PDP Ta Soki 'Yan Majalisar da Su ka Sauya Sheka, Ta Fara Kokarin Raba Su da Mukamansu
- Jam’iyyar PDP ta nemi ‘yan majalisar dokokin Kaduna da na majalisar wakilai da suka sauya sheƙa zuwa APC da su bar kujerunsu
- PDP ta bayyana cewa duk da kowane dan siyasa ya na da 'yancin shiga kowace jam'iyya, amma akwai tanadin da kundin tsarin mulki ya yi
- PDP ta sha alwashin yin amfani da tanadin kundin tsarin mulki don dawo da kujerun ‘yan majalisar da suka koma APC a kwanakin nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - PDP ta nemi dukkan ‘yan majalisar wakilai da kuma na majalisar dokokin jihar Kaduna da suka fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC mai mulki da su sauka daga kujerunsu.
‘Yan majalisar daga kudancin Kaduna sun kasance cikin jerin mutane 50 da suka sauya sheƙa daga jam’iyyar adawa zuwa APC a ranar Asabar.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Gwamna Uba Sani ne ya karɓi masu sauya shekar a hukumance, ciki har da tsohon gwamnan jihar, Ramalan Yero.

Asali: Twitter
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran wanda suka sauya sheka sun hada da tsohon Sanata Danjuma La’ah, a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da aka gudanar a Murtala Square, Kaduna.
PDP ta caccaki ‘yan majalisu
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Sakatariyar yaɗa labarai ta PDP a jihar Kaduna, Maria Dogo ta yi Allah wadai da yadda 'yan majalisar da aka zaba a inuwarta su ka sauya jam'iyya zuwa APC.
Ta bayyana cewa sauya shekar, musamman daga ‘yan majalisa da ke kan kujerunsu, cin amanar mutanen da suka kada masu kuri'a ne a jihar.
Mrs. Dogo ta ce ko da yake jam'iyyar PDP ta san cewa kowane ɗan Najeriya na da ‘yancin zaɓin jam’iyya a karkashin kundin tsarin mulki, amma wannan mataki bai dace ba kuma abin Allah wadai ne.

Kara karanta wannan
Ana tsakiyar rikicin El Rufai da Uba Sani, 'yan majalisa 3 sun fice daga PDP zuwa APC
PDP za ta dauki mataki a kan ‘yan majalisa
PDP ta bayyana cewa duk da wannan sauya sheƙar, jam’iyyar ba za ta yi rauni ba, har yanzu kuma ita ce zaɓin mafi yawan al’ummar jihar Kaduna.
Sanarwar ta ce:
“Saboda haka, muna tabbatar wa al’ummar jihar Kaduna, musamman mutanen mazabun da abin ya shafa, cewa shugabancin PDP zai yi amfani da tanadin kundin tsarin mulki don dawo da kujerunmu, duba da babu rabuwar kai ko wata matsala a shugabancinmu na ƙasa.
“A cewar sassa na 68(1)(g) da 109 na kundin tsarin mulkin Najeriya, duk wani ɗan majalisar da ya sauya sheƙa daga wata jam’iyya zuwa wata ya zama dole ya sauka daga kujerarsa.
Martanin APC ga tsohon gwamnan PDP
A wani labarin, mun wallafa cewa mai magana da yawun APC na kasa, Felix Morka ya bayyana cewa kalaman tsohon gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal sun tona halayensa wajen sauya sheka.
Wannan na zuwa a matsayin martani ga tsohon gwamnan, wanda ya ce dukkanin 'yan siyasar Najeriya da ke sauya sheka zuwa APC a yanzu na yin hakan ne domin gyara tukunyarsu ba kishin al'umma ba.
Asali: Legit.ng