Shugaban Majalisa Ya Gwangwaje Fitaccen Mawaki, Alan Waka da babban Mukami
- Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen, ya nada mawaki, Aminu Ladan Abubakar, a matsayin babban mataimaki a ofishinsa
- Alan Waka ya fara aiki daga 1 ga Fabrairun 2025, inda zai rika karbar albashi a matsayin ma’aikacin gwamnati da ke mataki na 16
- Masoya da abokan arziki sun taya Alan Waka murna, suna addu’ar Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da aka dora masa cikin nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen, ya gwangwaje fitaccen mawakin Kano, Aminu Ladan Abubakar da shirgegen mukami.
Aminu Ladan, wanda aka fi sani da Alan Waka, ya samu mukamin babban mataimaki na harkokin majalisa ga shugaban majalisar wakilai.

Asali: Twitter
Shugaban majalisa ya gwangwaje Alan Waka da mukami
Mawakin ne da kansa ya sanar da wannan abin albishir ga mabiyansa a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a, 14 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan
Bayan zargin masu hannu a ta'addanci, yan ta'adda sun kashe junansu a kazamin hari
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jikin takardar tabbatar da daukar aikin, Legit Hausa ta fahimci cewa Alan Waka ya fara aikin ne daga ranar 1 ga watan Fabrairun 2025.
Hakazalika, Alan Waka zai rika karbar albashi a matsayin ma'aikacin gwamnati da ke mataki na 16, step 05.
"Na amince da karbar wannan aiki" - Alan Waka
A sakon da ya wallafawa masoyansa, Alan Waka ya ce:
"An wayi gari a wannan zamani samun gurbi na aikin nauyi irin wannan ya zama abin da ake kakar taya murna da baloƙoƙon cewar namu ya samu.
"Ni ma a doron wannan sabuwar al'adar nake gabatar da wannan takarda mai nuna shaidar an ɗauke ni aiki a ofishin Babban Kakakin Majalisar Tarayyar Nijeriya Dr Abbas Tajuddeen Phd.
"Ina gabatar da wannan takarda a wadannan shafukan zumunta domin nuna amincewa ta da karbar wannan gurbin aiki, tare da neman addu'ar masoya akan Allah ya fisshe mu kunyar Dr. Aliyu Sani Madakin Gini, wanda ya zama tsani na isa wannan mataki."
Mutane sun taya Alan Waka Murna
Lawal Rabe Daura:
"Masha Allah. Hakika an ajiye kwarya a gurbinta. Duba da cancanta da jajircewarka da kuma kwazo. Allah ya sanya alkairi, ya tayaka riko, yasa ka taimaki al'umar mu ta kowane bangare."
Muhammad Lawal Barista:
"Masha Allah. Allah Ta'ala ya sanya albarka, ya ba ka ikon sauke wannan nauyi da aka dora maka. Allah Ta'ala ya yi riko da hannuwanku dukkanku."
Kamil Dahiru Gwammaja:
"AlhamdulilLahi. Haƙiƙa maigirma Hon. Aliyu Sani Madaki ya zamo jagora nagari, wanda al'ummarmu take alfahari da shi. Aminu Ladan Abubakar Allah ya sa albarka."
Zaharadden Haruna:
"Gwadabe sarkin waka, ina maka murna mai tarin yawa, Allah ya tayaka rikon wannan mukami, amin."
Sani Danja ya samu mukami a gwamnatin Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Jarumi Sani Danja, ya samu mukamin babban mai ba da shawara na musamman ga gwamnan Kano kan harkokin matasa da wasanni.
An ce Gwamna Abba Kabir ya nada Sani Danja wannan mukamin ne saboda jajircewarsa wajen tallafa wa matasa da bunkasa wasanni a jihar Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng