Uba Sani Ya Karbi 'Yan Siyasar da Aka Kora a APC Lokacin El Rufai Zuwa Jam'iyyar

Uba Sani Ya Karbi 'Yan Siyasar da Aka Kora a APC Lokacin El Rufai Zuwa Jam'iyyar

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Kaduna ta samu naƙasu bayan manyan jiga-jiganta sun sauya sheƙa zuwa APC
  • Daga cikin masu sauya sheƙar akwai tsohon gwamna, Mukhtar Ramalan Yero, tsofaffin sanatoci da manyan ƙusoshin jam'iyyar
  • Gwamna Uba Sani ya yi maraba da shigowarsu jam'iyyar inda ya ba su tabbacin cewa za a yi musu adalci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Jam'iyyar APC ta samu tagomashi a jihar Kaduna bayan manyan jiga-jigan PDP sun sauya sheƙa zuwa cikinta.

Daga cikin masu sauya sheƙar har da tsohon gwamna, tsofaffin sanatoci da tsohon ɗan takarar gwamna.

Jiga jigan PDP sun koma APC a Kaduna
Uba Sani ya yi maraba da jiga jigan PDP zuwa APC a Kaduna Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Jiga-jigan PDP sun koma APC a Kaduna

Jaridar The Nation ta rahoto cewa daga cikin masu sauya sheƙar akwai tsohon gwamnan Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero, Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya dura kan gwamnatin APC, ya yi wa 'yan siyasa tonon silili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun haɗa da Alhaji Sani Shaaban, Sanata Danjuma Laah, Alhaji Abubakar Mustapha, tsohon sakataren tsare-tsare na ƙasa na PDP da Ambasada Sule Buba, tsohon jakadan Najeriya a Koriya ta Kudu.

An dai tarbe su zuwa APC ne tare da dubunnan magoya bayansu a wani babban taro da aka shirya a ranar Asabar.

Gwamna Uba Sani ya samu yabo

Sanata Suleiman Hunkuyi ya yabawa Gwamna Uba Sani bisa ƙoƙarinsa na dawo da dukkanin jiga-jigan da tsohon Gwamna Nasir El-Rufa'i ya kore su daga jam'iyyar APC.

"Dukkanmu da muka kafa jam'iyyar APC a jihar Kaduna mun san cewa, a tsakiyar tafiyar, an tsayar da motar a cikin daji, aka umarce mu da mu sauka, kuma mun sauka ba tare da yin faɗa ba."
"Amma a yau muna da gwamna wanda ya zagaya dukkan wuraren da aka sauke mu, ya ɗauke mu ɗaya bayan ɗaya, ya mayar da mu cikin APC."

Kara karanta wannan

"Ka yi mubaya'a," Sanatan da El Rufa'i ya tsinewa ya ce tsohon Gwamna ya daina ja da Uba Sani

- Sanata Suleiman Hunkuyi

Uba Sani ya yi musu maraba zuwa APC

A nasa ɓangaren, Gwamna Uba Sani ya yi maraba da jiga-jigan ƴan adawan da kusan wasu mutane 200,000 da suka sauya sheƙa zuwa APC,

Gwamna Uba Sani ya tabbatar musu cewa a cikin jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna, za su samu dukkan haƙƙoki da damar da kowane mamba na jam'iyyar ke da su.

"Wanda ya shiga APC a yau da wanda ya kasance mamba tun shekaru 10 da suka wuce, duk suna da matsayi ɗaya. Za su ji daɗin dukkan hakkoki da damar da kowane mamba ke da su."

- Gwamna Uba Sani

Gwamnan ya kuma yi kira ga masu sauya shekar da su sanar da magoya bayansu game da shirye-shiryen APC na karbar su cikin jam'iyyar, tare da bayyana cewa ƙofofin jam'iyyar a bude suke don karbar ƙarin masu son shigowa cikinta.

Kara karanta wannan

APC ta shawarci El-Rufa'i a kawo ƙarshen takun saka da gwamnatin Tinubu

"A zaɓen 2027, masu zaɓe za su kaɗa kuri'a ga APC a dukkan zaɓuka, daga sama zuwa ƙasa. A sama, za a sake zaɓar shugabanmu, Shugaba Bola Ahmed Tinubu."
"A matakin jiha, jam'iyyar APC za ta ci zaɓen gwamna, majalisar dokoki ta ƙasa da ta jiha, da yardar Allah."

- Gwamna Uba Sani

Gwamnan ya yi alkawarin cewa za a aiwatar da ayyuka a dukkan sassan jihar Kaduna, ba tare da la'akari da bambancin jam'iyya, ƙabilanci ko addini ba.

Ƴan majalisar PDP sun koma APC a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan majalisar dokokin jihar Kaduna na jam'iyyar PDP, sun sauya sheƙa zuwa APC.

Ƴanajalisar dokokin guda uku sun bayyana cewa salon mulkn Gwamna Uba Sani ne ya sanya suka sauya sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng