Fitar Nabraska a NNPP zuwa APC Ya Jawo Rikita Rikita a Siyasar Kano

Fitar Nabraska a NNPP zuwa APC Ya Jawo Rikita Rikita a Siyasar Kano

  • Fitaccen jarumin Kannywood, Mustapha Badamasi Nabraska, ya fice daga NNPP da Kwankwasiyya tare da komawa APC
  • Ya bayyana ficewarsa daga Kwankwasiyya a Abuja, inda ya yar da jan hular da ke nuna alamar tafiyar
  • Wasu mutane sun bayyana ra’ayoyinsu kan sauyin shekarsa, wasu na maraba da shi yayin da wasu ke nuna rashin amincewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Shahararren jarumin fina-finan Kannywood, Mustapha Badamasi Nabraska, ya fice daga jam’iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya inda ya koma jam’iyyar APC.

Nabraska da ake wa lakabi da "His Excellency" a fim, ya bayyana sauyin shekarsa ne a Abuja yayin wata ziyara da ya kai wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin.

Kara karanta wannan

Cacar baki ta balle tsakanin APC, NNPP kan yi wa gwamnatin Abba Gida Gida kishiya

Naburaska
Nabraska ya koma jam'iyyar APC. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

A yayin taron, Nabraska ya yar da jan hulansa, alamar tafiyar Kwankwasiyya, tare da nuna cikakken biyayyarsa ga APC kamar yadda Sanata Barau ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan APC da suka tarbi Nabraska

Bayan sauyin shekar Nabraska, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya karbe shi a gidansa da ke Abuja.

Taron sauya shekarsa ya samu halartar Sanata Ibrahim Lamido daga Sokoto, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kiwon Lafiyar Farko da Yaki da Cututtuka.

Haka zalika, Mashawarci na Musamman kan Harkokin Siyasa ga Sanata Barau, Hon. Yusuf Tumfafi, shima yana daga cikin wadanda suka tarbi jarumin na Kannywood.

Sanata Barau ya bayyana sauyin shekar Nabraska a matsayin ci gaba mai kyau ga APC, yana mai cewa jam’iyyar na ci gaba da karɓar masu kishin kasa.

Ya bukaci sauran magoya baya da su mara wa APC baya domin ci gaban dimokuradiyya a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Na ɗauke shi uba," Tinubu ya kaɗu da Allah ya yi wa jagoran Yarbawa rasuwa

Riko da akidar Kwankwasiyya

Freedom Radio ya wallafa a Facebook cewa Nabraska ya ce bai shiga APC ba aiki ne ya kai shi ta hannun Sanatan Sokoto ta gabas Sen. Ibrahim Lamiɗo, inda ya wallafa cewa ya ce:

"Zan ci gaba da tallata ayyukan alkhairin Sanata Barau Jibrin. Amma ina jaddada muku ina nan aƙidata ta Kwankwasiyya."

Ra’ayoyin jama’a kan sauya shekar Nabraska

Bayan sauyin shekar Nabraska, mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu, inda wasu suka goyi bayan matakin, wasu kuma suka soki matakin.

Ibrahim Khalil ya ce:

“Ba ma fatan suutane irin su Nabraska cikin jam’iyyar nan. Ya kamata a dakatar da irin wannan shiriritar da ake yi a ƙasar nan.”

Abubakar Mukhtar ya bayyana rashin amincewarsa da matakin, yana mai cewa:

“Wannan siyasa ce ta ‘yan hijira. Ba na goyon bayan irin wannan siyasar. Ya kamata a daina karbar irin su Nabraska.”

Kara karanta wannan

Tinubu: Dan majalisa ya hada Ganduje da El Rufa'i, ya gyara musu zama kan 2027

Usman Abdullahi kuwa ya bayyana shakkunsa kan yadda APC ke karbar mutane da sauya sheka, inda ya ce:

“Da girmamawa, ba za a iya samun nasara da irin wadannan masu sauya sheka ba. Mun san cewa kawai suna bin ku ne don neman abin duniya.”

Ismail Abdullahi ya bayyana damuwarsa kan sahihancin jarumin a siyasa, yana mai cewa:

“Dole a yi taka-tsantsan da Nabraska. Ba na da cikakken yakini da shi a harkar siyasa.”

Sadiq Sabiu kuwa ya yi ikirarin cewa:

“Wallahi Nabraska sai ya koma Kwankwasiyya.”

Barau ya yi ta'aziyya ga mutanen Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Barau Jibrin ya yi ta'aziyya ga mutanen Kano bayan wani hadarin tirela da ya kashe jama'a.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya roki Allah ya gafarta wa wadanda suka rasu ya kuma bukaci a rika kiyaye dokokin tuki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel