Shugabannin Arewa Sun Yiwa Ganduje Kaca Kaca, Sun Kalubalanci Tazarcen Tinubu

Shugabannin Arewa Sun Yiwa Ganduje Kaca Kaca, Sun Kalubalanci Tazarcen Tinubu

  • Shugabannin Arewa sun yiwa Abdullahi Ganduje, shugaban APC na kasa kaca kaca kan tallata tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Legit Hausa ta rahoto cewa Ganduje ya ce Arewa ta mance da neman kujerar shugaban kasa a 2027 tare da kyale Tinubu ya yi wa'adi biyu
  • Wasu jiga-jigan siyasar Arewa sun bayyana furucin Ganduje a matsayin barazana ga tsarin dimokuradiyya, suna masu kalubalantar shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje, na fuskantar suka daga shugabanni da kungiyoyin Arewacin Najeriya kan matsayinsa game da zaben 2027.

Wasu manyan Arewa sun zargi Ganduje da fifita ra’ayin Shugaba Bola Tinubu a kan maslahar yankin, suna mai cewa bai kamata ya hana ‘yan Arewa takara ba.

Shugabannin Arewa sun yi wa Ganduje martani kan tazarcen Tinubu a 2027
Shugabannin Arewa sun gargadi Ganduje kan cusa Tinubu a matsayin shugaban kasa a 2027. Hoto: @OfficialAPCNg, @officialABAT, @elrufai
Asali: Facebook

Ganduje da El-Rufai sun yi musayar kalamai

Jaridar Vanguard, ta rahoto Ganduje ya bukaci ‘yan siyasar Arewa da ke shirin takara a 2027 su hakura, yana mai jaddada cewa Tinubu zai yi wa’adi biyu.

Kara karanta wannan

'Arewa ba za ta yafe ba': An fadi yadda Tinubu zai lallabi yankin a zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan kalamai sun biyo bayan jawabin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da ke cewa Arewa za ta mayar da martani ga Tinubu a 2027.

A lokacin da yake karbar bakuncin shugabanni da matasan Tinubu a Abuja, Ganduje ya bukaci Arewa ta daina tunanin fitar da dan takara, inji rahoton Legit Hausa.

Shugabannin Arewa sun fusata da kalaman Ganduje

Shugaban APC din ya tunatar da cewa lokacin da shugaba daga Arewa ya yi wa’adi biyu, an yarda shugaban kasa na gaba ya fito daga Kudu.

A cewarsa, bayan Tinubu ya kammala wa’adinsa a 2027, to shugabancin Najeriya zai koma Arewa kamar yadda tsarin karba-karba ke tafiya.

Sai dai wadannan kalamai sun fusata wasu shugabannin Arewa, wadanda suka bayyana su a matsayin barazana ga tsarin dimokuradiyya da daidaito.

Lokaci ne zai kawo karshen ce-ce-ku-ce kan 2027

Kara karanta wannan

Tsohon Jigo a APC, Dr. Bugaje ya yi wankin babban bargo ga Buhari, Tinubu da APC

Wasu jiga-jigan yankin sun bayyana cewa Ganduje bai da hurumin yanke wa Arewa hukunci game da makomar siyasar 2027.

Kalaman Ganduje sun kara tayar da muhawara kan rabon mulki a Najeriya, lamarin da ke kara daukar hankalin masu ruwa da tsaki.

Yanzu dai lokaci ne kawai zai bayyana yadda wannan cece-kuce zai shafi siyasar Najeriya yayin da ake shirin zaben 2027.

Kungiyar ACF ta caccaki Ganduje kan tallata Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar dattawa Arewa (ACF) tare da wasu jiga-jigan siyasar Arewa sun ce ba za a tilasta wa yankin zabar Tinubu a 2027 ba.

Kungiyar ta jaddada cewa babu wanda ke da ikon magana da yawun daukacin Arewa, don haka furucin shugaban APC, Abdullahi Ganduje, ba ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel