PDP Ta Samu Koma Baya, 'Yan Majalisa 3 da Tsohon Sanata Sun Koma APC

PDP Ta Samu Koma Baya, 'Yan Majalisa 3 da Tsohon Sanata Sun Koma APC

  • Jam'iyyar PDP ta samu naƙasu a siyasar jihar Kaduna ƴan majalisunta guda uku sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulki
  • Ƴan majalisar dokokin ta jihar sun bayyana cewa sun koma APC ne saboda gamsuwa da kamun ludayin mulkin Gwamna Uba Sani
  • Gwamna Uba Sani ya yi maraba da su zuwa jam'iyyar APC, inda ya ce zai ci gaba da ƙoƙarin ganin ya yi adalci ga mutanen Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Jam'iyyar PDP ta samu koma baya bayan ƴan majalisarta guda uku sun sauya sheƙa zuwa APC a jihar Kaduna.

Ƴan majalisar dokokin jihar Kaduna guda uku waɗanda aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa APC.

'Yan majalisar PDP sun koma APC a Kaduna
Uba Sani ya tarbi 'yan majalisar PDP da suka dawo APC Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Meyasa ƴan majalisar PDP suka koma APC?

Jaridar The Cable ta rahoto cewa ƴan majalisar sun ce kyakkyawan shugabanci da aikin da Gwamna Uba Sani ke yi a jihar Kaduna ya sa suka bar PDP suka koma APC.

Kara karanta wannan

Duk da yin sulhu, 'yan.bindiga sun tafka ta'asa a jihar Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan majalisar da suka sauya sheƙa sun haɗa da Henry Mara (mazaɓar Jaba), Emmanuel Kantiok (mazaɓar Zonkwa), da Samuel Kambai (mazaɓar Zango).

Ƴan majalisar dai sun bayyana matakin da suka ɗauka ɗin ne a cikin wata wasiƙa da suka aikawa shugabannin PDP a mazaɓunsu a ranar Alhamis.

Henry Mara, wanda shi ne shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, ya ce PDP ta rasa tasirinta a Kudancin Kaduna saboda nasarorin da Gwamna Uba Sani ya samu wajen samar da zaman lafiya da haɗin kai.

“Akwai gagarumin canji a tsarin siyasar majalisar dokoki, kuma muna sa ran karin wasu ƴan adawa za su bar PDP su koma APC."

- Henry Mara

Tsohon sanatan PDP ya koma APC

A gefe guda kuma, tsohon sanatan Kaduna ta Kudu, Danjuma La’ah, ya fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC, cewar rahoton jaridar The Nation.

Danjuma La’ah ya ce matakin da ya ɗauka na barin PDP na ƙashin kansa ne, bayan da ya miƙa takardar murabus dinsa ga shugaban jam’iyyar a ƙaramar hukumar Kaura.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya dawo daga rakiyar Tinubu, ya fadi babbar nadamar da ya yi

Wannan sauya sheka ya zo ne kwanaki kaɗan bayan da Amos Magaji, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Zangon Kataf/Jaba, ya sanar da komawarsa APC daga PDP.

Uba Sani ya tarbi masu sauya sheƙa

Yayin da yake tarbar sababbin mambobin a Kafanchan a ranar Juma’a, Gwamna Uba Sani ya ce APC na samun karɓuwa a Kudancin Kaduna, wanda a baya PDP ta mamaye saboda mulkinsa na adalci.

Ya ce yana da burin tabbatar da daidaito da ci gaba ga kowa da kowa ba tare da la’akari da bambancin siyasa, addini ko ƙabila ba.

A cewarsa, bayan an kammala zaɓe, ya kamata a ajiye siyasa gefe ɗaya, a mayar da hankali kan mulki, inda ya ce haka shi ne asalin shugabanci na gari.

Ƙungiyar APC ta yi wa Tinubu alƙawari

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar jam'iyyar APC ta yankin Arewa ta Tsakiya ta yi wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban PDP ya bi sahun ɗan Majalisa, ya tattara jiga jigai sun koma APC

Ƙungiyar ta yi wa shugaba Tinubu alƙawarin samun ƙuri'u miliyan huɗu a yankin a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe nan da shekara biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel