Dakatar da Ƴan Majalisa 4 a Kano Ya Tayar da Ƙura, Sun Yi Wa Kwankwaso Rubdugu

Dakatar da Ƴan Majalisa 4 a Kano Ya Tayar da Ƙura, Sun Yi Wa Kwankwaso Rubdugu

  • Ƴan Majalisar Tarayya huɗu da aka dakatar daga NNPP a Kano sun caccaki jagoran jam'iyyar na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso
  • A wata sanarwar haɗin guiwa da suka fitar, sun ce halastacciyar NNPP ta tsagin Boniface Aniebonam ta jima da korar Kwankwaso da mabiyansa
  • A cewarsu, kotu ta rushe tsagin da Kwankwaso yake jagoranta don haka suka nemi magoya bayan NNPP su yi watsi da dakatarwar da aka yi masu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - A jiya Litinin ne jam’iyyar NNPP reshen Kano ta dakatar da ‘yan majalisar tarayya guda hudu bisa zargin cin amana da aiki da wasu jam’iyyun adawa.

Waɗanɗa aka dakatar kamar yadda shugaban jam’iyyar a Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa, ya faɗa su ne; Sanata Kawu Sumaila, Ali Madakin Gini, Sani Rogo, da Kabiru Rurum.

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da yan majalisar NNPP 4, jam'iyyar APC ta gamu da matsala a Kano

Kawu Sumaila da Kwankwaso.
Yan Majalisar da aka dakatar a Kano sun dura kan Kwankwaso Hoto: Kawu Sumaila, Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Ya ce an dakatar da su ne saboda zarginsu da yunƙurin kawo ɓaraka da kuma cin amanar NNPP, kamar yadda jaridar Punch ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan Majalisar NNPP 4 sun yi magana

Sai dai wannan dakatarwa ta harzuƙa ƴan Majalisar, sun bayyana cewa matakin ba shi da wani amfani domin ya saɓa doka.

A wata sanarwar haɗin guiwa da suka fitar, ƴan Majalisar sun ce:

"Dungurawa ba shi da hurumin tsoma baki kan harkokin NNPP, dakatar da mu wata makarkashiya ce kawai da nufin yaudarar jama’a da rufe gazawar bangaren Kwankwaso."

Sun kuma yi nuni da cewa hukuncin da kotun jihar Abia ta yanke a ranar 1 ga Nuwamba, 2024, ya tabbatar da Dr. Boniface Aniebonam a matsayin sahihin jagoran NNPP.

Ƴan majalisa sun jaddada korar Kwankwaso

Ƴan Majalisa sun kuma nanata cewa an kori Rabiu Kwankwaso da mabiyansa daga jam’iyyar NNPP tuntuni.

"An kori Kwankwaso da mabiyansa daga NNPP a hukumance, kuma kokarinsu na mallake jam’iyyar tamkar wata siyasar ruɗu ce kawai," in ji su.

Kara karanta wannan

Rikicin NNPP: Dan majalisa ya yi martani kan dakatarwar da aka yi masa, ya yi fallasa

Sun bukaci jama’a da su yi watsi da dakatarwar, domin suna nan daram a kan tafiyar da ke neman ceto NNPP daga hannun masu son zuciya.

An zargi Kwankwaso da mallake NNPP

‘Yan majalisar sun kuma zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da mallake jam’iyyar NNPP tamkar kadararsa ta siyasa, rahoton Vanguard.

"A Kano, Kwankwaso ke juya jam’iyyar NNPP, bai damu da haɗin kan ƴan jam'iyya ko bin ƙa'iopji da tanadin dimokuradiyya ba."

Sun ce Kwankwaso bai halarci daurin auren ‘ya’yan Sanata Kawu Sumaila, ko bikin yaye dalibai na Jami’ar Al-Istiqama ba, duk da cewa an aika masa da goron gayyata.

Rabiu Kwankwaso.
Yan majalisar da aka dakatar a NNPP sun caccaki Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Twitter

A cewarsu, hakan ya nuna cewa yana fargabar karfin siyasar da suke da ita, musamman ganin yadda manyan jiga-jigai a Kano kamar Malam Ibrahim Shekarau da shugaban APC, Abdullahi Ganduje, suka halarci bikin.

Ƴan Majalisar sun yi zargin cewa maimakon Kwankwaso ya mayar da hankali kan ci gaban Ƙano da jam’iyyar, yana amfani da NNPP a matsayin hanyar biyan bukatun kansa.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila da wasu ƴan majalisa 3

Dubban ƴan APC sun koma NNPP

A wani labarin, kun ji cewa mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam ya karɓi ƴan APC sama da 1,500 da suka sauya sheka zuwa NNPP.

Masu sauya sheƙar sun bayyana cewa sun baro APC ne saboda ta gaza cika alƙawurran da ta ɗauka na inganta walwalar al'umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262