PDP Ta Fara Sayar da Fom Ɗin Takarar Gwamnan Anambra, Farashin Ya Jawo Cece Kuce
- Jam’iyyar PDP ta ƙaddamar da jadawalin zaben gwamnan Anambra, inda ta tsayar da N40m a matsayin kudin fom ɗin neman takara
- Zaɓen fidda gwani zai gudana a ranar 5 ga Afrilu, yayin da za a tantance ‘yan takara a ranar 11 ga Maris, kamar yadda takardun PDP suka nuna
- PDP za ta miƙa sunan ɗan takararta da mataimakinsa ga INEC a ranar 22 ga Mayu, bayan kammala dukkan tsare-tsaren da jam’iyyar ta tsara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Jam’iyyar PDP ta sanya Naira miliyan 40 a matsayin farashin fom ɗin neman tsayawa takarar gwamnan Anambra.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa za a gudanar da zaben gwamnan Anambra a ranar Asabar, 8 ga Nuwamba, 2025.

Asali: Twitter
PDP ta shriya zaben gwamnan Anambra

Kara karanta wannan
Ajali ya yi: Sanata ta riiga mu gidan gaskiya bayan an mata tiyata a ƙasar Amurka
Wata takarda da PDP ta aike wa shugaban jam’iyyar a Anambra, Chidi Chidebe, da sakataren APC, Sunday Ude-Okoye, ta ƙunshi jadawalin zaben, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Takardun da aka sanya wa hannu a ranar 13 ga Fabrairu, kuma aka fitar da su ranar Talata, sun nuna cewa 7 ga Maris ce ranar ƙarshe ta miƙa fom din.
Jam'iyyar PDP za ta fara sayar da fom ɗin nuna sha'awa da neman tsayawa takara daga ranar 24 ga Fabrairu, kuma za a kammala a watan Maris.
PDP ta sanya ranar zaben fitar da gwamni
Za a gudanar da zaɓen fitar da gwani na PDP a ranar 5 ga Afrilu, sannan a saurari ƙorafe-ƙorafen zaɓen a ranar 8 ga Afrilu.
Haka nan, za a yi taron tattaunawa tsakanin manyan jiga-jigan jam’iyyar da NWC a ranar 10 ga Maris a hedikwatar PDP da ke Abuja.
An tsara tantance ‘yan takara a ranar 11 ga Maris, yayin da za a saurari ƙorafe-ƙorafen tantancewar a ranar 14 ga Maris.
PDP ta sanya ranar mika sunan dan takara
Kwamitin ayyukan jam'iyyar na kasa (NWC) zai fitar da sunayen waɗanda suka tsallake tantancewa a ranar 19 ga Maris.
Za a gudanar da taron jam’iyyar a matakin gundumomi don zaɓen wakilai uku daga kowace gunduma daga 20 zuwa 21 ga Maris.
Haka nan, zaɓen wakilan zaben guda ɗaya daga kowace karamar hukuma zai gudana ranar 27 ga Maris.
Za a miƙa takardar shaidar cin zaɓe ga wanda ya yi nasara a ranar 10 ga Afrilu, sannan PDP za ta miƙa sunan ɗan takarar gwamna da mataimakinsa ga INEC a ranar 22 ga Mayu, 2025.
Dalilan da za su iya gwamna samun tazarce
A wani labarin, mun ruwaito cewa, magoya bayan Gwamna Charles Soludo sun daɗe suna cewa ba shi da abokin hamayya a 2025, amma abubuwa sun canza.
Daga rikicin addini da ya tsunduma ciki zuwa matsin lamba daga jam'iyyun adawa, ana hasashen zai fuskanci ƙalubale wajen neman tazarcensa.
Kafin zaɓen 2025, matsalolin siyasa sun fara fitowa fili, kuma Legit Hausa ta zakulo dalilai biyar da ka iya hana Soludo nasarar sake zama gwamna.
Asali: Legit.ng