadin Hon. Oloyelogun.

Majalisar Ondo.
Yadda rigima ta kaure kan shugabanci a Majalisar dokokin Ondo Hoto: Ondo State House Of Assembly
Asali: Facebook

Rahotanni sun bayyana cewa an rubuta wasikar ne cikin gaggawa don gujewa tsige shi, kwanaki kadan kafin karewar wa’adin majalisa ta 9 da yake jagoranta.

Jami’an tsaro sun toshe dukkanin kofofin shiga majalisar, lamarin da ya dakatar da duk wani aiki, komai ya tsaya cak.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30

A ranar 4 ga Yuni, 2023, Olamide Oladiji ya zama sabon kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, kamar yadda Daily Post ta tattaro.

5. Majalisar dokokin jihar Nasarawa

A 2023, rikici mai cike da rudani ya barke a Majalisar dokokin jihar Nasarawa, wanda ya kai ga darewar Majalisar gida biyu, kowane na ikirarin shugabanci.

An zabi Hon. Daniel Ogazi da Hon. Ibrahim Balarabe Abdullahi dukkansu ‘yan jam’iyyar APC a matsayin shugabannin majalisar a lokuta daban-daban, cewar rahoton Gazettengr.

Majalisar dokokin Nasarawa.
Majalisar dokokin Nasarawa ta sha fama da rikici a farkon 2023 Hoto: Nasarawa State House
Asali: Facebook

Abdullahi, wanda shi ne tsohon kakakin majalisar, kuma wanda ke neman wa’adi na uku, an sake zabarsa ne a wani zama da aka yi a ma’aikatar ƙananan hukumomi.

A daya bangaren kamar yadda Channels tv ta kawo labari cewa Hon. Ogazi ya bayyana a matsayin kakakin majalisar a lokacin wani zama da mambobi suka gudanar a harabar majalisar da ke Lafia.

6. Majalisar dokokin jihar Benuwai

Kara karanta wannan

'Yan Majalisa 27 sun tattara kayansu sun fice daga jam'iyyar APC? an samu bayanai

A 2018, ‘yan majalisar dokokin Benuwai sun dakatar da kakakin majalisar da suka tsige, Terkimbi Ikyange, na tsawon watanni shida bisa zargin rashin ɗa'a.

‘Yan majalisar sun yanke wannan hukunci ne a zaman da suka yi a gidan gwamnati da ke Makurdi, saboda ‘yan sanda sun kulle kofar shiga zauren majalisar kan rikicin da ke faruwa.

Majalisar Benue.
Rikicin majalisar dokokin jihar Benuwai Hoto: Benue State House Of Assembly
Asali: Facebook

Wasu daga cikin ‘yan majalisar sun yi kokarin haura katangar majalisar don su shiga harabar ginin, amma sai suka tarar da ɗakin da suke zama a kulle.

Bayan sun kasa gudanar da zamansu a zauren majalisar, sai suka koma gidan gwamnati, suka ci gaba da harkokinsu har suka dakatar da kakakin, rahoton Channels tv.

Kakakin majalisar Legas ta yi murabus?

A wani rahoton, kun ji cewa kakakin Majalisar dokokin jihar Legas, Hon. Majisola Meranda ta ƙaryata labarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa ta yi murabus.

Hon. Meranda, mace ta farko da Allah ya ba matsayin shugabar Majalisar dokokin Legas a tarihi, ta ce tana nan daram a kujerarta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262