APC Za Ta Kafa Gwamnatin Basaja a Kano, Za a Bi Diddigin Ayyukan Abba Gida Gida

APC Za Ta Kafa Gwamnatin Basaja a Kano, Za a Bi Diddigin Ayyukan Abba Gida Gida

  • Jam’iyyar APC ta sanar da shirinta na kafa gwamnatin basaja a Kano domin bin diddigin ayyukan gwamnatin Abba Kabir Yusuf
  • Kungiyar APC za ta tura wakilanta zuwa ma’aikatun gwamnati domin bibiyar ayyuka, sannan su fitar da rahotannin adawa
  • Shugaban kungiyar, Alhaji Usman, ya ce za su sanar da jama’a cikakken shirin nan gaba, domin tabbatar da adalci a mulkin Kano

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Jam’iyyar APC ta bayyana shirin kafa gwamnatin basaja a Kano domin sa ido kan tafiyar da mulkin Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.

Shugaban kungiyar masu kishin APC da ke cikin jam'iyyar a Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya bayyana haka a wani taro da kungiyar ta gudanar don sabunta shirye-shiryenta.

APC ta yi magana kan shirinta na kafa gwamnatin basaja a jihar Kano
APC za ta fara bin diddigin ayyukan gwamnatin Kano ta hanyar kafa gwamnati basaja. Hoto: @OfficialAPCNg, @Kyusufabba
Asali: Twitter

'Yan APC za su kafa gwamnatin basaja a Kano

Kara karanta wannan

Tsohon Jigo a APC, Dr. Bugaje ya yi wankin babban bargo ga Buhari, Tinubu da APC

A cewar Alhaji Usman, gwamnatin basaja za ta sanya ido kan ma’aikatun gwamnati, domin ta fitar da rahotannin suka masu ma'ana, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar ya ce wannan tsari ana yin irin sa a Birtaniya, inda ‘yan adawa ke nada ministoci na basaja don duba ayyukan gwamnatin da ke mulki.

Kungiyar ta ce za ta kawo irin wannan tsarin ne da nufin tabbatar da cewa an gudanar da mulki bisa tsari da bin ka’idojin da suka dacewa a Kano.

Alhaji Usman Alhaji ya ce APC za ta tura wakilanta zuwa dukkanin hukumomin gwamnati a Kano domin bin diddigin ayyukan da ake yi.

APC na zargin Abba da rashin iya mulki

Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba za su gudanar da taron manema labarai don sanar da jama’a cikakken shirin.

A cewarsa, hakan zai bai wa jama’a damar sanin yadda ake tafiyar da ayyukan gwamnati da kuma yiwuwar yin gyara.

Kara karanta wannan

APC ta shawarci El-Rufa'i a kawo ƙarshen takun saka da gwamnatin Tinubu

Jam’iyyar APC ta dade tana sukar salon da Abba ke amfani da shi wajen tafiyar da mulkin Kano, inda take zargin cewa ba a tafiya da Kano bisa turba madaidaiciya.

Yanzu dai ana jiran matakin da gwamnatin Kano za ta dauka dangane da wannan sabon yunkuri na jam’iyyar adawa.

Kusoshin NNPP sun koma APC a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya tarbi gungun 'yan NNPP da suka sauya sheka zuwa APC a Kano.

Wasu daga cikin wadanda suka sauya shekar sun ce sun gaji da salon shugabancin Kwankwasiyya, wanda suka bayyana a matsayin na danniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.