"Allah ne Ya Taimake Ni," Gwamna Ya Tattago Batun Alakarsa da Jiga Jigai 2 a Najeriya

"Allah ne Ya Taimake Ni," Gwamna Ya Tattago Batun Alakarsa da Jiga Jigai 2 a Najeriya

  • Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya karyata raɗe-raɗen da ake cewa iyayen gidansa ne ke juya shi yada suke so
  • Sanata Okpebholo ya bayyana cewa ba shi da uban gida a siyasa, sai dai Allah ya haɗa shi da manyan ƙusoshi da suka taimake shi ya zama gwamna
  • Gwamnan ya ce Adams Oshiomhole da ake zargin yana juya shi ba haka abin yake ba, amma yana bashi shawarwari masu amfani

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo - Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya karyata ikirarin cewa wasu jiga-jigan siyasa ne suka turo shi domin su rika sarrafa shi a matsayin gwamnan jihar.

A cewarsa, Allah ne kawai ya yi amfani da wasu mutane don tallafa masa wajen cimma burinsa na zama gwamna a zaben da aka gudanar bara.

Gwamnan Edo.
Gwamnan Edo ya musanta zargin cewa masu ke juya gwamnatinsa Hoto: Monday Okpebholo
Asali: Twitter

Gwamna Okpebholo na da ubangida?

Kara karanta wannan

"Yana raye ko ya mutu?": Watanni 3 ba a ga mataimakin gwamna ba, an fara tada jijiyoyin wuya

“Za ka iya nuna mani mutum ɗaya da sunan uban gidana da ya turo ni?” in ji gwamnan a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Allah ne ya yi amfani da mutane don su taimake ni, su goyi bayana, har na kai wannan matsayi.”

Gwamnan ya bayyana cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya mara masa baya ne a matsayinsa na jagoran jam’iyya mai mulki a yankin Kudu maso Kudu.

Dalilin da ya sa Akpabio ya taimaki gwamna

Okpebholo ya kara da cewa

“Shugaban Majalisar Dattawa shi ne jagoran APC daga Kudu maso Kudu. Duk abin da ya yi, domin ci gaban al’ummar Edo ya yi shi; yana so a sake farfaɗo da Edo.”

Gwamna Okpebholo ya bayyana cewa jama’ar Edo sun gaji da mulkin da ya gabata, kuma hakan ne ya sa suka zaɓe shi.

Kara karanta wannan

"Tinubu mutumin kirki ne, yana da niyya mai kyau," Babban malami ya yi wa mutane Nasiha

“Allah ne ya taimake ni, mutanen Edo suka fito suka bayyana ra'ayinsu a fili, mun gaji muna Alla-Alla a samu canji, ko a shekaru 20 masu zuwa, zan ci zaɓe.
“Ka san lokacin da na ci kujerar Sanata, kun manta ne akwai wani Sanata mai ci? A wancan lokacin kowa faɗa yake ba mi, amma duk da haka mun yi nasara," in ji shi.

Oshiomhole.ke juya gwamnan Edo?

Gwamnan ya kuma musanta cewa tsohon gwamnan Edo, kuma Sanata mai wakiltar Edo North, Adams Oshiomhole, yana da tasiri a mulkinsa kuma shi ke juya shi.

Ya ce Oshiomhole na ba shi shawara ne kawai idan ya bukaci hakan, kuma yawanci shawarwarin nasa sukan zama masu amfani.

Adams Oshiomhole.
Gwamna Okpebholo ya ce Oshiomhole na ɓa shawarwari masu amfani Hoto: Adams Oshiomhole
Asali: Twitter
“Duk lokacin da nake son magana da shi, sai ya ce: ‘Ɗana, na san yadda kake ji, kawai yi abin da kake so.’
"Amma sai na ce masa: ‘Ranka ya dade, ba zan yi yadda nake so ba, don Allah ka ba ni shawara.’ Sannan ya ba ni shawara, kuma yawanci shawarwarinsa suna haifar da sakamako mai kyau," in ji shi.

Kara karanta wannan

"Allah ne ya jaraba mu," Gwamna ya faɗawa babban malami abin da bai sani ba

Gwamna Okpebholo ya dakatar da mutum 2

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya dakatar da Antoni-Janar kuma kwamishinan shari’a, Hon. Samson Osagie bisa zarginsa da hannu a badaƙar kudi

Gwamnan ya kuma dakatar da shugaban hukumar kula da harkokin ƙananan hukumomi, ya ce su bar ofis har sai an kammala bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262