Yadda Adawar Manyan Yan Siyasar Najeriya Za Ta Shafi Tasirin Gwamnatin Tinubu

Yadda Adawar Manyan Yan Siyasar Najeriya Za Ta Shafi Tasirin Gwamnatin Tinubu

Tun bayan da Bola Ahmed Tinubu ya hau kujerar shugabancin Najeriya, ya ke fuskantar suka daga wasu sanannun ‘yan siyasa, masu fafutuka, da kungiyoyin adawa.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Atiku
Sukar adawa za ta yi tasiri a kan gwamnatin Tinubu Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Legit ta yi waiwaye a kan wasu daga cikin manyan 'yan siyasa da ke adawa da tsarin mulkin Tinubu, da kuma yadda masana kimiyyar siyasa ke kallon yadda hakan zai dakile tasirin gwamnati.

1. Atiku ya soki tsarin mulkin Tinubu

Daya daga cikin manyan masu sukar gwamnatin shi ne Atiku Abubakar, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku, wanda ke sukar sahihancin zaben, ya na ci gaba da nuna adawarsa a kan wasu manufofin tattalin arzikin Tinubu, musamman cire tallafin fetur.

Kara karanta wannan

"Raba daidai ake yi," Gwamnatin Tinubu ta ce babu son rai a salon mulkinta

Atiku
Atiku ya na matukar adawa da tsarin tattalin arzikin gwamnati Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Ya nanata cewa wannan ya haifar da tashin farashin mai, wanda ya kara ta'azzara matsalolin tattalin arziki da jama'a ke fuskanta, kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

Atiku da magoya bayansa suna kira ga inganta rayuwar jama'a da mulki da adalci, tare da bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu bai dace da mulkin kasa ba.

A kan tsarin mulki, Thisday ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin tarayya da kwace, inda ya ke ganin wannan ne tsarin da jam'iyyar APC za ta bi a 2027.

2. Obi na sukar tsare-tsaren Tinubu

Peter Obi, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP a zaben 2023, ya na yawan sukar gwamnatin Tinubu, musamman a kan yadda ake tafiyar da al’amuran tattalin arziki.

peter
Obi ya soki manufar gwamnatin tarayya Hoto: Peter Obi
Asali: Facebook

Ya nuna damuwa kan hauhawar farashin kayayyaki, tsadar abinci da kuma karuwar talauci a tsakanin talakawan kasar.

Obi ya jaddada cewa dole ne a samar da manufofi masu dorewa da za su taimaka wa talakawa, a maimakon kara jefa su a cikin wani hali.

Kara karanta wannan

'Yan Majalisa 27 sun tattara kayansu sun fice daga jam'iyyar APC? an samu bayanai

3. "Za mu kayar da Tinubu," Kwankwaso

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa jam’iyyarsa za ta samu nasara a zaɓen 2027, matuƙar an yi zaɓe cikin gaskiya da adalci, saboda halin da aka jefa jama'a a ciki.

Kwankwaso ya kuma caccaki gwamnatin APC mai mulki, yana mai cewa ta gaza cika alkawuran da ta ɗauka ga ‘yan Najeriya.

Atiku
Kwankwaso na ganin Tinubu ba zai kai labari ba a zaben 2027 Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Ya ce gwamnatin ta kara ta’azzara matsalolin tsaro, tattalin arziki da tsadar rayuwa, inda mutane ke ƙara faɗawa cikin fatara.

Gwamnatin Tinubu: Abin da kungiyoyin matasa ke cewa

Matasa a Najeriya na ganin wani musayar yawu tsakanin 'yan siyasa ba shi ne zai rage tasiri ba, amma ganin cewa ana fadin gaskiya, zai yi wahala shugaba Bola Tinubu ya koma kan mulki.

Kwamred Umar Ibrahim Umar, Shugaban kungiyar dake yaki da rashin adalci ya shaida wa Legit cewa 'yan Najeriya su na ganin bakar wahala saboda tsarin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

DSS ta gano makamai a ofishin hadimin tsohon shugaban majalisar Legas

Ya ce:

"Gyare–gyaren tattalin arziki da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta kawo, karin haraji, a kara wancan, a cire tallafi kaza, man fetur ya koma ninkin ba ninkin yadda gwamnati ta karbe shi.
"Sannan tsadar rayuwa ta ta'azzara, sannan duk inda talaka yake samun sauki na rayuwa kama daga bangaren wutar lantarki, ilimi, lafiya, duk gwamnati kokari take yi ta janye.

Ya nanata cewa 'yan siyasa dake adawa da gwamnati sun samu gaba mai kyau da za ta iya kai su gaci, amma 'yan kasar nan sun dawo daga rakiyar 'yan siyasa da dama.

Yadda masana ke kallon zaben 2027

Dr. Sa'id Dukawa, masanin siyasa a jami’ar Bayero da ke Kano, ya shaida wa majiyar Legit cewa alamu sun nuna dukkan jam’iyyun siyasa na son rage tasirin junansu.

Ya kara da cewa, duk da haka, ya yi wuri a bayyana abin da zai iya afkuwa tsakanin jam’iyyun kafin zaben 2027, amma abin da ya tabbata shi ne "za a fafata."

Kara karanta wannan

"Za mu kawo karshen mulkin kama karya," PDP ta musanta baraka a cikinta

Ana ganin Kwankwaso ya fara tanadin 2027

A wani labarin, mun wallafa cewa an yi ganawar sirri da aka yi tsakanin jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola.

Ana ganin wannan tattaunawa a matsayin wata dabarar Kwankwaso a kokarinsa na neman goyon baya a yankin Kudu maso Yamma yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.