‘Ina Abba da Kwankwaso?’ Yan NNPP ga Sumaila da Ya Gayyaci Ganduje, Barau
- An yi ta ce-ce-ku-ce a NNPP bayan Sanata Kawu Sumaila ya gayyaci Abdullahi Ganduje da Barau Jibrin wurin bikin ‘ya’yansa
- Dalilin ta da jijiyoyin wuya shi ne Sumaila bai gayyaci Gwamna Abba Yusuf ko jagorar siyasar Kano, Rabiu Kwankwaso ba
- Sumaila ya halarci taruka tare da jiga-jigan APC, lamarin da ya haddasa rade-radin cewa yana shirin sauya sheka daga NNPP zuwa APC
- Wasu ‘yan NNPP sun nuna damuwa kan yadda Sumaila da wasu ‘yan majalisa daga Kano Kudu suka nesanta kansu daga gwamnatinsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kano - Rikici ya kunno kai a jam’iyyar NNPP bayan da aka gano cewa Sanata Kawu Sumaila ya gayyaci shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje d ajia-jigan jam'iyyar.
Sumaila ya kuma gayyaci mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, zuwa taron bikin ‘ya’yansa, amma bai gayyaci Gwamna Abba Yusuf ko Rabiu Kwankwaso ba.

Kara karanta wannan
2027: El-Rufai ya fadi yankin da ya dace ya hada kai da Arewa domin ceto Najeriya

Asali: Facebook
Kano: An daura auren 'ya'yan Kawu Sumaila
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a, Barau Jibrin ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa shi ne ya jagoranci tawagar sanatoci zuwa bikin aure a Sumaila.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barau Jibrin ya ce:
"A yau, (21 ga Faburairu), na jagoranci tawagar majalisar dattawa zuwa bikin auren ‘ya’yan Sanata Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila da Alhaji Abdulmanaf Yunusa Sarina a garin Sumaila, Jihar Kano.
"Bikin auren Dr. Khadija Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila da Faisal Abdulmanaf Sarina, da kuma na Maryam Abdulrahman Kawu Sumaila da Bello.
"Shugaban jam’iyyarmu ta APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, CFR, shi ma ya halarci bikin. Allah ya albarkaci aurensu da hakuri, juriya, da soyayya. Muna taya su murna."

Asali: Facebook
Yan NNPP sun yi korafi kan auren 'ya'yan Sumaila
Premium Times ta ce wasu yan NNPP sun yi tambaya kan dalilin da ya sa Sumaila ya kaurace wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan
El-Rufai ya sake dagula siyasa, ya gana da shugabannin PDP, an yada hotunan ganawar
Sun koka yadda ya rungumi shugabannin jam’iyyun adawa kamar tsohon gwamna Ibrahim Shekarau na PDP.
Bayanai sun nuna cewa Sumaila da wasu ‘yan majalisa daga Kano ta Kudu sun saba da Gwamna Yusuf tun bayan da ya dawo da tsohon Sarkin Kano, Lamido Sanusi.
Zargin musabbabin samun matsalar Kwankwasiyya, Sumaila
‘Yan majalisar sun ce rusa sabbin masarautun da kuma tsige sarakuna guda biyar na barazanar ga muradun mazabarsu.
Tun daga wannan lokacin, Sumaila da wasu ‘yan majalisa daga yankin sun nesanta kansu daga harkokin gwamnatinsu.
Idan har Sumaila ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC, zai shiga jerin ‘yan majalisar adawa da ke komawa jam’iyya mai mulki.
Jam’iyyar NNPP ita ce jam’iyya ta hudu mafi girma a Najeriya dangane da yawan ‘yan majalisar da take da su a majalisun tarayya da na jihohi.
Kawu Sumaila: Manyan Najeriya sun cika Kano
Kun ji cewa jihar Kano ta cika makil yayin da aka daura auren ‘ya’yan Sanata Kawu Sumaila da Alhaji Abdulmanaf Sarina a Sumaila.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da sauran manyan ‘yan siyasa sun halarci bikin, inda suka taya sababbin ma’auratan murna da fatan alheri.
Asali: Legit.ng