2027: Ana Zargin Gwamnan PDP Ya Haɗa Kai da Gwamnatin Tinubu, Ya Fara Yi Wa APC Aiki

2027: Ana Zargin Gwamnan PDP Ya Haɗa Kai da Gwamnatin Tinubu, Ya Fara Yi Wa APC Aiki

  • Tsohon kwamishina a Bayelsa, Udengs Eradiri ya yi ikirarin cewa Gwamna Douye Diri ya haɗe kai da jam'iyyar APC a matakin ƙasa
  • Mista Eradiri, jigon APC kuma tsohon ɗan takarar gwamna ya buƙaci ƴan jam'iyyar su daina sukar Gwamna Diri domin an yi yarjejeniya da shi
  • Ɗan siyasar ya bayyana cewa haɗin guiwa tsakanin gwamnatin tarayya da Gwamna Diri na haifar da ɗa mai ido a jihar Bayelsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa - Ana zargin gwamnan jihar Beyelsa, Douye Diri, ya haɗa kai da jam'iyyar APC, yana cin amanar PDP a jiharsa.

Jigon APC kuma tsohon ɗan takarar gwamnan Bayelsa a inuwar jam'iyyar LP, Injiniya Udengs Eradiri ne ya yi wannan ikirari na cewa Gwamna Diri ya haɗa kai da APC.

Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa.
Gwamna Diri na yi wa jam'iyyar APC aiki a jihar Bayelsa, in ji Eradiri Hoto: Douye Diri
Asali: Facebook

Mista Eradiri, ya bukaci mambobin APC a Bayelsa da su daina sukar Gwamna Douye Diri, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ganduje ya firgita NNPP, ya fadi jiga jigan jam'iyyar da za su dawo APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Diri na tare da gwamnatin APC

Ya nanata cewa gwamnan yana aiki kafada da kafada da gwamnatin tarayya da jam'iyyar APC ke jagoranta, don haka babu buƙatar ƴan jam'iyya su rika sukarsa.

Da yake jawabi ga menama labarai a Yenagoa a ranar Lahadi, Eradiri ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar APC su girmama wannan yarjejeniya.

A cewarsa, hadin gwiwar da ke tsakanin Gwamna Douye Diri duk da ɗan PDP ne, da gwamnatin tarayya ta APC na haifar da manyan ayyukan ci gaba a Bayelsa.

Tsohon kwamishinan matasa da kuma na muhalli a jihar, Eradiri, ya jinjina wa gwamna Diri bisa samun goyon bayan gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Gwamnatin Bayelsa ta daina adawa da Tinubu

Ya ce Gwamna Diri ya samu goyon bayan Shugaba Tinubu wajen gudanar da manyan ayyuka da suka hada da titin Agge, tashar jiragen ruwa ta Deep Sea Port, da hanyar Nembe-Brass.

Kara karanta wannan

2027: Jigon PDP ya jijjiga tebur, ya fadi abin da ke shirin faruwa da APC a Arewa

Ya ƙara da cewa jihar Bayelsa ta wuce zaman adawa kuma yanzu tana cin gajiyar dangantakarta da gwamnatin APC a matakin tarayya, rahoton Vanguard.

"Gwamna Diri yana da wata yarjejeniya ta siyasa da mu watau APC domin ci gaban jiha kuma a sakamakon hakan, zai mikawa APC mulkin Bayelsa a 2027."
"Diri yana aiki tare da mu a APC, kuma muna farin ciki da yadda yake gina manyan tituna da ke hada karkara da yankunan da ke bakin teku zuwa babban birnin jihar."
Udengs Eradiri.
An bukaci ƴan APC su daina sukar gwamnan Bayelsa Hoto: Udengs Eradiri
Asali: Facebook

An roki ƴan APC su daina sukar Gwamna Diri

Eradiri ya kuma bukaci mambobin APC su daina sukar gwamnatin Bayelsa, yana mai cewa:

"Bayelsa ta fita daga siyasar adawa, yanzu muna aiki tare da APC a matakin tarayya. Ya kamata mambobin APC su girmama Gwamna Diri.
"Tun da ma yana da niyyar mika mulki ga APC a 2027, idan ma bai shigo cikinta ba kafin lokacin," in ji shi.

Kara karanta wannan

"Za a kayar da Tinubu": Kwankwaso ya hango wanda zai ci zaben shugaban ƙasa a 2027

Gwamna Diri ya ba bokaye kudi

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Douye Diri ya bayyana cewa ya kashe makudan kuɗi wajen bin bokaye a lokacin da yake neman mulkin jihar Bayelsa.

Douye Diri ya bukaci ƴan siyasa su rika dogaro da Ubangiji a duk kujerar da suke nema, yana mai jaddada cewa Allah ne ya taumake shi ya zama gwamna duk da ƙalubale.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262