'Neman Gindin Zama?': An Ji Dalilan Wasu 'Yan Majalisar Tarayya 9 na Komawa APC

'Neman Gindin Zama?': An Ji Dalilan Wasu 'Yan Majalisar Tarayya 9 na Komawa APC

Abuja - A yayin da ake tunkarar kakar zabe ta 2027, harkokin siyasa na kara daukar zafi a Najeriya, yayin da ‘yan siyasa ke kokarin kare matsayin da suke rike da shi.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A cikin kasa da shekaru biyu na mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu, 'yan majalisar tarayya akalla tara sun sauya sheka daga jam'iyyun da suka ci zabe a 2023 zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

'Yan majalisar tarayya 9 ne suka fice daga jam'iyyunsu zuwa APC tun bayan hawan Tinubu mulki
2023-2025: 'Yan majalisar tarayya 9 sun fice daga jam'iyyunsu zuwa APC. Hoto: @EzenwaOnyewuchi, @Prince_NedNwoko, @Connected_dev
Asali: Twitter

Siyasar 2027 ta fara daukar zafi a Najeriya

Bayan da aka kafa ta a 2013, APC ta karbe mulki daga PDP a zaben 2015 bayan PDP ta shafe shekaru 16 tana mulkin kasar, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da kokarin da PDP ke yi don komawa kan mulki, har yanzu hakan bai yiwu ba. A zaben 2023, jam’iyyun LP da NNPP sun shiga takara, wanda ya kara dagula lissafi a siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai wa fulani makiyaya hari, an sace basarake da wasu mutum 38

Jam’iyyar APC na ci gaba da kokarin rage karfin 'yan adawa, yayin da jam’iyyun hamayya ke sake tsara dabarun kwace mulki daga hannun APC.

Yayin da 'yan majalisar tarayya 9 suka koma APC, da yawansu sun danganta sauya shekarsu da rikice-rikicen cikin gida na jam'iyyun da suka bari.

'Yan majalisar tarayya 9 da suka bar jam'iyyunsu

Ga dai cikakken bayani kan wasu daga cikin waɗannan 'yan majalisar:

1. Sanata Francis Onyewuchi

Sanata Ezenwa Francis Onyewuchi ya sanar da ficewarsa daga LP zuwa APC a Yulin 2024.
Sanata Ezenwa Francis Onyewuchi ya ce ya fice daga LP zuwa APC saboda rikicin jam'iyya. Hoot: @EzenwaOnyewuchi
Asali: Twitter

A watan Yulin 2024, Sanata Francis Onyewuchi, mai wakiltar Imo ta Gabas, ya sauya sheka daga jam'iyyar LP zuwa APC mai mulki a kasa, kamar yadda muka ruwaito.

Sanata Onyewuchi ya bayyana cewa ya yanke wannan shawarar ne sakamakon rikice-rikicen cikin gida da rabuwar kai a matakan ƙasa da na jiha na jam'iyyar LP.

A lokacin da ya sanar da sauya shekar tasa, ya nuna damuwarsa kan yadda rashin jituwa tsakanin shugabannin LP ke shafar ci gaban jam'iyyar da kuma wakilcin al'ummar da ya ke yi.

Kara karanta wannan

An samu rudani kan rasuwar dan wasan Najeriya a kasar waje

Haka nan, ya yi nuni da cewa rabuwar kai a jam'iyyar na iya yin illa ga muradun al'ummar da ya ke wakilta, don haka ya ga dacewar komawa APC domin ci gaba da hidimtawa jama'arsa yadda ya kamata.

2. Sanata Ned Nwoko

Sanata Ned Nwoko ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC a Fabrairun 2025
Sanata Ned Nwoko ya ce akwai rikice-rikice a PDP, shi ya sa ya koma APC. Hoto: @Prince_NedNwoko
Asali: UGC

A watan Fabrairun 2025, Sanata Ned Nwoko, mai wakiltar Delta ta Arewa a majalisar dattawa, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Mun ruwaito cewa Sanata Nwoko ya danganta sauya shekarsa da rikice-rikice da rabuwar kai a cikin PDP, wanda ya ce hakan na iya yin illa ga ci gaban al'ummar da ya ke wakilta.

Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda rashin hadin kai a jam'iyyar ke hana aiwatar da manufofin da za su amfani jama'a.

Sanata Nwoko ya yi imanin cewa komawarsa jam'iyyar APC za ta ba shi damar ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba ga al'ummar Delta ta Arewa ba tare da cikas ba.

Kara karanta wannan

El Rufa'i: APC ta hango barazana a 2027, ta bukaci Tinubu ya dauki mataki

3. Hon. Amos Gwamna Magaji

Dan majalisar Kaduna, Amos Gwamna Magaji ya fadi dalilin sauya shekarsa daga PDP zuwa APC
Hon. Amos Gwamna Magaji daga Kaduna, ya fice daga PDP zuwa APC a Fabrairun 2025. Hoto: @Connected_dev
Asali: Twitter

A cikin watan Fabrairun 2025, Hon. Amos Gwamna Magaji, mai wakiltar mazabar Zangon Kataf/Jaba a majalisar wakilai, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Legit Hausa ta rahoto Hon. Magaji ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida na PDP a matakan jiha da ƙasa ne suka sa ya yanke shawarar komawa APC.

Hon. Magaji ya yi imanin cewa jam'iyyar APC za ta ba shi damar ci gaba da hidimtawa al'ummar Zangon Kataf/Jaba yadda ya kamata.

Yayin da dan majalisar ya ce akwai rigingimu a PDP, a hannu daya, Hon. Kingsley Chinda, shugaban marasa rinjaye, ya musanta batun rikici a jam'iyyar.

Hon. Amos Hon. Chinda ya bukaci Abbas ya ayyana kujerar Magaji a matsayin babu kowa a kanta bisa tanadin sashe na 68 na kundin tsarin mulkin 1999.

4. Hon. Chris Nkwonta

Dan majalisar PDP, Christian Nkwonta ya fice daga PDP zuwa APC
Dan majalisar PDP daga Abia ya koma APC Hoto: @Imranmuhdz, @FrancisAdeboye
Asali: Twitter

A watan Oktoban 2024, Hon. Christian Nkwonta, mai wakiltar mazabar Ukwa ta Gabas/Ukwa ta Yamma a majalisar wakilai, ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan

'APC suka yi wa aiki': PDP ta fallasa asirin yan siyasar da suka bar jam'iyyar a Kaduna

Hon. Nkwonta ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida na jam'iyyar PDP ne suka sa ya yanke shawarar sauya sheka.

Ya nuna damuwarsa kan yadda rashin jituwa a jam'iyyar ke hana ci gaban al'ummar da ya ke wakilta, a cewar rahoton Legit Hausa.

Sai dai, mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Aliyu Madaki, ya nuna rashin amincewarsa da sauya sheƙar.

Da yake kafa hujja da sashe na 68 na kundin tsarin mulkin ƙasar nan, Aliyu Madaki ya ce ɗan majalisa zai iya ficewa ne kawai daga jam’iyyar da ta ɗauki nauyin zaɓensa idan aka samu rikici a cikinta.

5. Hon. Alfred Illiya Ajang

Dan majalisar Jos ya sanar da ficewarsa daga LP zuwa APC a watan Disambar 2024.
An samu hatsaniya a majalisar wakilai da Hon. Alfred Illiya Ajang ya fice daga LP zuwa APC. Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

A ranar 12 ga Disamban 2024, Hon. Alfred Illiya Ajang, mai wakiltar mazabar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas a majalisar wakilai, ya sauya sheka daga jam'iyyar LP zuwa APC.

Hon. Ajang ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida na jam'iyyar LP ne suka sa ya yanke shawarar komawa APC.

Kara karanta wannan

'Yan adawa na kulla sabon shiri domin tunkarar Tinubu da gaske a 2027

Sai dai rigima ta barke a majalisar tarayya yayin da dan jam'iyyar na LP ya koma APC mai mulkin, kamar yadda muka rahoto.

Mambobin Majalisar daga ɓangaren adawa sun ki amincewa da sauya shekar inda suka ta da bore tare da neman a ayyana kujerar Alfred a matsayin wadda ba kowa a kanta.

Yayin da yake karanta wasikar sauya shekar, shugaban majalisar, Tajudden Abbas ya ce Iliya ya bar LP ne saboda rikicin jam'iyyar kuma ya koma APC saboda ayyukan alheri da Bola Tinubu ke yi a Najeriya.

6. Hon. Salisu Garba Koko

A watan Fabrairun 2025, Hon. Salisu Garba Koko, dan majalisar wakilai daga mazabar Basee/Maiyama a jihar Kebbi ya sauya sheka zuwa APC daga PDP.

A wasikar da ya aikawa majalisar wakilan, Hon. Salisu ya ce ya yanke shawarar sauya shekar ne saboda "rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa" a cikin PDP.

The Nation ta rahoto cewa shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda ya yi adawa da sauya shekar inda ya karyata cewa akwai rikici a PDP.

Kara karanta wannan

Yadda adawar manyan yan siyasar Najeriya za ta shafi tasirin gwamnatin Tinubu

Kingsley ya ce kuskure ne dan majalisa ya likawa jam'iyya sharrin rikici kawai don zai sauya sheka, yin hakan a cewarsa zai jawo rikici ne a siyasance.

Ya bukaci shugaban majalisar ya wofantar da kujerar Salisu saboda sauya sheka - sai dai Tajuddeen Abbas ya ce kotu ce kawai za ta iya yin hakan.

'Yan majalisar LP sun koma APC

A ranar 5 ga Disamban 2024, wasu 'yan majalisar wakilai hudu daga jam'iyyar Labour Party sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC. Wadannan 'yan majalisa sun hada da:

  • Hon. Chinedu Okere, mai wakiltar mazabar Owerri/Owerri ta Arewa/Owerri ta Yamma a jihar Imo.
  • Hon. Mathew Donatus, mai wakiltar mazabar Kaura a jihar Kaduna.
  • Hon. Akiba Bassey, mai wakiltar mazabar Calabar/Odukpani a jihar Cross River.
  • Hon. Esosa Iyawe, mai wakiltar mazabar Oredo a jihar Edo.

Mun ruwaito cewa wadannan 'yan majalisa sun bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida na jam'iyyar LP ne suka sa su yanke shawarar komawa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ga ta kansa: An jero manyan ƴan siyasa 17 da suka fice daga jam'iyyar LP

Sun nuna damuwarsu kan yadda rabuwar kai a jam'iyyar ke hana aiwatar da manufofin da suka dace da muradun al'ummar da suke wakilta.

PDP ta soki 'yan majalisar da suka sauya sheka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam’iyyar PDP ta bukaci ‘yan majalisar dokokin Kaduna da na majalisar wakilai da suka sauya sheƙa zuwa APC da su ajiye kujerunsu.

Jam’iyyar ta jaddada cewa duk da cewa ‘yan siyasa na da ‘yancin sauya sheƙa, dole ne a bi tanadin kundin tsarin mulki.

PDP ta yi alkawarin amfani da dokokin kasa don kwato kujerun ‘yan majalisar da suka fice daga jam’iyyar kwanan nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.