"Raba Daidai ake Yi," Gwamnatin Tinubu Ta ce Babu Son Rai a Salon Mulkinta

"Raba Daidai ake Yi," Gwamnatin Tinubu Ta ce Babu Son Rai a Salon Mulkinta

  • Gwamnatin tarayya ta ce Shugaba Bola Tinubu yana raba romon dimokuradiyya ga dukkan sassan kasar ba tare da nuna bambanci bas
  • Ministan tattalin arziki, Atiku Bagudu ya bayyana cewa an ware wa jihar Kebbi dimbin ayyuka a bangaren noma, lafiya da ilimi
  • Ya ce daga cikin ayyukan, an bayar da kwangilar titin Natisini – Kangiwa – Kamba akan N35 biliyan, da sauran tarin ayyukan inganta rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KebbiMinistan Kasafi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu ya ba da tabbacin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da adalci ga dukkan sassan kasar wajen raba romon dimokuradiyya.

A cewarsa, Jihar Kebbi ta samu kaso mai yawa na sama da ayyuka 40 da ke gudana a yanzu da suka kai darajar sama da Naira biliyan 600, wanda aka raba a fannoni daban-daban kamar noma, lafiya da ilimi.

Kara karanta wannan

Saukar farashi: Gwamna ya kawo shirin raba abinci kyauta a Ramadan

Tinubu
Bagudu ya ce kowa na cin moriyar gwamnatin tarayya Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar This Day ta ruwaito cewa Ministan ya yi wannan bayani ne a yayin wani gangami da aka gudanar jiya a filin wasa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce saboda irin dimbin ci gaba da Jihar Kebbi ta samu a kasa da shekaru biyu na gwamnatin Tinubu, Shugaban Kasa ya cancanci cikakken goyon bayan al’ummar jihar domin wa’adin mulkinsa na biyu.

Gwamnan Kebbi ya fadi aikin gwamnatin Tinubu

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Atiku Bagudu ya ce Shugaba Bola Tinubu ya nuna cewa jagora ne mai hangen nesa da karfin hada kan kowa a tafiyarsa.

Ya ce tun kafin hawa mulki, ya yi alkawarin zama shugaban kowa, kuma yana tabbatar da hakan a zahiri tun daga lokacin da ya hau mulki fiye da shekara daya da rabi da ta gabata.

Bagudu ya ce:

"A gare mu da ke Jihar Kebbi, muna godiya ga irin jagorancinsa wanda ke kara bunkasa ci gaban tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Yadda Sanatoci suka jawo hankalin Tinubu ya waiwayi gyaran titunan Arewa

"Gwamnatin Tarayya ta bayar da kwangilar gina titin Natisini – Kangiwa – Kamba akan naira biliyan 35, ta kammala titin Malamdo – Ngaski – Warah, ta fara aiki kan babbar hanyar Sokoto – Kebbi – Badagry, da kuma titin Koko-Mahuta – Dabai, duk don amfanin al’ummar Jihar Kebbi."

Gwamnatin Kebbi ta fadi ayyukan Tinubu

Yayin da yake jawabi a gangamin, Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa al’ummar jihar suna goyon bayan Shugaba Tinubu saboda irin ci gaba da ayyukan raya kasa da ya kawo musu.

Ya jinjinawa Shugaban Kasa bisa dimbin ayyukan ci gaba da ya kawo wa jihar, yana mai cewa:

"Za mu iya lissafa abubuwa da dama da Shugaban Kasa ya yi wa jiharmu. Saboda haka, ina tare da Tinubu a 2027. Idan lokaci ya yi, za mu ga ko suna da irin adadin jama’a kamar Tinubu a Jihar Kebbi."
"Wanda ya kawo mana ci gaba shi ne zabinmu."

Kara karanta wannan

Ana fargabar tsohon ciyaman ya bace bayan mummunan harin yan bindiga a Kebbi

An fara yi wa Tinubu kamfen

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APC reshen jihar Kebbi ta kaddamar da yakin neman tazarcen Gwamna Nasir Idris da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin zaben 2027.

Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa al'ummar jihar Kebbi suna goyon bayan Shugaba Tinubu saboda ayyukan ci gaba da ya kawo wa jihar, wanda ya sa ya zama wajibi a mara masa baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.