APC Ta Yi Bayani kan Ƴan Majalisa 27 da Ake Zargin Sun Sauya Sheka daga PDP zuwa cikinta

APC Ta Yi Bayani kan Ƴan Majalisa 27 da Ake Zargin Sun Sauya Sheka daga PDP zuwa cikinta

  • Shugaban APC a Ribas, Tony Okocha ya ce ƴan Majalisar Dokoki 27 na tsagin Nyesom Wike ba ƴan jam'iyyarsa ba ne
  • Okocha ya bayyana cewa har yanzu babu wata shaida da ke nuna ƴan Majalisar sun sauya sheka daga PDP zuwa APC
  • Ya soki Gwamna Siminalayi Fubara bisa yadda yake tafiyar da gwamnatinsa ba bisa ƙa'ida ba, tare da take umarnin kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Jam’iyyar APC reshen jihar Ribas ta bayyana cewa ƴan majalisar dokokin jihar guda 27 karkashin jagorancin Rt. Hon. Martins Amaewhule ba ƴaƴanta ba ne.

APC ta tabbatar da cewa ƴan majalisar waɗanda ake zargin sun bar PDP, ba su sauya sheƙa zuwa cikinta ba kamar yadda ake yaɗawa.

Shugaban APC a Ribas, Okocha.
APC ta ce ƴan majalisar tsarin Wike ba 'ya'yanta ba ne Hoto: @OfficialAPCNig
Asali: Facebook

Shugaban APC a jihar Ribas, Cif Tony Okocha, ne ya faɗi haka da yake hira da manema labarai yau Talata a Fatakwal, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Mun inganta tsaro," Shugaba Tinubu ya yi magana bayan El Rufai ya faɗi maganganu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu shaidar ƴan majalisan Ribas sun shiga APC

Okocha ya jaddada cewa babu wani lokaci da APC ta karɓi wadannan ‘yan majalisa duk da jita-jitar da ke yawo cewa sun koma APC.

Ya ce taron da aka yi a wancan lokacin ba taron karɓan su ba ne, biki ne na murnar kafa sabon kwamitin zartarwar APC a jihar, wanda NWC na ƙasa ya naɗa.

"Ba mu shirya wani biki domin karɓar ‘yan majalisar ba. Mun gayyace su ne kawai a matsayin abokai, domin muna da kyakkyawar alaka da su. Mun so su shigo jam’iyyarmu amma ba su amince ba."

Okocha ya ce a bisa dokokin sauya sheka, dole ne mutum ya fara rajista a matakin mazabarsa kafin a iya tabbatar da shi a matsayin sabon mamba.

Sai dai ya ce har yanzu ba a sami wata shaida ba da ke nuna cewa wadannan ‘yan majalisa sun yi rijista da APC a mazaɓunsu ba.

Kara karanta wannan

Martanin jiga jigan siyasar Najeriya kan abin da littafin IBB ke kunshe da shi

Shugaban APC ya soki Fubara da take doka

Shugaban APC ya kuma zargi Gwamna Siminalayi Fubara, da rashin bin umarnin kotu, wanda ya ce hakan barazana ce ga zaman lafiya da bin doka da oda a Ribas.

Martins Amaewhule.
APC ta musanta sauya sheƙar ƴan majalisa 27, ta caccaki Gwamna Fubara Hoto: Martins Amaewhule
Asali: Facebook

Okocha ya ƙara da cewa:

"Kotu ta bayar da umarni cewa dole ne a sake gabatar da kasafin kudin 2024 ga majalisar karkashin jagorancin Martins Amaewhule, amma gwamna ya ki bin umarnin."

Ya ce tsarin mulki bai amince gwamna ya gudanar da jiha ba tare da cikakken kasafin kudi daga majalisa ba.

A cewarsa, kotu ta riga ta bayyana cewa ba zai yiwu a ce majalisar dokoki kunshi mutum uku kaɗai ba.

Kotun koli ta tabbatar da ƴan Majalisa 27

A wani labarin, kun ji cewa Kotun Koli ta yi watsi da karar da Gwamna Simi Fubara na jihar Ribas ya shigar yana neman a tsige ‘yan majalisar dokoki guda 27 na tsagin Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Dakatar da ƴan Majalisa 4 a Kano ya tayar da ƙura, sun yi wa Kwankwaso rubdugu

Gwamna Fubata ya maka ƴan Majalisa a kotu ne kan sauya sheƙar da yake ikirarin sun yi daga jam'iyyarsu ta PDP zuwa APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262